ABDUL-MALEEK (BOBO)

By BilynAbdull

203K 11.3K 90

Labarin mai nuni da muhimmancin biyayya ga iyaye, gujema son zuciya, soyayya, zuminci, tare da cakwakiya tsak... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
31
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
27
28
29
30
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53

26

3.5K 227 1
By BilynAbdull

            💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 27

Appa yatashi zaune yana murmushi, oyoyo babana nida Ammi.
   Shima bobo dariyar yakeyi, yaje dafda Appa yazauna tamkar zai shige jikinsa.
   Appa yamik'a masa hannu su gaisa, amma saiya nok'e ya ce, "ina yini Appa.
  Dariya Appa yasakeyi, mukarram bakaso musamu ladan musabahane?, mirmushi yayi batareda yace komaiba, Appa yakamo hannun bobo yahad'e danasa yana fad'in ya iyalin?.
   Suna nan lfy Appanmu, sunama gaisheku.
    Muna amsawa. yau baka je aiki bane?.
   Naje Appa, amma nataso dawurine saboda d'akko Nawal a school.
   Ok, to ina direbanta?.
   Wai bayajin dad'in jikinsa, shine nacemasa yahuta kawai.
   ALLAH yabashi lafiya to.
  Amin.
Assalamu alaikum.
   Wa'alaikisslam. Appa da bobo suka amsawa ammi sallamarta, bobo yamik'e da sauri yakar6i kayan hannun ammi, kai Amminmu da kanki?, miye amfanin wad'ancan yaran?.
   Dariya tayi tazauna, to mukarram inbanyiba wazaiyi?, hidimar mijinace fa.
   Murmushi bobo yayi, shiyyasa kullum yakeson Amminsa haryau baiga macen datakai amminsu iya tattalin mijiba, gashidai sun tsufa amma har yanzu suna tattalin junansu tamkar yara.......
   Ammi tak'atsema bobo tunani da fad'in mukarram ga abinci.
   Firgigit yadawo da kallonsa Kansu, Ammi mikikace?.
    Tunanin mi kakeyine?.
  Bai 6oye musuba yafad'a musu abinda yake tunani, Dan akwai fahimtar juna da shak'uwa tsakaninsu da iyayensu.
   Daga Ammi har Appa dariya sukayi danjin firicin bobo, ammi ta ce, "toga abinci azuba?.
   A'a ammi nima matana tacikamin ciki da girkinta mai dad'i.
      hhhhhh d'an bantan uba, ashedai gaskiyar Hamza dayace kanason matarka, babanafa akwai iya taku.
   Dariya sosai bobo da Ammi sukeyi danjin zancen Appa, appa ya ce, " naji dad'i sosai wlhy, ALLAH yak'ara Baku zaman lfy da zuri'a tagari.
   Kansa ak'asa ya ce, "amin."
   Hira sukacigaba dayi, Appa yanacin abinci, bayan ya kammala ya ce, "mukarram!.”
    Yanda Appa yakira sunan nasa yasan tabbas maganar muhimmiyace, shima cikeda girmamawa da nutsuwa ya ce, " na'am Appa.
     Appa yagyara zamansa, yanamai tsurama bobo ido, mukarram mike tsakaninka da Alh sunusi Dala?.
    Ajiyar zuciya bobo yasauke, cikin nutsuwa yayma Appa bayanin tun farkon tsintar muheebat dakuma abinda yake faruwa a yanzun.
    Appa ya girgiza kai alamar gamsuwa, ya ce, "ina alfahari daku sosai 'ya'yana, ngd ma ALLAH dayayiku masu hankali dasanin darajar d'an Adam, lallai kaburgeni sosai babana, kuma Nagoya maka baya d'ari bisa d'ari ka kwatoma yarinyar hak'k'inta, “I'm proud of you my dear son”.
     ALLAH yatsare minku aduk inda kuka tsinci kanku.
    Amin Appa mungodema ALLAH dasamunku amatsayin iyaye nagari, bamuda abin biyanku saidai muyita binku da addu'a har k'arshen numfashinmu.
   Ammi dai sai murmushin jin dad'i takeyi.
   Appa yacigaba da fad'in dama abinda yasa kaji namaka maganar yaune Alhaji Sadiq muna hira yake bani labarin furucin Alh sunusi akanka, todaya fad'i sunanka shine yagano d'aya daga cikin 'ya'yanane, shine yasameni yake gayamin nasaka ido kar a cutarmin dakai, Dan Alh sunusi bashida imani ko kad'an.
      _(nasan har yanzu baima San kai d'ana bane shiyyasa yake rangwanta maka, Dan bama shiri sosai nidashi, siyasa tasakashi d'aukar gaba damu nida Abban Ammar)_
    amma kadage da addu'a muma zamu tayaka, ALLAH yana tareda mai gsky kaji my son.
    Murmushi bobo yayi, ya ce, " karka damu Appa wlhy daidai da second 1 banta6ajin tsoro ko Shankar Alh sunusi ba, ni duk sanda yay wani abunma k'aramin k'aimi yakeyi.
    Daga Ammi har Appa dariyar sukayi, sukace to ALLAH yak'ara tsareka auta, fira sosai yasha da iyayensa, saida suka dawo daga sallar magriba sannan yay musu sallama zai tafi.
   Appa ya ce, "gobe idan ALLAH yakaimu yanason ganinsu su duka, yanaso su tattauna akan maganar auren su khursiyya.
   To Appa ALLAH yakaimu lfy.
  Amin bobon Ammi.
  Dariyar bobo yayi yafice sai gida.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
     Bayan isha'i ummi tashiga d'akin safna danganin ko lfy?, akwance take tana chart itada baseera dawasu k'awayensu a group sunata zugata akan bobo, Dan tuni sunsan labarin bobo.
   Jin motsin tahowar mutum yasata tura wayar a k'ark'ashin filo, danbata buk'atar kowa yagane halin datake ciki.
    Azaune ummi tasameta tana duba takardunta na makaranta.
   Ummi ta ce, " o aini nazatama bakida lfy ne?, kimdawo baki nemeniba bare naji labarin autana.
   'Yar dariyar basarwa safna tayi, lah ummi wlhy fitsarine yakoroni shiyyasa banshigoba, daga baya kuma namak'ale ad'aki dankarki lik'amin girki.
    Dariyar ummi tayi, ta ce, "malalaciyar banza, ke koma auren akai miki yanzu aii mijin yabani, babu abinda kika iya sai kwalliya.
   Safna ta ce, " kai ummi, aidai nasan Kodan k'yawuna mijin ya zauna dani.
   Baki ummi ta ta6e ta ce, "keni rabani da shiriritarki Yakika ganomin autata?.
   Tana nan tak'ara k'iba, cewar Safna tana ta6e baki.
   Alhmdllh ummi tafad'a cikeda jin dad'i, ALLAH yak'ara baku zaman lfy autana, har hankalina ya kwanta aii wlhy.
    Itadai safna batace komaiba har ummi tafice.
Raka ummi tayi da harara kamar ba uwartaba.

Na ce, " ALLAH yashiryaki Safna.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
          Sai bayan isha'i bobo yashigo gidan, farking yayi Inda yadace, yafito yanufi cikin gida cikin takun gayunsa da k'asaita, hannunsa rik'e da ledoji.
    Rahma da Nawal suna zaune afalo suna homework.
   Dagudu Nawal taje ta rungumesa, Yaya sama da ita yana sumbatar kumatunta, d'iyar momy ya gida?.
    Ta ce, "my papa lfy, ledan hannunsa tak'ar6a, ya ce, " zaki iya kuwa baby?.
    Lah papa momyna ta ce, "niba raguwa bace, ko momyna?..
   Rahma ta ce, " hakane my dear keba raguwa bace.
   Tad'an kalli bobo ta ce, "sannu da zuwa.
    Yauwa ya amsa yana mata munafukin kallon nan NASA k'asa², d'akinsa yanufa yana fad'in kid'an kawomin ruwa.
     Rahma tad'an turo baki gaba, mutum ace kullum fuska a d'aure kamar wani soja?, azuciyarta take wannan maganar.
   Tamik'e tana cigaba da mitarta azuciya, to miye nacewama nakai masa ruwan sha d'aki?, sabon salo wai gaida uwar miji akasuwa, dahakadai tad'auki ruwa da cup tasaka a k'aramin filet tanufi d'akinsa.

Harya cire kaya dagashi sai gajeren wando, yana zaune abakin gado yana waya da ya Hamza.
   Ta turo k'ofar tashigo da sallama, tai saurin kauda kanta Dan ganinsa babu kaya, aiko tazame zata fad'i suuuuuuuu.
    Da sauri yatareta tafad'o jikinsa, saurin kallon inda tafad'a tayi, karaf suka had'a ido, kallon juna sukeyi cikin kallon ido cikin ido, da sauri Rahma ta lumshe idanunta danbazata juri kallon cikin idonsaba.
    Shikam aituni tsigar jikinsa ta tashi, shima yalumshe nasa fararen idanun yana murmushi, haka kawai yatinci Kansa anishad'in kasancewarsu haka.
     Rahma tafara yunk'urin tashi daga jikinsa, duk kunya ta lullu6eta.
    Cikin muryar nan tasa mai sanyi da amo ya ce, "sorry."
   Itama ahankali ta ce, ''ngd, har yanzu yak'i bata damar tashi daga jikinsa, saima k'ara rik'eta dayayi.
    Wayarsa aka kira, suduka suka kalli wayar, Rahma tayunk'ura ta zame jikinta, tiren hannunta yakar6a Wanda ALLAH yatsare babu abinda yazube, tomiya tsorataki?, yay maganar yana watsa mata wani shi'umin kallo.
      Azuciyarta ta ce, ''Kaine mana, amma afili saitace babu komaifa.
             Murmushi kawai yayi Dan yasan ganinsa datayi babu rigane ya razanata.
    Batayi auneba taji anjamata hanci, matsoraciya kirage tsoronnan naki.
    Dad'an gudunta tafice daga d'akin.
    Murmushi yayi yana girgiza kai, afili ya ce, "k'uruci dangin hauka.

Falo tadawo tabud'e abinda yakawo musu, gasashshen namane da ice-cream, tana cikin dubawa yafito sanye cikin wando 3½ da k'aramar riga tashan iska, yau da alama babu karatun jarida babu danna laptop Dan wayoyinsane kawai ahannunsa.
   Kujerar dasu Rahma ke jingine ya zauna, Nawal ta ce, "papa zomiyi game.
     Baga shinan kinayi da momyn kiba, Nawal tayi shiru dantaji haushi.
        Yakalli Rahma wai INA bak'uwar takin?.
   Tafa wuce gida tun d'azun.
    Baice komaiba, Wayarsa yad'auka yafara charting Wanda saiyayi kwana uku bai hauba.
    Rahama ta ce, " azuciyarta ana nandai da hali.
   Ta daure ta ce, "papa akawo abinci, yad'ago yana kallonta, shikam mamaki take bashi idan tace masa papa, ya ce, "zuwa anjima.
    Daganan kowa yay shiru shi yana danna waya, sukuma suna game.

        Ajiye wayar yayi yana kallonsu batareda sun saniba, Nawal tafi Rahma iyawa sosai, Dan suna 'Yar tseren motocine, amma tuni Nawal ta tserema Rahma, yashagala sosai akallen nasu, can Nawal tayi winning, Rahma ta ce, " bata yardaba, sai dariya da murna Nawal takeyi.
    Nawal tamik'ama bobo handle d'inta, papa kar6i handle d'ina kuyi da momy naje nayo fitsari.
    Babu musu yakar6a, tanufi d'akinsu da gudu, shikuma yasakko k'asa kan carpet Kusada Rahma, har jikinsu nad'an gogar juna.
   Kad'an Rahma tad'an muskuta suka fara, anutse kowa ke controling d'in motarsa, saidai awannan karon Rahma tafi bobo iyawa.
    Dariya ta kufcema Rahma Dan ganin yanda bobo kek'ara k'aimi, shima dariyar yafara yana k'ara gudu danson wuceta amma yakasa, Nawal tafito taje bayan papanta tad'ane tana kallonsu, dariya sosai sukeyi kowa yana Nuna kwarewarsa, Nawal tana k'ara zugasu, momy gooo karki bari papa yakamaki, idan sukayi kamar zasuyi karo Nawal tabuga k'ara tamkar wad'anda suke agidan kwallo, bobo yana ganin Rahma zata masa game over sai kawai yafara k'ok'arin kwace handle d'inta, nanfa suka kaure kokawa suna dariya, itama Nawal tad'aresu tana dariya wai momy tafi papa k'arfi.
     Sun shagala sosai wajen tumurmusar juna, hardai Bobo yasamu nasarar kwace handle d'in Rahma, ya ce, "saidai kar kowa yayi winning, dadai nayarda na d'auki game over.
    Rahma tarik'e ciki tana dariya, cikin dariya ta ce, " wannandai game ta fin k'arfice, miyasa zaka karaya dawuri haka?, hhhhhh.
    Tsayawa yayi cak yana kallonta Dan dariyar tayi mata bala'in k'yau, jiyake kamar karta daina, yalumshe ido ahankali yabud'e akan Rahma data fara tsagaitawa da dariya tana d'aukar d'ankwalinta daya fad'i can gefe wajen kokawa.
   Shi saima yanzu yalura da bak'in gashinta sid'ik irin Wanda ake kira roba roba d'innan, Dan yacika kan dam, ta d'aureshi kamar acuci, dukda bata saka masa mai amma sai kyalli da shek'i yakeyi, ahankali yakai hannu yakama gashin nata mai d'an tsawo babu laifi, Dan dazata cire ribom d'in to zai sauka harkan kafad'arta.
    Jin hannunsa cikin gashinta yasakata dawowa hayyacinta, tayi saurin matsawa tareda d'aura d'ankwalinta.
    Murmushi shima yayi, yatashi yakoma bisa kujera shida Nawal.
   Itakam duk kunya tarufeta, mik'ewa tayi zata gudu d'aki, muryarsa ta dakatar da ita.
    Abamu abinci muci ko babyna?.
   Da Sauri Nawal ta ce, "eh momy yunwa mukeji.
   Dole Rahma tadawo tagabatar da abinda yakawo, zata tafi d'akinta yay saurin rik'o hannunta, cikin sauri tajuyo, aranta tace waishi baya ganin Nawal mai shegen wayau da surutu.
     Hannunta tashiga k'ok'arin kar6ewa, shikam yasake mata hannu, ina zaki? yafad'a adake.
   Ganin yanda yay magar saita kama kanta, kanta ak'asa ta ce, " d'aki.
   Abincinfa?.
Nak'oshi.
  Ashe zanmiki d'ura.
   Da sauri ta ce, "tom zanci.
    Murmushi yayi, itakuma tadawo ta zauna, babu yanda zatayi dole tasaka hannu sukaci naman a filet d'aya su uku.
    Dad'i Nawal taketaji, Dan haka idan tad'ako nama tasakam Rahma abaki saita sakama bobo shima abaki, cikeda nishad'i sukecin naman, bayan sun gama aka dawo kan ice-cream, babbar roba d'aya sukesha su uku.
   Rahma dukta kasa sakin jikinta, saboda kunya, bobo yana kula da ita amma ya share, yad'auke kansa yana maida TV wajen labarai.
     Nawal tad'ebo ice-cream tabama bobo abaki, takuma d'ebowa tabama Rahma.
   Shima bobo yad'ebo yabama Nawal, Yakuma d'ebowa yanufi bakin Rahma, k'asa tayi da kanta wai ita kunya, muryarsa kasa² kamar mai rad'a ya ce, " zan zuba abakina sannan nakama bakinki najuye miki, kuma agaban Nawal komai zai faru.
   Babu shiri Rahma tabud'e baki yazuba mata ta shanye.
   Nawal ta ce, "momy kema kibamu to.
   Babu yanda Rahma zatayi tunda an rutsata, ta d'ebo tabama Nawal, takuma d'ebowa amma takasa d'agowa.
   Cikin shagwa6a bobo ya ce, ''baby kinga momyn ki ko tak'i tabani ni.
   Lah momy kibama baby karyayi kukafa.
   Bak'aramar dariya abin yabama Rahma ba, wai k'ato dashi yanama 'yarsa shagwa6a, tana k'umshe dariya tad'ago tabashi shima, shikuma yad'aga mata gira.
    Kanta ta tura cikin cin yoyinta Dan abin yabata matuk'ar kunya.
   Hakadai suka riski wannan dare cikin nishad'i, bayan angama labarai suka tafi d'aki, shima yatafi d'akinsa cike da kewarsu, da mamakin Kansa a yau, yana Abu tamkar bashiba.
    Wani 6angare na zuciyarsa ya ce, " kafad'a tarko ne..............

*_Happy juma'at Mubarak my lovely fan's._*
❤❤❤❤💋💋💋💋💋💋💋




luv  you all my fan's
   (((S)))....2017

Continue Reading

You'll Also Like

1.7M 69.5K 79
ငါလား.... စိတ်ချ...... နိဗ္ဗာန်ရောက်ရင်လည်း မင်းကိုပဲ ချစ်နေအုံးမှာ.......... သုနေတင်ထွဋ် ကမ္ဘာပျက်သလို လေပြင်းမိုးသံတွေထ...
87.1K 12.1K 85
ကျန်းမိသားစုမှာ သမီးနှစ်ယောက်ပြီး တစ်ယောက်စီက ပန်းကလေးတွေနဲ့ ကျောက်စိမ်းရုပ်လေးတွေလို လှပကြတယ်။ အငတ်ဘေးရာသီနဲ့ ကြုံကြိုက်လာတော့ အသက်ဆက်ရှန်သန်ဖို့အရေ...
2.4M 375K 159
English Title- After a Flash Marriage With the Disabled Tyrant Author- 惗肆 English Translator- [Hua]rricane Status in COO- 94 chapters &17 extras All...