Chapter 2

1.6K 110 9
                                    


Tunda shaheed ya taimaka suka dawo da ita dakin mairo take kalle2,
" oya jeki hada mata ruwan wanka"
"Toh",
Mairo tace tana kallon ikon Allah tashige toilet din tabarsu nan,
" kina Jin Hausa"
Kallonsa take kawae tana kallon kafafunsa kai hannunta tayi tana taba kafarsa data gani cikin safa,
Tana kallon kafarta Tana kallon nasa mamakine ya cika SHAZMAH yadda leg dinsa yayi baki ga yatsu nasa kuma baki,
Kara kai hannunta tayi wannan karon kokarin cire mai safa take,
"Uhm! Uhm! Uhmm!!!" Dakarfinta ganin takasa cirewa yasa ta fashe mai da kuka,
Mamakine ya cikasa agun ya rage tsayinsa zuwa inda zai iya ganinta " do you speak English",
Yakara dankara mata tambaya nan ma still shiru ganin ma ya rage tsawo tana iya ganinsa yasa tajanye daga gunsa,
Mamakin gashin kanta yake yadda suka dawo suka rufe mata face gaba daya haka kawae yaji yana son ganin eyes dinta,
Hannunsa yakai a hankali ya Tana "uhm uhm" tana dan ja da baya ya buda ta tamke su sosai,
Murmushi yayi me sauti Jin sautin murmushinsa yasa SHAZMAH bude idanunta da sukai dau kamar na cat ga wani haske da suke da sauri ya razana ya sake gashin yatashi,
Time din mairo tafito " naka tafi ba" murmushi yayi " gudnight" Yafada yayi gaba tare da ja masu kofa.

" uhm ni dai kawae anbarni da aiki ko daga Ina ya dibo wannan mahaukaciyar oho,
" dallah Malama taso muje kiyi wanka haka kawae mutum na baccinsa an wani tashe sa saboda mugunta mtsw",
Ganin SHAZMAH Sam bata da niyyar motsi ko alamun tajita yasa ta tashi taje ta fincike ta "ahhhhhh" SHAZMAH tayi ihu,
" karki kuskura kimun ihu taso muje kawae"
Takara fisgota cike da jin zafi da bacin rae SHAZMAH ta dago hannunta wani blue din haske ne ya shiga mairo,
"Woo...",
Mairo tayi cak ta tsaya agun bata iya motsi ko magana sai idanunta da take juya su tana kallon SHAZMAH,
Da alama Tana so ta roketa tana Jin jiki da tsayuwar nan SHAZMAH ta bude gashin idannunta nan wani abu kamar wuta yafito saitin bangon,
Take wani halitta ya bayyana shiba mermaid ba shi kuma ba kifi ba sam,
Dariya abun ya mata SHAZMAH sosai taji takara fusata " gimbiyata karki taorata wadanda kikaje dan kiyi rayuwa dasu kisama farin ciki",
A fusace take kallon halittar "bogur ban kiraka dan wannan ba amma haryanzu bana iya yima bil'adama magana,
" duk sanda zanyi magana sai naji Ina ihu meya sa kuma kafafuna irin nasu yaki yayi amfani meyasa".

Dariya bogur yayi tabe baki tayi " bogur nazama abun dariya ko",
Hadiye dariyar tasa yayi " yanzu zan miki yadda Zaki iya magana sannan ki kuma iya tafiya irin nasu",
Take ya ya rufe idannunsa yana budewa akanta sai wani haske ya lullubeta har baka iya ganinta,
Cikin lokaci Kalilan sai gata tsaye a kan kafarta,
" murmushi tayi nagode bogur inda wani abu zan nemeka"
"Tsaya"
Ya dakatar da ita daga datse tattaunawar su,
" wannan ki sake ta kirike hannunta ki goge komai data gani tattare dake dan su bil'adama Zaki iya gogewa",
Godiya tayi ta koma ta zauna tana sakinta mairo na kokarin gudu ta damki hannunta nan ta goge komai,
Inda mairo ta cigaba da mata ihu taja ta zuwa gun wanka ganin ruwan sosai SHAZMAH taji tsoro saboda kar tail dinta ya bayyana,
Dakyar ta yarda mairo ta shiga da ita harta taba ruwa sai dai ba abunda ya faru sosai taji dadi,
Nan mairo ta wanke mata kai amma ganin bata San meye wanka bama bakaramun mamaki abun yaba mairo ba ganin yadda ta wurgar da zanin a gabanta ta tsaya mata tairara,
Nan dai mairo ta nununa mata amma still har lokacin SHAZMAH bata mata magana ba harta shiryata suka kwanta.

" mairo Ina bakuwa ta kikawo ta kan nayi breakfast na fita naganta",
Murmushi mairo tayi " owk bari na kawota",
Tsaye yake yana kurban coffee dinshi na sabo a balcony dinsa sanda ya hango yarinyar na kalle2,
Tsayawa yayi yana kallon yarinyar dan bayajin ya santa wa take nema and why is she dressing that way,
Sai dai bashi da amsa kamar zai sauka ya tambaya wa take nema sai ya hango mairo,
Inda baijin me take fada tajata zuwa dakinta inda mamaki ya Kara rufe shi,
"My bro baban coffee"
Murmushi yayi me sauti tare da maida daya hannunsa cikin pocket din wandonsa,
" and what do you want this early morning"
" my darling Saal bro"
Tafada tare da rungumo hannunsa " no sakeni karki zubarmun da coffee dina just answer the question hadil I know for sure you need something",
Dariya tayi " ok ok o yes of course I want something nasan kuma zaka bani because you are my cute brother"
Murmushi yayi " so tell me now I am tired of this long easy"
" olright sorry some cash"
Wucewa yayi zuwa dakinsa inda take biye dashi a baya bandir din 1k biyu ya mika mata tasa hannu ta amsa "thank yhu muaah".

Tafada tare da yima kudin kiss tafice da gudu girgiza Kansa yayi ya shiga shiri abunsa,
Yana kamalla wa ya sauka zuwa dinning inda already kowa ya hallara harda dad dinsu,
" wae Ina mairo ne",
" gani hajiya"
Mairo tashigo rike da SHAZMAH da wannan karon ke cikin riga da skirt sai dai taki sa dankwali Sam taki yadda a taje mata kai Sam,
A baje suke har fuskarta dan ba'a iya ganin idannunta sam,
" and who is this"
Hadil ta tambayeta tare da nunota,
" my guess"
Shaheed ya amsa tare da yima mairo nuni data kawo mai ita dinning tayi break,
" doctor don't tell me treatment din naka yanzu har gida kakeyinshi"
Dadynsu Alhaji Ahmad M Abdulkadir ya tambaya cike da zolayar dan nasa,
" uhm banga abun wasaba gaskiya amma Sam bazan ci abinci da wannan a dining ba haka kawae ka tsinto yar bamu San ma ko ba mutum bace ma kawo kace ta zo inda muje haba",
Dariya Alhaji Ahmad zancen matar tasa yabasa sosai,
" wait wait Niima don't tell me dama kina da tsoro niban sani ba" Yafada yana dariya sosai tsakaninsa da Allah.

" dad is not fair gaskiya how can we dine with someone like her wacce bamu ma San inda tafito ba,
" and I think bro should take her to the hospital taya mu zai kawaso mana ita nan",
Sosai shaheed ranshi ya baci tashi yayi daga dinning din suna kallonsa sun zata ma fita zaiyi,
" mairo kikawo breakfast dina da nata falona yanzu ke kuma muje",
SHAZMAH batai mai gardama ba tabi bayansa da tafiyar ta kamar na tata dan kafar still ba kwari,
Zuwa sukai suka zauna a falon nasa " Ina kwana",
Juyawa yayi yana mamakin ta inda yaji maganar ganin daga shi sai ita ya tabbatar mai da cewan itance,
Mamakine sosai a fuskarshi wani irin dadi muryar tamai tunda yake baitaba Jin muryar data mai dadi irin wannan ba,
Mamaki ne ya rufe SHAZMAH dan mairo tace idan tace Ina kwana za'a ce mata lafiya ma'ana anji dadin gaisuwar ta amma saita ga akasin hakan,
Tunani tafara yadda yake mutumin kirki yake mata komai amma bai amsa gaisuwar ta ba saita fara tunanin ko baiji bane,
" inakwana"
" lafiya!"
Da sauri ya amsa a dan tsorace abun nabata mamaki matuka yadda ya amsa matan.



              Saimun hadu next page kar amanta a dunga comments....👌

WACECE SHAZMAHWhere stories live. Discover now