ABDUL-MALEEK (BOBO)

بواسطة BilynAbdull

203K 11.2K 90

Labarin mai nuni da muhimmancin biyayya ga iyaye, gujema son zuciya, soyayya, zuminci, tare da cakwakiya tsak... المزيد

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
31
12
13
14
15
16
17
18
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53

19

3.2K 213 0
بواسطة BilynAbdull

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 20

washe gari

  Rahma tatashi tayi duk abinda tasabayi dukda tasan yau weekend Bobo bazai fitaba, tana cikin saka turare a falo bobo yafito sanye da jallabiya ruwan toka mai gajeren hannu, rissinawa tayi ta gaidashi, kamar yanda yasaba ya amsa da lfy.
    Amsa gaisuwar nan nabama Rahma haushi, amma babu yanda zatayi.
   Yad'anbi falon da kallo komai tsaf, gawani k'amshi na musamman, yana jin dad'in kasancewarta mace mai tsafta.
   Itadai cigaba tayi da abundan takeyi.               Ya ce, "bari nad'anje wani waje nadawo.
    Aranta tace kofa wanka bakayiba, amma afili ta ce, " to ga Break.
   No barinaje nadawo, aiba dad'ewa zanyiba, yafad'a yana ficewa.
   Itama ta ce, "ALLAH ya tsare.
   Dukda yafita amma yajiyo addu'arta.

Bayan takammala saka turaren zuciyarta tabata shawara dataje ta gyara masa d'akinsa, kamar bazatajeba saikuma tatuna nasihar mahaifiyarta da ummansu Basma.
   d'akin tanufa da tunanin ALLAH yasa bai rufeba, tana tura k'ofar tabud'e, k'amshinnan yana nan kamar kullum, yau tanutsu takalli ko ina na d'akin, komai farine tas, aranta tace farin Abu name tsaftane.
     Sai manya manyan hotunanan Ni'ima Maman Nawal, bani gurin ita kad'a, wani gurin kuma shida ita.
     Ko kad'an bataji haushiba bare kishinta, Bata 6ata lokaciba tafara gyara ko ina, Dan danan tagama d'akin yak'ara d'aukar haske komai yana d'aukar ido.
    Bathroom tashiga zata wanke saitaga kaya ajik'e abokiti.
    Shiru tayi tana tunanin ta wanke kota barmasa abinsa, wata zuciya ta ce, " ki wanke, kobabu komai zaki samu lada aii.
   Haka tazauna tahau wankin gajerun wandunansa da vest, akunyace take wankin tamkar tana gabansa, gudu gudu sauri sauri tagama bataso yazo yataddata tanayi.
   Dandanan tagama tawanke bayin, tad'auki kayan tafito waje, acan baya taje tashanyasu sannan tadawo d'akinta tashiga wanka, Dan Nawal bata tashiba.
  
Shigarta wanka babu dad'ewa yashigo gidan, d'akinsa yanufa kai tsaye, baki da hanci da ido yasaki yana kallon d'akin NASA, yalek'a bayi nanma fes, bokitin daya jik'a kaya wayam, wani lallausan murmushi yasaki, labulen window d'insa yad'aga, can yahango kayan ashanye.
   Jiyay wani Abu nata6a zuciyarsa, afili ya ce, ''ALLAH yaymiki albarka.
   Fitowa yayi yanufi d'akin Rahma, hakan yayi daidai da fitowarta daga wanka, daga ita sai guntun tawul iya cinya.
   Wata tsayuwar sojan badakkare bobo yayi, sai Raba idanu yake akan Rahma, da wannan munafikin kallon nasa k'asa k'asa.
    Itakam dukta rikice, waige waigen abinda zata rufe jikinta kawai takeyi, can ta hango hijjabin sallarta, amma dole saitabi tagabansa zata d'auka, ganin haka saikawai takoma cikin bayin da sauri.
   Murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya, yak'arasa inda hijjabin sallarta yake yad'auka, ahankali yak'arasa har k'ofar bayin ya kwankwasa, Rahma dake jingine da k'ofa tagwalo ido waje, k'irjinta sai dukan Tara Tara yakeyi.
   Yak'ara kwankwasawa.
   Muryarta narawa tamkar zatayi kuka tace yes, yanda tayi maganar tabashi dariya amma saiya gimtse ya ce, "bud'emin k'ofar.
     Innnalillahi tace azuciyarta, wai mi mutumin nan yake nufi.........maganarsa ta katse mata tunani, " wai kobaki jinane?.
   Bayan k'ofar takoma tala6e sannan tabud'e, gaba yay tamkar zai Shiga, saikuma yamik'a mata hijjabin, dasauri takar6a tamaida k'ofar burum tadatse.
   Girgiza kai yayi yanad'an ta6e bakinsa, yazauna bakin gadon yana shafa kan Nawal daketa barcinta hankali kwance, shi mamakin kansama yakeyi, wai miyake jirane?, zuciyarsa ta ce, "kanason sake kallon Rahma ne.
   d'an tsaki yaja yamik'e yafice, shi adole zuciyarsa tayi k'arya.

Saida taga yafita sannan tafito, taje tasakama k'ofar key, sannan tazauna tagyara jikinta, tasaka Riga da wando na Pakistan, nakula tana son irin kayannan sosai.
   Nawal ta tashi itama tayimata wanka tashiryata cikin wandon Jin's da pink d'in T shert mai k'yau.
   Falo suka fito, fitowarsu babu dad'ewa shima ogan yafito, haryayi wanka yashirya cikin jins blue da farar Riga sai zabga k'amshi yakeyi.
   dinning suka nufa, Rahma sai sinne kai takeyi Dan kunya, shikam ko'a kwalar rigarsa, yanacin abinci Nawal namasa surutu, iyakarsa Yamata murmushi koya d'aga kai.
   Rahma ta ce, " azuciyarta, muskili kafi mahaukaci ban haushi.
    Suna kammalawa Nawal taja hannun Rahma wai suje tamata lilo, fitowa sukai sukabarsa kwance saman doguwar kujera yana kallon film.

Sunacan a lambu Rahma NATA biyema Nawal suna lilo, jiyay falon babu dad'i Dan haka yafito, jiyo dariyarsu alambu yasashi nufarcan, Rahma na zaune akan lilo, Nawal na shillata suna dariya, k'arasowarsa yasa Nawal cewa lah papa kaima zona lilaku.
    Kai ya girgiza mata alamar A'a.
   Takwa6e fuska zatayi kuka, cikin takun k'asaitarsa yak'arasa wajen lilo d'in, Rahma tayi yunk'urin sauka Nawal ta ce, "momy kubiyufa zanyimawa, sandarewa Rahma tayi azaune, kafin ta farga Bobo ya haye lilo d'in amma d'an nesa da ita.
    Da k'arfi Nawal ta hankad'a lilo d'in, aiko sukayi gaba kamar zasu fad'i, da Sauri Rahma ta ruk'unk'ume Bobo, shima yarik'eta.
    Nawal Yar kwal uba tacigaba da lila lilo da k'arfi, basuda za6i bayan rik'e junansu dak'yau, Nawal dai sai dariya takema iyayen nata, saida tagaji Dan kanta sannan tadaina lilasu.
    Bobo yabud'e idanunsa ahankali danjin lilo ya tsaya, ga Rahma na mutsu2n kwace kanta, yana sakinta tasauka, da Sauri tabar wajen, binta da kallo yayi yana murmushi, Nawal takatse masa tunani, baby d'orani muyi tare tunda momy tagudu.
   daukarta yayi yad'ora sukacigaba da lilonsu zuciyarsa cikeda tunani kala kala.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
         Safna zaune gaban Abba da ummi da alama fad'a ake mata, Dan fukarnan adagule take.
   Abba ya ce, " wlhy nabakinan da wata uku zuwa hud'u kifito da miji a had'a aurenku keda amira, inbandama auren ameerar da sati biyu zan baki, amma Abubakarne yaceceki ya ce, "abari ahad'a bikin dan a samu sauk'i."
   To saikiyi gaggawar sanar da Wanda kikace kinason harkikaso wulak'antamu akansa.
    Insha ALLAHU Abba zan kawoshi, nidai kuyi hak'uri kubar ganin laifina, ALLAH yariga yarubuta Dama shid'in Mijin k'anwatane baniba...
    Dallah yimana shiru!!, ummi takatseta atsawace, Mara mutunci kawai, Indai duniyace aigaki gata nan, kuma koyaya Wanda kikace kinason yake wlhy haka ZAMU aura miki shi, kijecan kiji da bak'in halinki, tashi kibamu waje mu.
   Mik'ewa Safna tayi tabar falon tana k'unk'uni.

Na ce, " ALLAH ya shirya to.

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
       Ad'an hanzarce takeyin aikin gidan, Sauri take tagama dawuri taje tayi girki Dan maigidan ya ce, "mata yau abokinsa zaizo da iyalinsa, tagama komai tsaf har girkin ta kammala d'akin bobone kawai yarage mata shima Dan yana kwance ad'akinne.
    Saiwajen 12 yafito daga d'akin yafita danufin siyo ruwa datace masa babu.
   Yana fita tashiga d'akin Dan gyarawa, tagama aikinta lfy lau, tsautsayi yasa takai hannunta kan wani hoton Ni'ima datayi bala'in k'yau, Ashe bai zauna da k'yauba aiko yafad'o jikake taratsatsa!!! ya tarwatse ak'asa abinka da gilas.
    Hakan yayi daidai dashigowar Bobo falon, da hanzari yanufi cikin d'akinsa, aiko abinda yake zarginne yagani, dandanan fuskarsa ta canja kama idonnan sukayi ja danshi aganinsa da gangan Rahma tayi saboda batason ganin hotunnan tunda dai yasan mata da kishi.
    Tunda yashigo jikinta ke rawa, tabud'e baki arazane zatayi masa magana yadaka mata tsawa.
    Dallah yimin shiru, dama kina shigowa gyaramin d'akine danki kashemin hotuna?, to wlhy idanma kishi kikeyi da ita kidaina Dan babu yanda kika iya da ita, wannan dakike gani itakad'aice nabawa zuciyata, daga itakuwa babu wata mace dazata samu haka daga gareni, wlhy akan wad'an nan hotunan sainayi mugun sa6a miki, banason cikin da iskanci.
    Rahma tamatso danufin tsugunnawa tabashi hak'uri amma abisa tsautsayi ta taka gilas ak'afa, runtse idonta tayi saboda azaba, dama ga hawaye tuni sun wanke mata fuska.
    Tsawa yasake dama mata, dallah malama fitarmin ad'aki, kuma karna sake ganin k'afarki ad'akina.
   Ran Rahma ya6aci sosai ganin yanda yake cimata mutunci akan hoto, Wanda inyanzu yaso zaikai amaida gilas d'in daya fashe, haka tataka k'afa tabar d'akin tana kuka, tanazuwa tazube akan gado, ga azabar da k'afarta take mata amma bata kulaba, sai kuka maicin rai data saki.
   Duk abinnan yake faruwa Nawal tana can baya tana wasa, Rahma taturata wajene dantabarta tayi aiki, batason surutu.
     
Bobo kam tana fita yadurkushe agaban hoton, d'agosa yayi yana gogewa tamkar zai fasa kuka, muryarsa na Rawa ya ce, "kiyi hak'uri Ni'imana bada sanina tayiba, ALLAH ya gafarta miki ya yafe miki kinji.

Nawal tashiga d'akin Rahma tana kwala mata kira momy! Momy!!, tak'arasa cikin d'akin da murnarta, amma ganin jini ahanyar sai jikinta kuma yay sanyi, tak'arasa har bakin gadon tana kallon k'afar Rahma da gilas ke jiki ga jini yanata zuba ak'asan wajen.
   Fitowa tayi da gudu tanufi d'akin Papan ta, har yanzu yana gaban  Hoton adurk'ushe, papa papa zokaga k'afar momy jini yanata zuba dayawan tsiya.
   d'agowa yayi yana kallonta, yanda tabirkice shima sai jikinsa yay sanyi, mik'ewa yayi suka nufi d'akin Rahma d'in, gsky shima abin yabashi tsoro ganin jinin dad'an yawa, ga gilas babba kafe ak'afarta, tana kwance rubda ciki tana darzar kuka.
   Tsugunnawa yayi Kusada k'afar yakama gilas d'in zai cire tasaki wata k'ara wadda tasaka Nawal fashewa da kuka itama, ga gilas d'in yakafe dayawa, ganin karya k'ara jimata ciwo yasa yamik'e dasauri yaje d'akinsa yad'akko key d'in mota.
    Dawowa yayi ya ce, " tashi muje asibiti acire miki wannan kwalban.
    Banza tayi masa tacigaba da kukanta, wani haushi yak'ara turnik'eshi, baisan lokacin daya sungumetaba yay waje da itaba, Nawal nabinsa abaya, Nawal tabud'e masa k'ofar motar yasakata aciki, suma suka shiga sai asibiti.........






luv u oll my fans
(((C)))..........2017

واصل القراءة

ستعجبك أيضاً

568K 30.3K 61
📌 fic ပါ အကြောင်းအရာများသည် သာသာ့စိတ်ကူးကမ္ဘာလေးအား ဖန်တီးထားခြင်းသာ 📌 ဆယ်ကျော်သက် အချစ်တွေက မတည်မြဲနိုင်ဘူးတဲ့...အဲ့စကားပြောတဲ့ စောက်ပါးစပ်တွေ ပိတ...
565K 73.2K 102
This novel is not mine. Just a fan translation. Unicode +Zawgyi Author - 桃花引
1.1M 57.8K 48
အမိန္႔စည္း+သခြပ္႐ိုး ( ႐ွင္မႈန္းနံ႔သာ) အမိန့်စည်း+သခွပ်ရိုး ( ရှင်မှုန်းနံ့သာ) ခြင့္ျပဳခ်က္မရပဲ ငါ့အနားကထြက္ခြာခြင့္မျပဳနိင္ဘူး အသက္နဲ႔ခႏၶာတည္ျမဲေနသ...
251K 26.9K 33
ရိုးရိုးအချစ်ဇာတ်လမ်းလေးတစ်ပုဒ်ပါပဲ