Chapter 2

755 40 1
                                    



" shaheed!"
Takira sunansa a sanyaye tsaki yaja yayi hanyar kofar shiga dakinsa da sauri,
Tasha gabansa dai2 kofar " why are you blocking my way" Yafada cikin dakakkiyar murya,
" shaheed meyasa kake wulakanta ni dan kaga inasonka ne ko",
" malama ki tashi mun a hanya na wuce banson problem",
Kokarin rungumoshi tayi ta handata gefe tayi kasa,
Batare da ya lura da faduwan da tayi ba yasa kai a dakinsa abunsa,
" khairy dama nan kikayo why are you doing this bayan kinsan munada plans akanshi iye",
Sunkuyawa ZAYNA tayi tare da taimakon khairy ta tashi ta tsaya da kafafunta,
" ZAYNA Ina son shaheed fiye da komai a dadin duniyar nan indai zan sameshi zan iya komai",
Murmushi ZAYNA tayi " indai wannan ne Yau na mallaka miki shi kishirya a daren Yau Zaki kasance a kirjin shaheed is a promise",
Kara rungume ta khairy Tana mata godiya sosai dan tasan zata iya yima ta wannan.

" Aunty Ashe baki da lafiya" SHAZMAH ta tambaya,
Girgiza kai aunty hanne tayi " eh walh SHAZMAH tun shekaran jiya nake jinsa amma Yau yafi zafi",
" eyya Allah yabaki lafiya"
"Ameen innawuro"
Kowannensu naso ya mata magana kan abunda ke faruwa yana tsoro,
SHAZMAH ce tayi karfin Hali " aunty Yau me kika ma dady"
Tabe baki aunty hanne tayi " karku yadda kudama kanku tsakanin miji da mata Ana samun haka Insha Allahu komai zai warware",
Badan sun gamsu da amsoshin nata ba sukai shiru,

"SHAZMAH! SHAZMAH!! Kina inane" shiru sukai Jin alamun kiran,
" SHAZMAH kamar muryar hadil muke ji Tana kiranki ko",
" na'am!"
SHAZMAH ta amsa tare da fita " hadil gani nan"
Bata bata lokaci ba gun karasowa da murmushi sosai akan fuskarta tazo gun SHAZMAH din,
" muje inason miki tambaya ne kan MAALIK please SHAZMAH",
"To" kawai SHAZMAH tace mata tabi bayanta basu tsaya ko ina ba sai dakinta,
" SHAZMAH Yau banga MAALIK ba sam lafiya",
" eh walh ya MAALIK ankirashi agun aiki yana shaheed ma sallama lokacin baki fitoba",
" amma SHAZMAH please yaushe zai dawo",
Murmushi SHAZMAH tayi ganin da gaske hadil keson MAALIK din " walh bansaniba amma in munyi waya zance kintambaya",
Zaro ido hadil tayi " dama yana da waya ya hanani no dinsa please kiban" ba musu,
SHAZMAH taba hadil no dinshi dan tunda yazo yabata saboda su shaheed kan iya neman sa in baya nan,
Bata tayi har rungumarta hadil tayi dan murna sai fa man godiya take mata.

" amma SHAZMAH intambayeki mana shin bro dinki yana da budurwa ne",
Sosai SHAZMAH taji gabanta yafadi tunawa da yadda yake sonta saboda ita yaki kula kowa ce mace,
" kinyi shiru na cika tambaya ko I am very sorry for disturbing you",
" no walh ba haka bane is owk ae a iya sanina da bro bashi da budurwa baya iya kulasu,
" shiyasa haryanzu bai iya zancen da budurwa ba sam sai kallo",
Kallon hadil SHAZMAH tayi ta kyakyalce da dariya,
"Lafiya SHAZMAH ko banda kyan da zai soni ne",
" no hadil"
" then tell me please SHAZMAH inason sanin MAALIK sosai his likes and dislikes I want to know all",
" kwantar da hankalin ki zan fada miki komai kan MAALIK kawae Zaki sha wuya ne kanki koya mai sonki saboda baitaba ba",
Cike da murna hadil ke kallon SHAZMAH " kina nufin I will be his first wow SHAZMAH,
" thanks so very much my inlaw" tafada tare da yima SHAZMAH peck a kumatu " muyi magana anjima let me think" hadil tafada ta fita da murna Tana ma SHAZMAH godiya.

A hanya sukaci karo ita da ZAYNA kallonta ZAYNA tayi taga irin murmushin dake kan face dinta,
" hadil lafiya naganki cikin farin ciki haka"
" uhmm ZAYNA is all about love"
Tunawa da MAALIK hadil keso yasa gabanta faduwa,
Sai dai ta dake " meya faru da love din" cike da murna hadil ke bata labarin yadda sukai da SHAZMAH,
Tana gamawa ta wuce tabar ZAYNA tsaye cike da bacin rae,
" SHAZMAH in wannan shine choice dinki ki aura bil'adama I am sorry I won't allow it,
" MAALIK shiyafi cacanta dake Wanda zakuyi mulkin MAISUM tare kece hope dinmu bazan yarda zuwana nan yazama a banza ba",
Tafada cikin anger dinta na bakin ciki da bacin rae sosai kai kace ita keda masaurautar.

" tunda hadil nason MAALIK inaga matsalarmu is solve kowa zai aura daya cikin su",
" wannan kuma karyane"
Muryar ZAYNA ta doki kunnenta " SHAZMAH meyasa",
Cike da mamaki SHAZMAH ke kallon ZAYNA,
" eh bazan taba bari ki sama yadda kikeso ba dan kujerar MASARAUTAR MAISUM ke take jira mu mutanenki koyaushe burinmu ki hau ko zalunci zairagu,
" kisani wannan ba burin mu bane kadai jama'ar ki hatta mahaifiyar ki shine burinta",
Cike da mamaki SHAZMAH ke kallon ZAYNA " kina nufin kinsan mahaifiyar ta ",
Sai a lokacin ZAYNA ta gane taso tayi baran barama tagyara zancenta da Tana Jin labari,
" meyasa dole saina koma MAISUM bayan ni nafison nan",
Girgiza kai ZAYNA tayi kina ganin duk sanda suka San ke WACECE zasu yarda su zauna dake ne",
Da confident dinta ta daga kai tace " eh nasan zasu yadda na zauna tare dasu they will accept me"
Girgiza kai ZAYNA tayi "to we will see about that",
Nan SHAZMAH ta juya tabar ta a tsaye binta da kallo ZAYNA tayi,
" inama da kinsan me bil'adama sukai ma mahaifiyar ki a baya da baki yadda da su ba SHAZMAH.

Ba cewa tayi agun MAALIK ne zaune a falon shi yadawo aiki yana kallo kai inka ganshi,
Bazaka taba cewa ba mutum bane saboda yadda yake rayuwa kamar dan Adam,
"MAALIK!"
Takira sunan shi sanda ta bayyana tashi yayi ganinta zaune kusa dashi " ZAYNA mekike a nan",
"Uhmm MAALIK kenan meyasa ba zaka ganni a nan ba bayan kana kokarin bata mana masarauta saboda bil'adama",
Cike da mamaki yake kallonta " ZAYNA meyasa kikace haka kinsan bazan taba zaba wani abu fiyeda MAISUM ba",
Dariya ta sheke dashi " MAALIK kenan kariga ma ka zaba tunda kabar SHAZMAH da soyayyar bil'adama wanda kafi kowa sanin abunda hakan ke nufi,
" kafi kowa sanin abunda yafaru da SARINA Wanda saboda banzar soyayya ta da bil'adama yasa har Yau MASARAUTAR mu takasa samun natsuwa zubda jinin mu yazma ba komai ba",
Sosai MAALIK ke kallonta a wannan lokacin ta fahimci ranshi a bace yake murmushi tayi,
" MAALIK yazama dole SAAL ya mutum a wannan labarin gaba daya dan,
" shi din hadarine ga SHAZMAH da masarautar mu".

Shiru sukai su duka " amma taya zamu kashe shi batare da SHAZMAH ta fahimce muba",
Dariya tashiga yi " hahahahahaha wannan ba matsala bace dan Yau din nan nakeson,
" depriving dinta daga powers dinta gaba daya,
" Kaga kaima zaka sama SHAZMAH under you ko Baka son hakan MAALIK",
Tafada cikin wata siga me ratsa jiki yayinda ta isa gab dashi Tana shafa kirjinsa,
Take akayi wata irin walkiya sai ruwa sosai gurin yayi duhu " zaka iya tabani MAALIK",
Ta rada mishi a kunne dagota yayi sosai inda yashiga kissing dinta a cikin wannan duhun da ruwa da walkiya da ake ta sama MAALIK sosai.

" MAALIK!!!",
SHAZMAH tafada da karfi ganin Sauyin da garin ya dauka lokaci guda ga ruwa ga walkiya kuma ba lokacin damuna bane,
Zama tayi tafara kuka " MAALIK na cikin matsala sosai a yanzu Ina kake MAALIK",
Nan ta zauna zaman dirshen a tsakar dakin tana kuka burinta bai wuce taga MAALIK ba,
Tasan halin da yake ciki tayi iyayinta taganshi abun ya gagara gashi batason neman taimakon ZAYNA,
Dan tajima da sanin ZAYNA muguwace ta karshe dan ko a MAISUM Ana labarin halinta.
" SHAZMAH mekike a daki ke daya Muna can Ana hira gari ya dauka anata ruwa ikon Allah kuma ga iska sosai fa ba lokacin damuna ba,
" taso muje kiga abunda ke faruwa",
Dan dole SHAZMAH tabi bayan innawuro inda suka haura sama dan hango waje,
Sosai ruwa ke wucewa yayi yawa sosai " SHAZMAH kamar Ana ambaliya kiga kayan jama'a",
Rufe ido SHAZMAH tayi sanin cewan Ana controlling din abun ne yasa tashiga laluben mafita.........,,,


Me ZAYNA ke nufi me tayi ma MAALIK haka shin MAALIK zai yadda su kashe SAAL me ZAYNA keso? Shin SHAZMAH will save the day or not......the more you comments the more I type👌

WACECE SHAZMAHTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang