Chapter 9

921 76 3
                                    




" Tafiya kauye yazama dole",
Tuni idannun momy ya Raina fata yayinda Saal da hadil ke goyon bayan mahaifiyar su dan basu son zuwa,
Shaheed ko shiru yayi dan mamaki yake dan tunda yayi wayo dady baikaisu kauye ba ko zancen ba yayi sai yau,
" haba alha....",
" dakata bana son shashanci tun yaushe rabon da naje naga 'yan kwana tafiya yazama dole",
" amma dady kasan inada meeting gobe kuma is important ga company dinmu taya zanbar aiki",
Yarfe hannu dadyn yayi " wannan baidaman ba tunda a business akwai lost dan anrasa wani bazai hana naki ga yan uwana ba",
Ganin zasu cigaba da kallo da dadyn yasa shaheed yace " Allah yakaimu goben",
" Uhm dama kace haka mana tunda kaima so kake kaje can din lallai2",
Momy tafada cikin Jin haushi tashi tayi daga dinning din ta haura dakinta,
Wayar ta ta ciro tahau kiran furera ba'a dau lokaci ba furera ta amsa,
" lafiya kike kirana yanzu",
" ke inafa lafiya bayan gamu nan Alhaji yasamu a gaba ya dage sai munje kauye kinfi kowa sanin komai,
" mukaje kauye kashina ya bushe ya zamuyi ga boka yaki yayi komai kan lamarin ya kenan".

Ajiyar zuciya furera tayi " bamu da zafi na kitara komai kawae shine abunda kawae zamuyi",
" furera bazaki gane damuwa ta bane zuwana kauye dai2 yake da rasa aurena saboda abubuwan Dana aikata,
" ba shakka 'yan uwansa ba zasu yi shiru ba",
" amma Ni'ima kinsan dole bamu da zabi daya wuce kije din ko",
Haka dai sukaita zantukansu Wanda karshe haka nan ta hakura a zatan.
"amma SHAZMAH nasan tare za'abar mu dake dan ko shaheed naso hajiya bazata amince ba",
SHAZMAH dai shiru tayi bata cema mairo komai ba dan ita duk abunda akayi da ita a gidan dai2 ne,
" mairo!"
Ya kwala mata kira " kinji yana kira bari naje naji",
Tashi tayi ta amsa ta fita SHAZMAH kam tunanin ta nakan momy a yanzu dan sam bata yarda da itaba,
" mairo ki shirya kayan SHAZMAH tare da ita zamu tafi",
Shiru mairo tayi tana kallon kasa ganin bata ce komai ba yasa ya tambayeta" lafiya mairo",
" eh lafiya amma kana ganin hajiya"
" wannan ba damuwarki bace kishirya ta kawae"
Yana fada ya koma part dinshi ya barta cike da mamakinsa " Anya shaheed bason yarinyar nan yake ba",
Sai kuma takama bakinta da hannunta " Uhm ba'a bakina ba"
Komawa tayi ta sanar da SHAZMAH inda tafara hada mata kayanta SHAZMAH na zaune abunta bata ce mata komai ba.

Gyngyadi ne yafara fuzgar SHAZMAH dake zaune inda tadau filo ta tokare bayanta dashi,
Wani guri ne me shegen kyau sai furanni gun ya tsaru ya hadu gudu take a cikin dajin me kyau,
Tana dariya inda wani saurayi ke binta yana kokarin kamata Tana subucewa kamar daga sama,
Taga ja ya bayyana sararin samaniya ga wani uban Kara me tsawa da take ji tuni gun yafara sauyawa,
Juyawa tayi taga wannan saurayin dan bataga fuskarshi ba Tana juyawa taga maalik kwance cikin jini,
" SHAZMAH kitaimakeni",
Abunda yake fada yana maimaitawa kenan da gudu ta karasa gabanshi,
Damko hannunta yayi tuni yanayin sa ya sauya zuwa abun tausayi,
Ihu tayi tana kokarin tashi amma Sam takasa " kina shiga aikinmu karfinki yafara raguwa hahahahahahaha",
Abunda abun ke fada kenan.

Sai juye2 take tana zufa mairo tashi tayi tana girgiza ta amma Ina ga jikin nata yayi zafi rau kamar wuta,
Fita mairo tayi ta kira shaheed danya duba SHAZMAH,
" meya faru kuke sauri"
" SHAZMAH ba lafiya" tabe baki momy tayi,
" ke mairo yi maza kizo kimun wani aiki dan ba aikinta nakawo kiba",
Alamu shaheed ya nata da taje din ya shiga dakin da SHAZMAH ke kwance banda jijjiga ba abunda gadon yake yi karasawa yayi da sauri,
Tana zufa tana motsa baki irin wahalan nan,
Can kuma abun Sam takasa kwatar kanta " nan zamu kulleki ba ruwa muga yadda abun ki zaiyi aiki",
Shaheed kai hannu yayi ya rike hannun SHAZMAH take abun yayi ihu ya bace mata,
Hakan yayi dai2 da bude idannunta wani irin ja sukayi wani haske daya sauka kan gefen gadon sai da gun yayi alamun kuna,
Shaheed ma wani zafi yaji a hannunsa Wanda take ya saketa yayi gefe,
Tajima a zaune tana sauke numfashi kafin ta koma ta kwanta sai bacci me dadi yayi gaba da ita,
Shaheed rasa meyake faruwa yayi tashi yayi yakoma kusa da ita yakai hannu amma kamar me jin tsoro dan hannunsa har rawa yake dakyar ya yabata,
Saida yatabbatar komai normal ya fita amma abunda yagani ne ke tsorata shi " WACECE SHAZMAH"
Tambayar data zo mishi kenan sai dai baida amsar su Sam,
Amma yadau ma Kansa alkawarin sai ya gano abunda ke tare da ita me kuma ya faru.

Koda mairo ta dawo ta tarar dashi ce mata yayi kawae ya kona masu gu da wani chemical,
Dake da yar jaka yashiga dakin na kayan aikinshi haka ya mata sallama ya koma dakinshi,
Ranar bai iya bacin kirki ba gashi yana tsoron karta cutar mai da 'yan gidansu sai dai,
Bazai taba iya tarar ta da wannan lamarin ba,
Sai ya gano WACECE meya kawo ta dan yafara tantama kanta sosai.
" SHAZMAH! Ke SHAZMAH!! Tashi maza kiyi wanka kun kusa kama hanya oya",
Bude idannunta tayi taga tangararan gari ya waye sai a lokacin abunda yafaru daren jiya ya fado mata,
Tashi tayi da sauri " Ina yake" kallonta mairo tayi da mamaki wai wakike nema ko shaheed",
Daga mata kai tayi alamar eh " jeki yi wanka zaki ganshi",
Koda yayi wanka aka fito tafiya shaheed kau da kai yayita yi baison ganinta Sam,
Dafashi Saal yayi " what's up bro inafa lura da yadda kaketa kau da kai have you two....",
Kai mishi duka shaheed yayi dan yasan halin dan uwansa sarae yasan me yake nufi,
" baka da kunya ko Saal harni yanzu kakeson sawa a abun baka ko",
Dariya Saal yayi yawuce yana "oho zadai muji".

Da akazo shiga mota kiri2 shaheed yaki shiga motar da SHAZMAH zata hau ya like ma Dadynsu,
" Saal shiga mota muje mana" kallon cikin motar yayi yana kau da kai,
" seriously with her"
Murmushi mom dake front sit tayi " yes bakada zabi tunda me ita ma ya gudu",
Haka nan sukai ta mai dariya dole yashiga ya zauna can nesa da ita dake su biyu ne kawae a bayan,
Mamakin Saal SHAZMAH take saboda halayensa kaf ba irin na shaheed bane ga kyama kuma ance yan uwa,
Sun dau hanya sosai take kallon yadda suke tafiya sai dai anyi nisa tafara Jin jiri hakan yasa tadan jingina jikin kujerar Wanda daga nan bacci yayi a won gaba da ita,
Saal banda Jin wakokinsa dayasa earpiece ba abunda yake da motar tashiga hanya me gargada motar na gurgurasu sosai,
Da tayi wani tsallene sai SHAZMAH ta hantsilo jikinsa toshe hanci yayi yana kallonta,
Yana so ya tureta amma baison tabata Jin dumin jinkinsa yasa ta Kara gyara kwanciyarta jikinsa batare da ta saniba,
Fuskarta dake dan rufe ta bude tsura ma fuskarta kallo yayi dan kusan tunda tazo bai taba tsayawa ya kalleta ba,
Kasa dauke idonsa yayi kanta gefen sajenta ga wani irin kwantaccen gashi tamatukar sace shi,
Batare da tasani ba baisan sanda ya cire hannunsa daga hancinsa yadan gyara kafarsa yadda takara sakewa a jikin nasa,
Anyi tafiya mai nisa kafin momy ta farka inda ta hangosu ta mirror ta juyo " kake yadda wannan mayyar na hawa ma kafa",
Da zafin nama ya turata can gefe hakan yayi sanadiyar farkawarta bata bi takansa saima rufe duka fuskarta datayi tacigaba da bacci,
Haka nan ya tsinci zuciyarsa da wani irin bugu da baitaba tsintar kanshi ba wakar da yake ji tuni yadaina jindadinsu sai kallota dayake ta satar yi amma still fuskar ta.



Yau ayi hakuri da wannan page din walh nagaji yau sosai dakyar na typing dinshi👏

WACECE SHAZMAHWhere stories live. Discover now