Chapter 10

944 75 2
                                    



Tunda suka fara shiga garin ake bin motocin da ido yayinda wasu ke murna wasu bakin ciki,
Direct motocin basu tsayawa sai wani babban gida irin na kauye amma kusan shine babba,
Gefe massalacine wanda suka ga jama'a suna alwala amma ganin motocin sosai yaja hankalin mutanen wajen,
Parking sukai inda suka fara fitowa " tab yau a kauyen nan lallai za'ayi ruwan kankara",
" lamido dole kam" kada kai wasu suke alamun mamaki ne kawae yayinda wasu ke zuba habaici,
" dama komai dadewa komai dukiyar mutum dole ya nema gida yau ga tabbas nan",
Dady koda ya fito sallama ya musu inda yama momy umarni da su shiga gida zasuyi sallah,
Gaban umma ne ke faduwa rashin sanin mezata tarar a cikin gidan dan dai kam dole da damuwa,
" hadil kuzo mushiga ciki"
Ita ko SHAZMAH da bata San kan komai ba tsayawa tayi sai da momy ta kira sunanta ta nuna mata tabisu,
" wae inna kiji wae yau ya Ahmad ne a wannnan kauyen ko kunya ma baiji ba ya kwaso iyalansa",
" aikuwa inna wuro ni kaina abun nason yabani mamaki amma kuma halin dan yaufa",
Abunda kunnen momy taji sanda suka shiga zauren kansu kai ga shiga cikin gidan.

" Assalamu Alaikum"
Momy tayi sallama suna kallonta amma ba Wanda ya amsa mata zuwa tayi inda inba ke shirin Sallah ta tsuguna,
" Ina wuni inna"
Share ta inna tayi tafara sallolinta sosai hadil taji haushin abunda inna tayi ma momy duk da bata sansu ba,
" Inna wuro manya lallai" tashi inna wuro tayi me makon ta gaida su amma saitai wucewarta ciki",
Abun sosai yakara taba haadil ganin haka yasa momy nuna mata buta " oya tashi kija SHAZMAH kuyi alwala",
Tashi tayi tana zunbura baki " ke kitaso" SHAZMAH ko Jin bata kira sunan ta ba yasa ta shareta barin da take wacce ake girmamawa tasan ko cikin bil'adama akwai babba,
" ke SHAZMAH wae ba magana ake miki ba",
Jin muryar momy yasa SHAZMAH tashi dole zuwa hadil na daukar butar ko tajita empty,
" momy there is no water"
Kallon filin gidan tayi amma Sam bata hango randa bama sai rijiya hakan yasa tace,
" like ga rijiya kija mana" turo baki haadil tayi
" you say what mom seriously" ajiye butar tayi " ke SHAZMAH kidauka kija mana ruwan,
Kallonta SHAZMAH ta tsaya tanayi dan Sam bata fahimci inda ta dosa ba " dauka mana ga rijiyar",
Ta nuna ma SHAZMAH. Wacce ke kallon inda take.

Takawa SHAZMAH tayi a hankali zuwa gun tana lekawa kuwa ganin ruwan da wasu abubuwa,
Tayi Wanda mutum baya gani yasa taji jiri na dibarta cikin wata irin murya taji Ana mata magana,
" barka da zuwa gimbiyar gimbiyoyi SHAZMAH wacce labarin ki yakare de mu tunkan kizo muka San da wannan ranan",
Muryar kamar ba daya bane take ji a kunnuwanta hakan yasa tafadi gefen rijiyar tim,
Da sauri inna ta dake zaman addu'a ta tashi tayi kan SHAZMAH " lafiya ajam ko",
Kallon inda hadil take inna tayi wacce ko a jikinta "ke bake naji Ana kija maku ruwan ba amma shine kike sata",
Girgiza kanta tayi " tab inna nizan Ja ruwa tabdi Allah ya sawa ke walh",
Kallonta inna tayi cike da takaici " toko uwar ki taja ruwa a wannan rijiyar ke har uban naki ma",
Hadil zatai magana momy ta taso ta hanata inda ta dau gugar taja ma hadil din,
Inna kuwa taimaka ma SHAZMAH tayi banda sannu ba abunda take mata bayan,
An idea da Sallah ne maigari ya shigo cikin gidan tare dasu shaheed da Saal Wanda ke Jin kamar Ana cizgar maman jikinsa,
" Karima ku hadu duka yanzu saboda zuwan yaron nan Allah yasa ma kawunshi hussaini na kusa".

Ba bata lokaci ko yan uwa aka hadu da labarin Ahmad da Ni'iman birni sunzo tuni gida yacika,
Sai dai har lokacin ba Wanda yake kula su ko shiga har karsu a dai basu ruwa da fura,
Ahmad kuwa duba ta inda mahaifiyar sa zata billo yake tashi yayi ya isa dakinta,
Bakowa a rufe yaga kofar ya juya ga inna karima,
" Inna lafiya banga innata ba"
Girgiza kai kawae tayi kamar bazatai mai magana ba sai kuma taji bazata iya mai shirun ba,
" katambayi yan uwanka da mahaifinka",
Bayan kowa ya hallara an nutsu ne mahaifinsu ya kalla dady ya yajuya ga kallonsa gun kannan dadyn,
" Amina kinga ikon Allah ko saiga dattijo yau a cikin gidan nan",
kasa magana tayi sai wani irin kallo me wuyar fassara data maka mishi,
" ayi hakuri...."
Dakatar dashi mahaifin nasa yayi " kasan da rasuwar mahaifiyarka",
Zaro ido dady yayi cike da tashin hankali su kansu su shaheed abun ya girgiza su tashi yayi yana girgiza kai,
" aa datti dawo ka zauna"
Komawa dady yayi yazauna yana kwalla yana tambayar yaushe ta rasu ya ba'a sanar mishiba,
" matar ma bata fada maka zuwan su inna wuro da Amina ba"
Kallon momy da jin an ambaci sunan ta ta dukufar dakai yayi,
Shiru tayi zai mata magana mahaifinshi ya dakatar dashi " tabbas sun sanar da baka nan ance baka kasar amma banyi tunanin bazata sanar maka da wannan babban lamarin ba yau shekara dai dai Gina kenan zancen nan da nake maka".

" dama datti nihi dun wadata ko (haka ake ko",
" dama bada shiyasa tun farko bangoyi bayan tafiyar datti burnin nan ba amma kaida hussaina kuka daga kuna ganin bakomi,
" yanzu ga irinta nan yabar gida gaba daya saboda yayi kudi baya neman yan uwansa sam",
Kawu hussaini ne me wannan maganar nan da kyar dai aka shawo kan lamarin dady yayita rokon gafarar yan uwansa,
Cikin ikon Allah yasamu yardar dayawan cikin su yayinda wasu ke kan ba kansu.
Karshe aka bige da hira amma fa su Saal sosai sukejinsu a takure,
Har wannan lokacin shaheed baya son abunda zai hada shi da SHAZMAH Sam,
SHAZMAH kuma duk yadda zasu hadu nema take saboda ta goge abunda yagani a tattatare da ita ko zai daina gudunta,
Da dare kuwa sunsha cizon sauro ba kadan ba tabbas sun San sunje kauyen ruga.

" SHAZMAH! SHAZMAH!! SHAZMAH!!!" Kamar a mafarki take jin muryar nakiranta,
A hankali ta bude idonta Jin kiran kamar yana kuma karuwa yasa ta tashi daga tabar man data ke kwance kusa da inna wuro tafito,
Saida tazo dai2 rijiyar ta tsaya wani abune taga yafito daga rijiyar hasken taga ya koma gefe,
Inda ya rikide zuwa tsohuwa " Ina mika gaisuwa ta gareki gimbiya shazmah",
Kallonta SHAZMAH tayi cike da mamaki " taya zan zama gimbiyarki bayan ni dake ba jinsin mu dayaba",
Dariya tsohuwar tayi " saboda tun kafin kishigo duniyar nan muka sama labarin zuwan ki gun kakaninmu,
" ba jinun da baisan da zaki zo ba sai dai yaranmu da jikoki amma munsan dama zakizo",
Shiru taohuwar tayi na wasu lokuta " sai dai SHAZMAH akwai abubuwa agabanki sosai kalubale saboda daga jinsina harna bil'adama akwai wadanda zaki sha gugurmaya dasu,
" dan haka kikiyaye karki yi wasa da kanki zan dunga zuwa duk sanda kika bukaceni ko kike da tambaya game da jinsina ko bil'adama,
" a karshe Ina shawartarki karki yadda ki shiga cikin ruwan garin nan wanka gwanda in a banda ki ne amma karki shiga kogi!!!",
But ta bace tabar SHAZMAH cike da tunanin ta komawa tayi dakin ta ratsa makwancinta sai bacci.

Biye take da wuka hannunta tana huci yana gudu " please SHAZMAH karki mun haka mena miki",
Ihu yake Tana Kara tunkararshi tana dariya " saina kasheka da dukkan yan uwanka",
Tana fada Tana dariya Tana Kara binsa a zahiri juyi yake yana zufa sosai yana dan kuka,
Hakan ya farkar da dady yatashi inda ya fara tofa mai addu'a a hankali yafara samun nutsuwa ta bace mishi,
Dady bai koma bacci ba saida yaji shaheed yasama bacci me lafiya kafin ya koma.
Washe gari shaheed tashi yayi da zazzabi me zafin gaske " daga kwana daya sai zazzabi",
Inna karima tafada rike da baki Jin ance shaheed ba lafiya,
Nan dae iyayen sa ke ganin malaria ne kuma da rashin sabo.

 

                     Tofah make damun shaheed meyayi zafi haka....meyasa SHAZMAH keda yan gogor maya dayawa.....?
      Tafe muke saimun gano komai ba anwarware shi kaf dinsa.
Don't forget to comment and also share and vote👌

WACECE SHAZMAHWhere stories live. Discover now