Chapter 13

995 64 2
                                    



Wani abune yafita jikin shaheed tuni idanunsa ke kan SHAZMAH wadda tuni takoma,
Suffanta na ainahi zaro ido yayi cike da tsoron abunda idanunsa ke gani tuni jikinsa ya saki,
Yakasa koda numfashi ganin yadda yakoma cikin ruwa gaba daya yakara tada ma SHAZMAH hankali,
Komawa tayi ta dagoshi tana jijjigashi sai dai shaheed koda baya iya komai idonshi nakanta,
Ganin yakasa numfashi ga ruwan nakara wani irin juyi dasu yasa SHAZMAH,
Sa lips dinta cikin nasa tare da kamoshi gaba daya Tana kokari cetonshi kamar daga sama taga komai na komawa normal,
Hatta jikinta hakan yabata karfin fito da shaheed Wanda a yanzu kam gaba daya ya sume mata,
" SHAZMAH meyasa",
Muryar Wanda taji bayanta yasa tai saurin waigawa,
Maalik ne tsaye rasa mezatai tayi dan farin cikin ganinsa,
" kinsan me zai faru da bana wannan wajen"
Yafada cikin fada Wanda hakan ya tabbatar mata da fushi yake da ita " ya maalik ya zanyi shah....",
Dakatar da ita yayi " kina nufin wannan bil'adaman yafiki ne da har kike kokarin salwantar da kanki saboda shi kike kokarin bata mana Komai da muka shirya,
" kinmanta dalilin zuwan ki wannan guri gaba daya kina kokarin wargaza mana masarauta saboda wannan bil'adaman",
" banma taba amma bazan iya kallon shi ya mutu ba".

" SHAZMAH me hadinki dasu karki manta abunda yakawo ki baki zo danki cecesu ba,
" kodan kikashe kanki kinajina ko" ganin da gaske ranshi bace yake yasa tafara bashi hakuri,
" ya maalik Ina umma" sai a lokacin ya mata murmushi " tana gaishe ki amma nasan da tasan abunda kikayi yau da lallai ranta zai baci",
Murmushi itama tayi tare da tashi ganin shaheed na kokarin bude ido ta kalla maalik,
Gaban shaheed yazo yasa hannunshi Kansa wani haske ne ke fitowa daga hannun,
Tuni maalik yafara ganin abubuwan dake tattare da shaheed tashi yayi da sauri,
" lafiyarsa kalau"
" eh lafiya yaganki amma na goge bazai tuna komai game da abubuwan dake tattare dake ba,
" bacin sanin ki kan shiya tsinto ki amma komai yagogu karki damu",
Kallonsa take saboda yanayin dataga yadan shiga " lafiya ya maalik",
Murmushi yayi " lafiya SHAZMAH karki damu yanzu ta yaki zanyi mukai shi gidansu ko,
" amma SHAZMAH kibar gidansu kibini zamu nema inda zamu zauna kinji ko",
Girgiza kai SHAZMAH tayi dan tariga tasaba dasu batajin zata iya barin su nan dai yayi iya kokarin sa amma taki haka nan ya hakura,
Amma da sharadin duk inda take yana tare da ita dan bazai iya barinta ita kadai ba.

MASARAUTAR MAISUM

" SHAZMAH!!!"
Tafada da karfi Wanda hakan yasa fadan yin wani irin girgiza,
Duk Wanda ke cikin fadan hankalinsa a tashe yake hatta matsafan dake suna aikinsu,
" Ranki ya dade naganta yanzu inakokarin gano inda take kuma sai komai ya rufe",
Daya daga cikin matasafan yayi magana " tabbas nima hakan ne yakasance",
Wani ma Yafada inda muryoyin matsafan ya gauraye fadan gaba daya inda kowa ke cewa yaganta,
" tabbas anyi amfani da tsafi me karfin gaske wajen boye inda take",
Wani irin huci safwana tafara Tana gurnani hakan yasa duk bokayen suka kame bakunansu,
" mama inaganin farin ciki yakamata kiyi"
Sahima tafada sanda take shigowa cikin fadan cike da mamaki kowa ke binta da kallo,
" sahima meya kawo ki fada yanzu ba lokacin wasa bane"
" Niko nasan ba lokacin wasa bane dan kina nan fada zaune yanzu haka maalik ma ba'a ganshiba",
Nan fada ya dauka da surutai kowa na fadin albarkacin bakinsa,
" anjima da sanin dalilinki mama keda SHAZMAH zan iya rasa maalik gashi kuwa ya tabbata",
Fashewa tayi da kuka me ciwo yayinda safwana ke kallon yartata cike da tausayawa,
" yazama dole ki nemo mun maalik duk inda yake koki rasani" da gudu sahima tabar fada.
Tashi safwana tayi cikin tsawa tafara magana " yazama dole a samo mun su dan abunda yafaru kaina bazan taba bari yasama 'Yata ba".

Bogur ne tsaye gefen sarauniya safwana yana tunanin tattauna warsu da mahira,
Baya da boka yayi aiki kan zuwan maalik inda take saboda matsala da aka samu na rashin jinta kwanaki,
Kallon safwana yayi wacce keta hawa tana sauka " mezai hana asa mahira dakin horo kila tafito dasu duka koya kike gani",
Murmushi gimbiya safwana tayi " mekuke saurare kuyi duk yadda bogur yace",
Tana fada tabar fada din magoya bayanta suka bita yayinda fada yafara watsewa,
Dariya bogur yayi  ya kallah Omid " maza kaje kai kawo mahira fada yanzun nan",
Omid kallon bogur yake cike da mamakinsa,
" meka tsaya kallo maza kaje kayi abunda nasaka",
" amma meya...." bogur wucewa yayi haka nan su Omid suka dan zuwa kawo mahira.

WACECE SHAZMAHWhere stories live. Discover now