Chapter 28

737 43 2
                                    



" Nifa gaskiya Ni'ima inatsoron shiga dajin nan kinsan da ba kasar mu bace nan",
" oh furera ko kinmanta gun boka ne" girgiza kai haj.furera tayi amma fuskarta fal tsorone,
" uhm ni bama wannan ba wannan matar fa bata Jin Hausa ko turanci Sam in mun shiga gun da ba network taya zamu kira waya amata bayanin abunda mukeso",
Kada kai haj.furera tayi tare da yarfe hannu,
" ahto nidai inkinbi shawarata tun dare bai mana ba mujuya",
Tabe baki momy tayi " tabdi ba zanyi wahalar banza ba sai naga abunda ya ture ma buzu nadi yau",
Haj.furera bata Kara ma momy magana ba a cikin motar su hudu ne su biyu a baya sai matar dake zaune gaba tare da driver din,
Cikin su ba Wanda ya kuma cewa dan uwansa komai har saida suka zo wani kauye,
" kila nan ne ko munzo ne",
Shiru matar ta musu batare da ta saka driver din ya tsaya ba,
Sai da suka wuce kauyen tafiya me nisa matar ta juya ma driver din da yare kan ya dakata,
Tsayawa yayi a kauyen tafito katuwa ce baka amma tubarkallah ba za'a kirata da mummuna ba,
Kana ganinta kasan kudi sun ratsa ta itama sosai.

Ganin ya tsaya haj.furera tafara zazzaro idanu alamu ta musu dasu fito,
" kuttt gaskiya bazan biki ba saikin dawo",
Tsaki haj.niima tayi " haba da girmanki kina abu kamar wata yarinya na dauko dallah sauko muje",
Sai da haj.Ni'ima tayi da gaske sosai kafin haj.furera ta sauka daga motar inda,
Suka bar driver a tsaye suka nufi dajin sosai tsoro ke ziyartar zukatansu ganin dajin ba irin Wanda suka saba gani a Arewa ba,
A cikin dajin banda kukan tsuntsaye babu abunda akeji,
" gaskiya Ni'ima mukoma" tafara kokarin juyawa,
Kamo hannunta momy tayi tana kokarin fisga matar nan ta juyo ta kallesu,
Sa yatsanta tayi saman lips dinta " shhhhhhhh",
Ba bata lokaci haj.furera takama bakinta da hannayenta dan tabbas tafara tsurewa,
Sunyi tafiya me mugun nisa duk sun galabaita banda ruwa ba abunda suke bida a wannan lokacin,
Zama haj.furera tayi a kasa ta sauke numfashi dakyar suka samu ta tashi tabisu,
Daga nesa suka hango hayaki na tashi sai wata irin bukka dan karami kwali daya tal,
Alamu matar tayi musu dasu karasa gun bukkar a tunaninsu anzo ne har suna washe baki,
Bama kamar haj.furera wacce gaba daya take ji duniyar ta na juyawa Tana Dana sanin bin kawartata.

Fitowa tayi cikin kayan bacci riga da Wando kanta ba dan kwali sai hula data saka,
Kana iya ganin gashinta me tsayi daya sauka,
Kitchen ta nufa dan ganin innawuro zata tambayeta abu,
Zaune yake yana latse2  na wayarsa daya saba Jin motsin mutum yasa ya dago,
Yana duba mai fitowar ganinta kawae yayi ba make up amma ta masifar masa kyau kasa,
Kwakwaran motsi yayi bare ya daga idonsa daga kanta,
Ita sam bata da mutum ba dan tasaba basu tashi da wannan sammakon amma Yau sai akayi sa'a,
Shaheed ne daga sama yana hango fitowar ta da yadda Saal ke kallonta yana mamaki,
Tazo zata wuce ta kusa da Saal batare data lura ba tayi tuntube da kafarsa ta tafi luuuuu kamar zata ci kasa,
Taji anfizgota cikin zafin nama ta fadi a kafadunsa,
Idonsu ne ya sarke cikin na juna suka kafa ma junansu ido,
Shaheed dake kallon abunda yake faruwa wani irin bakin ciki ne yake taso mishi,
Me mugun zafi baisan sanda ya matse glass cup dake hannunsa sukai tassss suka tarwatse ba,
Karar fashewar glass dinne ya dawo dasu daga hayyacinsu inda suka saki juna da sauri,
Tare suka daga kai zuwa kallon inda sukaji karar shaheed ne tsaye hannunsa sai digan jini yake.

Da sauri Saal ya haura saman yana mai tambayoyi ita kuwa ganin hakan yasa tayi kitchen da sauri,
Dan tabbas Tana zargin ganinsu a hakan da yayi ne tunda yace mata bakyau yin hakan Sam a addininsu,
" please kaje kashirya is nothing zanyi dressing wound din",
Girgiza kai Saal yayi " just wait for me I will be right back",
Cikin rudani Saal ke duka wadan nan maganganun,
Shaheed mamakin yadda Saal ya rude Kansa yake  girgiza kai yayi,
" how I wish you are not my brother I will have.....",
Sai kuma yayi shiru kamar Wanda ya tuna wani abu,
Cikin sauri Saal yadawo dauke da first Aid box inda ya gyara mai ciwon yasa mai bandage ajiki,
" please inkaje office kyau tetanus" kallonsa shaheed yayi yana mai Dariya sosai,
" and you think I don't know that",
" oh yes nasani kai doctor ne sorry brother",
Nan kowannensu yayi nasa hanyar kowa da abunda yake sakawa a ransa tabbas wannan shine love triangle din yaya da kani a gu daya,
Tunda tashiga kitchen take murmushi tuna abunda yafaru tsakanin ta da Saal wani irin dadi take ji a ranta da jikinta sosai.

" kintashi",
Aunty hanne ta tambayeta yayinda innawuro ke tsokanarta,
" jiya kinsha bacci har ba'a magana gashi Yau kintashi cike da nishadi kodai akwai abunda kike boye mana",
Rufe fuskata tayi tana dariya " aikam nima haka nagani duk ta sauya",
Dariya dukansu suka kwashe dashi a kitchen din,
SHAZMAH kuma fita tayi daga kitchen din ta koma daki Tana zuwa daki tayi tsalle tafada kan gadon,
Tana ajiyyar zuciya dadi take ji sosai ta lumshe idannunta inda take Kara hango abunda yafaru,
Sa hannu tayi tana murmushi Tana Kara rufe idannunta,
Shima Saal a bangarensa kusan Hakanne ke faruwa dan bakaramun dadin,
Abunda yafaru yayi ba har wani Kara rungume hannayensa yake a kirjinsa " oh my god I love her",
Ya fada a hankali.
" Aunty Anya SHAZMAH lafiya naga kullum sauyawa take",
Murmushi aunty tayi Jin abunda innawuro ke fada,
" uhmm innawuro ae dagani har aunty yanzu kinfimu kusa da SHAZMAH yakamata ace kinsan me ya kawo wannan sauyin,
" kodai akwai samari makarantar kune dan da alama kamar soyayya ce ke dawainiya da ita",
Kama baki aunty hannu tayi " uhm lallai mairo ansan soyayya to yayi kyau" Dariya su duka suka kwashe dashi,
Dan sun dan sun Dana rashin kunya gabanta.

Kai tsaye bukkar suka nufa inda take suka ga wata mata ta bayyana a gabansu,
Tsalle sukai su biyu suka rungumi juna Dariya tasaka masu,
" barks da zuwa Hausa akwai" Tafada cikin tsamin hausarta da bata wani iya sosai ba,
Jikinta farin yadine sol akayi daurin kirji dashi,
Haka kanta ma farine sol akayi dankwali dashi,
Nuna masu fararen yadin tayi daga gefe cikin wani kwando Tana dariya,
Alamu dayar matar ta musu dasu dauka su saka ta musu nuni da bukkar yayinda waccan ta bace take,
Cike da tsoro suka diba yadukan suka shiga " Ni'ima yanzu sai mun cire kaya ma gaskiya bazan iyaba",
Jawo hannunta tayi suka shige bukkar haka dole suka sauya kayan nasu zuwa wannan yanayin,
Itama matar haka tashiga tasaka nata daurin kirjin tafito,
Inda suka kama wata yar siririyar hanya sun danyi tafiya mai nisa kafin suka fara ganin jeren mataye masu irin kayan su,
Farare sai dai ko wacce dauke take da abubuwa wata insun wuce suganta dauke da koko,
Wata kuma dauke da dai abubuwa kala kala sunyi layi har suka kusa fara hango jan kyallayen dake jikin wajen tsafin,
Inda suka fara hango kana nun yara zazzaune kowa suma da abunda yake agun,
Kamar gunkuna dan Sam ba masu motsi ciki.

Sosai hankalin su momy ke tashe dan wasu irin abubuwan tsafi tagani Wanda Sam bata taba gani ba duk bin bokan ta ta zama bakuwa a wannan guri,
Suna shiga gun wajen yayi wani irin duhu,
Take wata irin dariya ta bayyana Mara dadinji sosai haj.furera ke shirin tashi gudu,
Inda momy ta damketa da karfi dan ta tsorata sosai,
Wani irin haske ne ya bayyana take sai ganin dan yaro sukai gabansu Wanda baiwuce,
1yr ba yana musu dariya kafin su gama mamaki wani yaron ya juya zuwa wata irin halitta me,
Manyan hakora ga kuma gashi sam duk cikinsu banda wannan bayerabiyar ba Wanda bai tsorata ba ciki,
Yayo kansu ae tuni suka rungume junansu dan kasa gudu ma sukai abun ya bace but dakyar suka bude idannunsu,
Inda suka gansu a wani irin mugun daji take,
Waige2 suka fara dan ba nan suke ba nan idanunsu yakara raina fata basu aune ba wani katon Zaki yayo kansu,
Wannan karon kasa koda kwakwaran motsi sukayi yayinda haj.furera ta saki fitsarin wahala take,
Kasa ihu tayi ma Sam a wannan lokacin duk suka tsaya cak a wannan lokacin tabbas in za'a gwanda jininsu to tabbas ya hau iya hawa................


     

                 Muhadu a next page ayi ta hakuri dani please bayin Allah nagode da kulawarku....👏👌

WACECE SHAZMAHWhere stories live. Discover now