Chapter 3

665 46 2
                                    



SHAZMAH koda ta rufe ido nan ta gano harda ambaliya da wani katon kogi ke yi,
Tana kokarin tsaida shi kuma taji ruwan ya tsaya lokaci daya dan yayyafi da ake,
" Masha Allah walh harna tsorata da wannan ruwan",
Innawuro tafada " walh nima" hadil tabata amsa,
Dan suma tsaye suke da khairy suna kallon ikon Allah.
Tashi ZAYNA ta maida kayan ta Tana kallon MAALIK Tana dariya,
Tashi yayi yana rike Kansa da alama kan naciwo tuna abubuwan da suka faru yasa ya dago da sauri yana kallon ZAYNA,
" mekikai mun" ya tambayeta a fusace murmushi tayi tana kallonsa,
" magana nake miki"
" hahahaha nayi controlling dinka ne na wasu dakiku MAALIK najima inason kasancewa dakai,
" amma Sam bana gabanka kaki sahima ma sai SHAZMAH wacce bata da raayinka",
Cikin bacin rae ya daga hannu ya wanke ta da mari,
Sa hannu tayi ta sosa gurin Tana murmushi " MAALIK kome zaka mun bazai daman ba tunda na sameka a farko Baka taba sanin mace ba nice farko,
" Amma karka damu dan daga yanzu nice zan zame maka dole dan sai abunda nace zakai daga Yau",
Kallonta yayi Jin abunda tace tabbas tafi karfinsa akan magic yariga yasan zata iya komai,
" please ZAYNA karki yi mun haka zanyi duk abunda kikeso amma karki yi using komai akaina".

Ganin taci galaba Kansa yasa tafara murmushi " good boy suke cewa ko zan barka but,
" inkayi kokarin making dina fool zaka sameni yadda bakai tunani ba kasan ko SHAZMAH bata da karfin ja dani"
Tana fadin haka tasa Dariya ta bace agun gaba daya tabarshi yana mai Jin haushin Kansa sosai,
Kuka yashiga yi irin me zafin nan nacikin rae Wanda bai fitowa fili " shikenan ta cuceni ta maidani bawanta lokaci daya,
" but ZAYNA zan nemo hanyar fita daga sharrinki dan bazaki taba nasara kanmu nida SHAZMAH ba".

Haka SHAZMAH ta yini cike da damuwa kan abunda yake faruwa Wanda bata saniba,
Ga kuma matsalar aunty hanne da dady sosai abubuwan ke Kara tabarbarewa,
Dan Yau dady ma daya ganta a dining kin cin abinci yayi yace ma momy su tafi dakinta can suci,
Tana zaune MAALIK ya bayyana mata " SHAZMAH lafiya"
Da sauri ta tashi ta nufeshi kamar zata rungume shi sai kuma ta dan ha tayi baya,
" MAALIK Ina kashiga Yau meya faru na tabbatar akwai abunda yafaru dakai",
Shiru yayi yana kallonta rasa amsar da zai bata yayi hakan ya hadiyi wani mugun bacin rae a makogoronshi me daci,
" kwantar da hankalinki kan wata ba abunda ya faru serious kawae dae banjin dadine amma yanzu da sauki tunda gani",
Kallonsa tayi kamar bazata yarda ba saikuma tayi murmushi,
" to Masha Allah tunda kana lafiya muje ciki kaci abinci",
Ta juya riko hannunta yayi ya dawo da ita " aa zan koma ne saboda akwai aiki gabana sosai",
Badan taso ba ta rabu dashi sai dan taji dadin ganin shi lafiya kalau.

Ciki ta wuce shima kuma bacewa yayi abunsa,
" khairy ga wannan abun Shan kisan duk yadda zakiyi kiba SHAZMAH wannan kafin,
" dare saboda plans dinmu kinji ko" murmushi tayi tace " nasan wa zan ba tabata",
Karba tayi ta fita ta nufi falo kwance innawuro take tana karanta book dinta " innawuro",
" Na'am" ta amsa mata tana kallonta zama tayi gefenta,
" wannan nakeso kiba SHAZMAH ya shaheed ne yabani nabata kinsan in nice ba amsa zatai ba,
" yace kamar yaga batajin dadi ne yasan batason magani shiyasa yasa mata a ciki",
" aikuwa kwana kin nan narasa gane kan SHAZMAH Sam to bakomai zan bata nagode",
" bakomai"
Tashi tayi tabar innawuro gun SHAZMAH tazo wucewa innawuro takira ta,
" Ga wannan shaheed yace a baki Kisha" Jin sunan shaheed yasa SHAZMAH bata kawo komai a ranta ba takarba tasha.

"Nashanye to"
" yayi kyau" innawuro tace mata nan ta zauna sukaita hirar makaranta dan sunyi Hutu sai missing suke,
ZAYNA dake labe Tana hango abunda ke faruwa dadine ya fufeta hartana dan tsalle,
" ZAYNA kingani nabata Tasha muje toh",
Komawa sukai daki suka zauna kan gado suna dariya na cikar burinsu na farko,
" Amma ZAYNA meyasa muka ba SHAZMAH Tasha abu yanzu",
" kibar wannan zancen inada dalilinsa da bazaki sani yanzu ba",
Tabe baki khairy tayi yamutsa fuska kallonta ZAYNA tayi ta kyakyale da Dariya,
" kedae ba zamu yi aikin ki anjima ba ae bakida matsala kamar anyi angama ne",
Tunawa da khairy tayi na kasancewarta da abun sonta yasa ta murmushi,
" that's more like you"
Nan suma suka cigaba da plans dinsu suka sa ido suka tsare dan jiran dare tayi su aikata.

" Alisha yanzu ya ake ciki ne batun revenge dinki naga gaba daya kinshare tunda,
" Saal ya koreni a aiki me shirun ke nufi ko kin fasa ne",
Girgiza kai Alisha tayi " ko kadan nadai bari ne sai lokaci yayi Zaki San mena tanada kanshi",
" walh Alisha ko kinbar Saal ni bazan barshi ba saboda yaci mun mutunci sosai I can't forget",
" oh no karki damu dan very soon I will make him pay for what he has done Insha Allahu,
" just kibarni dashi kawae kibarshi yanzu yagama da new found love dinshi lokacinmu na nan tafe",
" yes Alisha that is more like you" tamata peck,
" bakida matsala"
" but Alisha me kince Zaki fada mun abunda Saal ya miki kuma naji shiru haryanzu time baiyi bane",
Murmushi Alisha tayi " karki damu Zaki sani at the right time basai kin rokan ba zan fada miki",
Badan sofie taso ba ta rabu da ita gudun samun matsala.

" shaheed problem dinka aurene kake bukata amma Sam kaki yarda nayi iya yina Sam,
" kadai duba Baka rasa kyau ba ko wani abu infact kadu ba kaga yadda yarinyar nan Amina ke sonka",
Zaro ido shaheed yayi yatashi zaune " come again wace Amina kake magana akai ne",
Murmushi " haba mana karka fadamun duk yadda lake da yarinyar nan ba kasan Dinka take ba",
Girgiza kai shaheed " aikuwa ta makara dan ba wacce nakeso sai SHAZMAH na riga nafada tarkon sonta bazan iya dai nawa ba",
" uhmm kai kasani kayita fama kuwa da ciwon ciki"
Bata rae shaheed yayi " malam fita mun a office tunda abun naka yazama iskanci",
Da gudu doctor yafita yana ma shaheed Dariya,
Shiru shaheed yayi yana tunanin yadda zai billoma lamarin shi Sam baya Jin zai iya kusantar wata 'ya mace ba SHAZMAH a rayuwarsa,
Knocking din kofar shi akayi " yes come in",
Abunda Yafada kenan ta turo kofar tashigo " Doctor we have patients that need you",
Kallonta yayi Sam Amina bata mai ba face mutuntata da yake baya Jin zai iya yaudararta,
" sir!" Tafada da yar muryarta " kije I will be there soon but which ward",
" Famele ward",
" alright Ina zuwa" juyawa tayi yayinda shikuma yadau farar rigar shi yasa da glass dinshi dasu stethoscope dinshi ya rataya a wuyanshi yafita.

Yau Sam dady da mom basu fito dinner ba kai masu akayi dan dady cewa yayi bazai iya zama inda hanne take ba sam gwara akai mai part dinshi,
Aunty hanne mamakin sauyin dady take na lokaci guda tasan basu sama matsala da mijinta ba sam,
Haka dae kowa ya zauna yaci abincin badan kowa nason,
Yadda abun yazamto bane hadil kam da khairy dadi suke ji dan har jikinsu rawa yake,
Bayan anci abinci andan zauna falo sunyi hira kusan 11pm kowa yatafi makwancinsa,
Shaheed ne kwance sai juyi yake yarasa inda zai sa kansa saboda matsalolinsa dake damunsa,
Knocking yaji a kofar yaje ya bude kafin ma yagama bude kofar tuni sun sa kai,
Matsowa kusa dashi ZAYNA tayi tace " kasa key",
Haka nan ya tsinci kanshi da bin umarninta............

Sai mun hadu a next page dan ganin yadda zata kaya masu wazai yi wining🤔

WACECE SHAZMAHWhere stories live. Discover now