Chapter 5

762 42 2
                                    

MASARAUTAR MAISUM

Zaune suke su duka da alama akwai babban abunda yake damunsu sosai Wanda,
Kecin kowannensu a zuciya kallon juna sukai sai suka Kara shiru,
A tare kuma suka dago har suna hada baki,
" Katuna shekaru......." shiru sukai suna kallon juna,
" bogur kai kafara da alama abu daya muke son fada",
Girgiza kai yayi cike da damuwa " shin SAFWANA ko kin tuna abubuwan da suka faru shekaru talatin",
" abunda yake damuna kenan bogur bama wannan ba ko kasan Yau ne wannan ranar,
" da akacika shekara talatin dai2",
" ya za'ayi namanta bayan nasan me hakan ke nufi Yau ne ranar da zai sama duka tsafinshi,
" Wanda girman abunda zai samu yafi namu duka",
Shiru SAFWANA tayi cike da tsoro da kuma tambayoyi,
" Amma meyasa zaifi kowa a cikin wannan masarauta"
Ta tambaya Tana kallonshi,
" saboda shidin ruwa biyu ne ya hada jinsi biyu",
" amma bogur kana ganin boka bazai iya taimakon my kan wannan lamarin ba kuwa",
Girgiza kai bogur yayi " sai dai muje mu gwada amma abune da kowa yasan ranar na zuwa",
Nan dai sukai shiri dan wannan karon SAFWANA da kanta zata inda boka yake saboda tsoron abunda zai faru a wannan ranar a cikin MASARAUTA.

" yake wannan SARAUNIYA nayi dukkan iya bincikena tun kafin kuzo gareni sai dai,
" Sam babu abunda zan iya akai hasalima bansan inda yaron yake ba sai dai,
" Ina da tabbacin a daren jiya rubuttacen lamarin yafaru dan ya kusanci mace kuma wacce baya so Wanda,
" Wanda kowa yasan muddin ba wacce yake so bane akwai matsala kawae ku koma mijira abunda zai faru bazamu rasa kofa ba amma a yanzu a rufe suke",
Sosai SAFWANA tasama disapointment suna fitowa ta shiga yiwa bogur mita,
" wannan duk laifin kane kaida SARINA daka kula da ita yadda ya kamata,
" ka dakatar da ita daga wannan soyayyar tun wuri da wannan bil'adaman da hakan bai faru ba",
Kallonta yayi cike da takaici ya girgiza kai,
" SAFWANA kinfi kowa sanin nayi iya kokarina kan SARINA kuma duba zakiyi da a lokacin yarinta ce ke damun mu sosai,
" Wanda ya kaini ga son duk abunda SARINA keso harna barta tafita daga duniyar nan amma bantaba sanin SARINA zata kamu da son bil'adama ba sam",
Ture shi tayi ta wuce abunta " kundai jawo mana matsala Tana da ranta SARINA matsala ta mutum ma bamu huta ba",
Tsaki tayi cike da takaici tabarshi agun inda mabiyanta suka rufa mata.

Bogur kuwa wucewa yayi inda yake tsare da SARINA,
Yau shiga gun yayi shiru kamar ba shiba yaje ya nema guri ya zauna dan nesa da ita,
Tana kallonshi tayi shiru ganin yana yinshi sunjima a haka kafin yafara magana,
" Kin tuna Yau yaushene a shekarun da suka wuce",
Daga kai tayi " taya zanmanta ranar da aka rabani da abunda nake so da karfi da yaji",
Murmushi bogur yayi yana kallonta " SARINA!",
Yakira sunan ta da sanyin muryar da ya jima baikirata ba dagowa tayi ta Kara kallonsa,
" kintuna sanda muke yara"
Murmushi tayi " tabbas na tuna mun kasance cikin farin ciki da kaunar juna",
Sai kuma tayi shiru shima shirun yayi suna tuna abubuwan da suka faru a rayuwarsu.

" SARINA! SARINA!! SARINA!!!"
Muryar yar budurwar ne ya karade cikin kogunan,
"Oh h!" Tafada sanda ta tsaya tare da kama dan kugunta,
" Oh SAFWANA nasha fada miki kidinga sauri amma saikiyi ta bina da kira har gashi kinsa bogur ya bace mun kinsan dama ya fini iya iyo",
Kada ido SAFWANA tayi " to meyasa inzakuyi tseren naku kuke nemo ni tunda kunsan basona kuke agun ba iye SARINA",
Rungumota SARINA tayi " yi hakuri yar uwata nadaina miki fada taho muje mu kamo shi",
Murmushi SAFWANA tayi tabi bayan SARINA,
'Yan matane kyawawan da basu wuce 15yrs to 16yrs ba,
" SARINA nagaji haryanzu banga alamun bogur bafa",
" muje nasan yana nan kusa",
" to"
Tafada tana tabe baki da alama tagajin ita kam,
Jin hayaniyar samari sukai dan sunyi sama sosai da alama suna wasa aguraren ruwan ne,
Dai dai wani dutse sukaje suka buya inda suke dan fidda kansu suna hango samarin,
" woooooh!"
Duk sun tsorata da jin muryar Kankame juna sukai suna shirin yin ihu sanda bogur ya bullo.

" kinfiya tsoro SARINA"
Yafada yana kwashe wa da dariya ciki suka dan koma,
Inda ya daura mata wani abun kai da ya hada da flowers yayi matukar yin kyau,
Sosai SAFWANA taji badadi yadda suke wasa suke yamutsa juna,
Har basu San duhu yafara ba ihun wani saurayi sukaji yana a taimakeshi,
Yayinda can sukaji anwulloshi cikin ruwan,
Da sauri SARINA tafara kokarin zuwa taimakon yaron inda bogur ya rike hannunta,
Fisgewa tayi iyo ta isa ga dan matashin ta rikoshi gaba daya ganin duku yasa tayi tsafi,
Jikinta gaba daya kamar fitila haka yadawo bama kamar tail dinta,
Saurayin ta gani idonsa bude yana wuntsil2 inda ta tuna abunda kakarta ta tafa fada mata,
Kan yadda ake ceton bil'adama saurayin sosai yayi mata kyau kyakyawa ne sosai ya tafi da zuciyarta,
Bogur da suke nesa mamakin yadda take kallon saurayin suke sanda takai bakinta zuwa nashi,
Nan kishi ya daki bogur zaije SAFWANA ta riko shi suna kallo tayi sama dashi,
Bakin ruwan ta fidda shi " tashi baka ruwa yanzu",
Tana yi tana jijjiga shi ganin zai farfado yasa tayi sauri tabar kusa dashi,
Ina tuni ya riga ya hango ta sanda take komawa ruwa inda yasake rufe idannunshi,
Tana ji yan uwansa suka iso suka dauke shi.

" SARINA meyasa kika shiga cikin sabgar bil'adama",
Shiru tayi bata ce masu komai ba sai murmushi da tayi tuna fuskar saurayin sosai takejin dadi,
Tafiya tayi dan komawa gida suka ganin haka yasa sukabita,
Ba Wanda yayi ma kowa magana cikin su har suka isa gida sai sallama da sukai ma juna,
" SARINA Yau inakuka shiga nayi ta tura wa a nemoku daga ke har abokan wadan naki ba ko daya",
Murmushi tayi ta nema guri ta zauna Tana Kara cigaba da murmushi,
" lafiya kike ta murmushi ke ka daya kamar tababbiya",
"Lafiya kaka Yau na taimaki bil'adama" cike da tsoro kakarta ke kallonta,
" kaka ai na kyau ta ko",
" a ina kika ga bil'adama kar dai kice mun har duniyarsu kuke zuwa wasa",
Tabe baki tayi ta bata fuska sanin fada kaka zatai mata,
Nan taba ta labari inda kakarta taja mata kunne karta bari kakanta yaji wato sarkin wannan lokacin,
Tun daga wannan rana SARINA ke fita duniyar bil'adama saman ruwa da tunanin zata ga wannan saurayin,
Wanda shima hakan ne ya kasance gunsa,
Sai dai saba ni da suke na lokaci. (Zamu cigaba).

CIGABAN LABARI SHAZMAH

SHAZMAH ce kwance Tana mafarki sai juyi take tana wasu abubuwa da alama mafarkin nata dakwai ban tsoro,
(Mimsqueen nabita ciki)
Shaheed ne idanunsa sunyi Jazur kamar na garwashi,
Sifofinshi gaba daya sun juya zuwa irin nasu SHAZMAH,
Wato sama mutum kasa kifi daga hannayensa yayi duka biyu inda MASARAUTAR MAISUM ba abunda take sai jijjiga,
Yayinda ruwa ke ambaliya ruwanke wani irin jujjuyawa,
Ga wani irin tsawa da ake sosai abubuwa ke destroying sama ruwan banda guguwa da iska babu abunda ke faruwa,
" shaheed! shaheed!! shaheed!!! Ka dakata dan Allah",
Tafada da karfi Tana kokarin nufarsa iska na dagata suna nesan tata dashi gun gaba daya banda Kara ba abunda kakeji,
Ga wani ruwan sama da ake kamar da bakin kwarya,
" Saheed!!!",
SHAZMAH tafada da karfi Wanda batasan har a zahiri tayi wannan kiran ba,
Wanda hakan yayi sanadiyyar tashin innawuro da mutanen gidan hakan yasa kowa yayo dakin,
Still bata farka ba ita har innawuro ta bude ma su dady dasu Saal kofa harma da shaheed din,
" innawuro tashe ta koki yita tofa mata addu'oi"
Dady yafada ganin hakan yasa ZAYNA taje gefen SHAZMAH ta zauna ita burinta bai wuce tasan meke damunta ba tasan ba lallai su su saniba yan gidan.

Sa hannu ZAYNA tayi tadan riko hannunta,
Tuni ta hasko fuskar shaheed da sauri ta janye hannunta cike da tsoro,
Sai dai tayi kokari ta danne abunda ta gani din,
Dady kuwa fita yayi da sauri ya koma dakinsa dauko wayarsa yayi yafara dialing,
Baa dau lokaci ba kuwa aka picking " Ba lafiya",
Abunda Dady Yafada kenan yayi shiru yana sauraran daya bangaren,
" lokaci yayi yau ne inatsoron abunda zai kasance Baba kasan komai kan shaheed ba saina boye maka ba",
Shiru yayi yana Kara saurara " eh bata San wannan maganar ba tadai San ba danta bane tabbas",
Shiru ya kuma yi yana jiran abunda za'a fada mishi,
" to da sassafe zan dauko shi mutaho nan kauye inda abun yafara a karasa agun",
Nan dai sukai Sallah amma kana ganin Dady zaka fahimci yana cikin damuwa sosai.
SHAZMAH kuwa Dady na fita tashi Tana binsu da kallon especially shaheed din,
Dan kamar tsoron shi ma take ji gaba daya wannan karon.



End of part1

Identity din shaheed na gab da bayya nuwa garemu waye shaheed❓ that's my question and everyone question too👌

WACECE SHAZMAHNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ