Chapter 17

587 36 7
                                    


Daukar wayar yayi batare da ya answer ba ya nufi kofa inda ya bude ganin wacce ke turo kai dakin yasa ya tsaya yana kallon ikon Allah
" Lafiya!"
Murmushi tayi Tana kallonsa yama manya meke hannunsa batare da yasan ya danna ba,
" kayi mamakin ganina a kofarka a wannan lokacin Ko"
Shiru yayi ya koma bakin bed dinshi ya zauna yana kallonta
"ZAYNA!"
Abunda SHAZMAH tafada kenan ta tashi da sauri tayi toilet ganin innawuro na zaune Tana karatu gun ba halin da zata bace
Murmushi Saal yayi yana kallonta " ba abun mamaki bane sanin yadda yan mata keson kasancewa Dani
" zaiyu kina daga cikin wadanda ke gama da wannan heart illness din"
Murmushi tayi ta taka zuwa gabanshi ta zauna kusa dashi matsawa yayi sanda tayi murmushi
Takai hannunta jikinsa da sauri ya tashi agun
Murmushi Tana cizar lebenta " wow I believe kai din namiji ne da kowa ce irin mace zata falling
" sai dai kash kuskuren dakayi kenan daka kasance kyakyawa a cikin sauran mazan Wanda aganina sunfika kira but kai din na daban ne"
Duk wannan zantukan da take ko kallonta SAAL baiyi ba ya jawo wani duba wayarsa yayi dan sai a lokacin ya tuna SHAZMAH ta kirashi.

SHAZMAH Tana ta kokarin ta bace a toilet din abun sai yaki Sam tsafin nata yaki yi
Saal ganin har tayi picking yasa yayi tsaki
ZAYNA kuwa ganin irin abubuwan da ake a TV din yasa tayi murmushi Tana kallonshi
" wow romance film kake kallo Wanda kusan duk sex yafi yawa ma ciki Nima nafi son irinsa"
Kallonsa ta kuma yi Tana murmushi " killing me softly" wow shine ko favorite dina how I wish nida kai zamu......." kallon daya mata ne yasa tayi shiru,
" I think tunda ba ajiya kika bani ba baki da abunda zakiyi a nan just leave in aka ganki zan iya samun problem please just go"
Tashi tayi ta bishi kan couch din ta zauna a gefe
Tashi yayi ta riko hannunsa " well I am very sorry sweetheart not so easily dan nazo canza maka duniya"
Wani irin kallo ya mata me tare da alamomin tambaya
Take wani abu yafara fita a idonta zuwa nashi jikinsa yafara rawa sakin hannun nasa tayi take yayi kasa
Tsallakeshi tayi ta wuce inda ta bace bat
Bacewarta tayi dai2 da zuwan SHAZMAH dakin cikin rudu SHAZMAH tayi kan SAAL,
" SAAL! SAAL!! SAAL!!! Meya faru please ka bude idannunsa dan Allah" Tafada tana girgiza shi.

Ganin tayi2 yasa ta rufe idannunta ta daura hannunta kan kirjinsa a hankali take motsa lips dinta
Baa dau lokaci ba Saal yayi ya motsa inda yafara tari
Tashi yayi a hankali yana kallonta duk tayi hawaye " SHAZMAH meya faru me kike a dakina"
Nan taji dadi gashi baida memory din abunda yafaru Sam tashi tayi ta cire shi a jikinta
" bakomai kawae nazo wucewa na leko naganka kwance bansan meya same ka ba"
" oh sorry maybe gajiyar aiki ne bansan ma na sauka na kwanta a kasa ba"
Yafada yana shafa Kansa " toshikenan bari na tafi"
Sallama sukai tafita inda sai a lokacin yafara tunanin meya faru yaushe ya kunna Tv Sam
Baida memoryn komai daya faru dashi haka dai ya girgiza kai ya koma ya kwanta ganin film din dake playing yasa mamakinsa ya karu cewan harya kunna Tv.
SHAZMAH cike da bacin Rae ta fita inda hankalinta ba abunda take Ji irin taje taga ZAYNA taji metakeso,
" bari innawuro tayi bacci saina tafi can din"
Dakinsu direct ta wuce inda ta tarar da innawuro zaune Tana Jin sallamar SHAZMAH ta kalleta
Cike da mamaki da tambayoyi dake ranta kan SHAZMAH.

Gidansu direct ZAYNA ta bayanna kamar ba abunda yafaru ta iske SAHIMA na kallon zeeworld
Da alama series din da take kallo yana mata dadi sosai,
Kuma Tana fahimatar abunda suke cewa bata San da shigowar ZAYNA ba sam,
Kallonta ZAYNA ta tsaya tanayi ganin yadda ta maida hankalinta gaba daya kan TV din
A hankali taje ta bayanta ta tureta a tsorace SAHIMA ta juyo Tana kallonta "hahahah"
Dariya ZAYNA tasa Tana kallonta sosai ran SAHIMA ya baci fuskarta ba alamun Dariya sam
" I am very sorry nazata bil'adama kadai kejin tsoro"
ZAYNA Tafada tana rike cikin ta da sauri SAHIMA ta kalleta take ZAYNA tafara tari tana mika ma ZAYNA hannu alamun
Ta yi hakuri ta taimaketa amma Ina tuni takai kasa yayinda SAHIMA ke kallonta idon
ZAYNA sunyi ja sosai shigowar MAALIK ne yasa SAHIMA ta saketa inda ta tashi da gudu Tana rike wuyanta tashige daki,
" SAHIMA meya faru kikai ma ZAYNA haka"
Kallonsa tayi ta koma ta zauna " ba hurumin ka bane inaga zaifi idan kyau minding din business dinka"
Murmushi yayi Jin tafara iya turanci sai dai yadda kalaman ta ke fitowa hakan bai taba faruwa tsakaninsu ba tabbas
Yanzu bata son shi " amma meya faru rana daya haka".

Amsar tambayar da bashi dashi kenan girgiza kai yayi " bari na duba ZAYNA amma karki kuma abu haka"
Ko Juyowa batai ta kalleshi ba Wanda inda ada ne bazata yarda ba har yaje gun ZAYNA,
Yana shiga tarar da ita yayi kwance idanunta a lumshe Jin shigowar sa yasa ta bude idanunta,
" ya kinyi abunda nasaki"
Tashi tayi ta zauna Tana murmushi " bama da matsala nasan zuwa Safiya zakaji labari"
Karasawa yayi  gabanta yayi hugging dinta Wanda take yaji wani feelings na taso mishi
Jin yayi shiru yasa tadan cireshi a jikinta
" ka manta dawa muke zama agidan"
Tashi yayi yayi ya mata sallama yafita bai koma falo ba dan dadin da yaji dakinsa ya nufa direct,
Shiru ZAYNA tayi tare da lumshe idonta tuna shaheed dinta take nan take ta tashi tafara shiri,
Har wannan lokacin kallo SAHIMA take ganin ZAYNA cikin shiri yasa take tambayar ta
" Ina zakije a daren nan"
Murmushi ZAYNA tayi tare da tabe bakinta " gun masoyina!"
Tabata amsa a fakaice ta bace batare data saurara abunda SAHIMA zata fada mata next ba
Tabe baki SAHIMA tayi " ke kika sani wai masoyi" tayi murmushi ta cigaba da kallonta abunta dan Tana Jin dadin kallon sosai.

Kwance yake yana baccinsa sanda ta bayyana kallonsa take karasawa tayi kusa dashi ta tsura mishi ido
" so cute"
Tafada a hankali Tana murmushi gyara kwanciyar sa yayi dai2 sanda takai hannunta kan kansa,
Take ya cafke hannun nata " SHAZMAH karkije ko ina" wani irin tukukin haushi da bacin rae ne taji ya daki kirjinta
Tashi tayi ta cire hannunta harta juya taji ya cafko hannunta inda yaja shi yasa kanshi akai,
Har wani murmushi yake batare da yasan hannun waye ya rike ba sam kamar mafarkin SHAZMAH yake yayi nisa
Janye hannunta tayi da karfi Wanda hakan yayi sanadiyyar bude idanunsa da sukai ja
Tashi yayi da sauri ganin ZAYNA " yaushe kika shigo me kike a nan da wannan daren"
Kallonsa tayi tare da tabe baki " how can you know na shigo kana mafarkin abar sonka"
Tsoro ne ya shige shi yana kallonta " aa banyi mafarkin kowa ba mafarkin ki nake"
Murmushi tayi sanin Tana iya juya shi kawae tasan ba zata iya cire SHAZMAH a cikin rayuwarsa bane,
Tausayinsa taji tuna yadda ya shaku da SAAL gashi da safe zaiji labarin mutuwarsa
Tashi yayi ya nufi inda take tsaye ya riko hannunta " look I am very sorry" Yafada yana rike kunnensa........




                     
                        Sai mun hadu a next page in Allah yakaimu👌

WACECE SHAZMAHOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz