Chapter 6

1.1K 76 3
                                    



Yau kwanan SHAZMAH bakwai gaidansu doctor,
Inda tafara ganema kan gidan sosai a yanzu masu kyamarta da hantarar ta nayi abun sai karuwa yake,
" SHAZMAH"
Ya ambaci sunanta "me kike ke daya haka a garden",
Shiru tamasa bata basa amsa ba ganin haka yasa ya fahimci akwai abunda ke damunta,
" owk taso kinga yau Saturday inada break muje kidan sama kaya" Jin zai fita da ita yasa ta saki ranta,
Tafe yake Tana binsa baya har suka isa parking space din ya ma mota key " shiga muje",
Tsayawa tayi tana rarraba ido dan Sam bata San ya ake shiga ba,
Ganin tana kallo yasa ya rufe nasa murfin ya zaga ya bude mata " shiga" nan ma kallonsa take,
" ki shiga muje"
Hawaye ne suka fara tsiyaya a idanunta ganin haka yasa ya matso inda take tsaye,
" meya saki kuka"
Nuna mai motar tayi " bansan meye wannan ba",
Dariya yaso subce masa ganin yadda takalle shi yasa yayi tsaurin maidata ciki,
" zoki kiga yadda ake shiga wannan sunanta mota",
" mota!",
Itama ta maimaita shiga ciki yayi ya zauna " kingani ko" murmushi tayi tare da dauke fuska dan kunya taji,
" to ae kingani shiga muje"
Shiga tayi ya rufe kofar shima ya zaga ya shiga yama motar key karar saida yadan tsorata ta yana ankare sai yayi kamar baiganta ba.

Tana ganin motar tafara tafiya tafara kokarin fita Tana son mai ihu taka burki yayi a hankali yadunga mata bayani,
Basu dau lokaci ba suka fita abun yana SHAZMAH dadi sosai sai mai2 ta sunan take,
" haadil kina kallon yayanki abunda yake",
Mom ta nuna ma hadil ta window suna kallon duk abunda yake faruwa,
" momy Anya wannan yarinyar mutum ce kuwa"
" I don't think so haadil but yanzu me zamuyi akai kina kallon yadda shaheed ya kafe ya tsare kan taimakon yarinyar nan",
Murmushi hadil tayi " I know what we should do why not mukira momyn Khairat na tabbatar inta mai magana dole zai saurareta",
" ko kun kira wannan matar me son kudin tsiya it will be in vain",
Aka fada tabayansu Saal ne dauke da yar black sport bag dinshi yayi kyau sosai saboda yana yin jikinsa,
" amma Saal meyasa baka da Kara ne baka da ta ido yayar tawace meson kudi bayan kadan Tana dashi",
Dariya ya sheke dashi haadil ma biye mai tayi " aiko intazo yabata kudi shikenan ya rufe bakinta",
Kai mata duka momynsu tayi da sauri ta tsere.
"ni zanje gym saina dawo"
harara tabishi dashi  " a dawo lafiya" yafice abunsa.

Tafiya suke shiru amma ganin shirin yayi yawa yasa ya kunna radio mamakin ta inda ake magana take hakan yasa taketa leke like a motar sai dai ya kalleta yayi murmushi,
Inda data gaji ta kalle shi cike da jin haushin dan itama Tana lura da abunda yake mata,
" a ina mutanen nan suke"
Dariya yayi wannan karon dan ya kasa rikewa hakan yasa tayi fushi " SHAZMAH a.....",
" bana son ji nafasa",
Dariya fushin nata yaba sa har suka karasa shopping mall din ba Wanda ya sake kula dan uwansa,
Dan shi dama bamai magana sosai bane hakan yasa yarasa meyasa yake jinsa daban in tana kusa,
Parking yayi ya bude ya zagayo ya bude mata kofa " fito muje" cunno baki tayi " ni bazan jeba",
" are you angry" ya tambayeta cikin halcen turanci mamaki yasa ta dubeshi dan da juya mai baya tayi,
" wannan wani yare kayi mekace naji tunda nazo gidanku anayinsa",
Murmushi yayi " wannan turanci ne" mamaki tayi,
" meye turanci"
" abunda nafada da ake baki ji"
Murmushi yayi a karshe Wanda hakan ya tuna mata ranta a bace dashi yake " nafasa" ,
Nan dae yayi ta lallabata dakyar ta sauka tabishi cikin mall kowa kallonsu yake,
Saboda komai ta gani sai ta taba ta kuma tambaya kallo daya zaka mata kadan bata taba zuwa mall ba infact bata San komai ba,
Hakan yasa shaheed Jin wani tausayinta yana Kara ratsashi har cikin jininsa.

A nan gurin tambaye2 dinta taci karo da shirgin yara inda taga Art book na yara,
Na colouring inda taga drawing din mermaid dasauri ta dau littafin tana murna,
Tsayawa shaheed yayi yana kallonta " me zakiyi da littafin yara",
Shi bai San meta gani ba ita agunta babban abune saboda anzana  zanen yayi kyau kamar mermaid din gaskiya,
Ya mata siyayya ba kadan ba ya kashe kudi,
Takalma riguna turarukan mata sosai ya kashe mata kudi harta yan kana nan under wears ya saya mata da taimakon wata worker din gun dan Sam ya lura SHAZMAH bata san abubuwa irinsu ba mamaki ne yake ta Kara cika shi game da ita,
Koda suka he gida mairo yakira yaba kayan ya mata bayani kan ta koya ma SHAZMAH,
Yadda zata na amfani da kayayyakinta sosai taji dadi dan yanzu tafara sabawa da SHAZMAH sosai,
Dan Sam bata da matsala ko damuwa tasama kawar hira.

MASARAUTAR MAISUM

" mahira nayi duk abunda kika bukata kan SHAZMAH sai dai akwai wani abu da yake daure mun kai",
Kallon bokan mahira tayi tamaida dubanta kan maalik,
" meyake baka mamaki boka" maalik ya tambaya cike da zakuwa,
" mahira abun haryanzu ni kaina nakasa fahimtar sa bare har namiki bayani"
Cike da damuwa mahira take duban boka,
" abune nadamuwa da zai iya jawo ma SHAZMAH matsala"
Ta tambayeshi amma sai ya girgiza mata kai,
" a bincike da nayi kan inda SHAZMAH take a yanzu gurin bil'adaman nan nagano akwai jininmu a cikinsu",
Dafe kirji mahira tayi " jinin mu kamarya",
" ba abun damuwa bane dan shima baisan tsotson shiba bare yasan nata bashi baisan komai game da irin rayuwar mu wannan duniyar ba",
Cike da damuwa su duka suke kallon boka " garin ya hakan ya kasance",
" antsare shi tsari sosai yadda bazan gano meya kaishi can ba kuma ta Ina yakai nan,
" amma nasan ba zasu taba cutar juna ba saima Jin kai da tausayin juna nasan shima lokacin,
" bayyanar asalinsa na nan tafe ku kwantar da hankali.....".

Shigowar sarauniya safwana ne ya katse su daga tattaunawar da suke kallonsu tayi,
Daya bayan daya take binsu da kallo yayinda tsoro da fargaba duk yaga ma dira a zukatansu,
" sanin kowa ne a wannan gari na nawa bana fada na maimaita sannan bana son karya,
" dan haka tambaya daya zan muku  Wanda shine Ina SHAZMAH!",
Mahira ce  tasamu ta yakice tsoron dake zuciyar ta tashi ta fuskanci safwana dake tsaye tana huci,
" ke zan tambaya wannan kalmar dan kowa a wannan gari yasan ke kika rufe ta kike azabtar da ita,
" inkuma wani abune ma ya sameta yana da kyau kifito fili kifada mana Ina SHAZMAH",
Take jama'ar dake biye da ita da yan kallo suka fara cecene kuce inda dayawa suke marawa mahira baya saboda,
Kowa yasan safwana da zalunci da yadda ta kwace masarautar a hannun maman SHAZMAH ta yaudareta,
Ganin tuhuma naso ya dawo kanta tabar gun tare da mabiyanta da rundunar ta,
" Omid!!!"
Takira sunan da karfi jiki na bari ya durfana a gabanta,
Jira kawae yake yaga makomarsa a wannan lokaci.

" Inaso kaje duk inda SHAZMAH take inaso akawo mun ita yanzu nan",
Ba bata lokaci ya diba wasu daga masu tsaron fada da makamai suka tafi,
" sabeer inaso ayo kira ga dukkan masu duba da bokayen wannan gari namu dan,
" duk inda SHAZMAH take inaso a nemo mun ita in yazama dole ta mutu inaso ta mutu a gabana",
"Angama"
Abunda yafa kenan shima yafita yin nasa aiken,
Wani irin shegen dariya safwana tafara yayinda duk halittun dake gabanta suka tsorata,
Duk sanda tayi dariyar gaba daya gurin ke jijjiga,
Hatta sahima a wannan lokaci gefe tayi saboda tsoron uwartata,
Gaba daya ko ina yadauka neman SHAZMAH ake ruwa a jallo mahira tuni suka koma gida da maalik,
" maalik yanzu ne yakamata kabar wannan guri",
Matsowa yayi ya riko hannun mahaifiyar tasa " umma bazan iya barin ki ba a yanzu ki bari komai ya kafa",
Girgiza kai tayi "maalik inatsoron abunda safwana zatai mana a yanzu banso ace bani bakai,
" kaje yanzu nasan in anganka zaaga kamar nemanta kaima kake",
"A'a umma"
Dakyar ya lallabeta ta yarda sai komai ya lafa zaibar gida zuwa inda shazma take.

GUN SHAZMAH

fita tazoyi falon inda suka ci karo ita da Alhaji Ahmad mahaifinsu shaheed amma me,
Wani abune tagani a tattare dashi Wanda ita kadai take iya ganin abun ni kaina,
Mimsqueen bangani ba ha tayi da baya ya mata murmushi suka gaisa yafita abunsa,
Daki taje da sauri ta rufe kofa inda Tana kallon bango Alhajin ya bayyana sai kuma wani halitta ta bayanna tattare dashi,
" baiwar Allah meyasa kikeson shiga aikin da baishafe kiba"
Murmushi tayi tana kallon abun " kiyi gaggawar cire hannunki ciki",
" kai!"
Cikin tsawa tamai magana Wanda har saida ya tsorata" kafita daga inda yake banson Kara haduwa dakai a wannan gida inkaki zamu dama",
Cike da tsoro yake kallonta wannan karon " bansan a halitta ke wacce bace dan baki cikin jinsina baki cikin jinsin bil'adama",
Murmushi tayi " wannan ba lallai kasani ba kakaninka zasu sani kayi yadda nace ma",
" angama"
Yafada bai bata lokaci ba yabace bat jikinsa Alhaji ya bayyana saida ta tabbatar da lafiyarsa kafin tadaina ganinsa,
Take bogur ya bayyana...........

    

         Tambayata bai wuce me SHAZMAH ta cire ma Alhaji ba kuma meyasa abun ya shigesa ba kubiyo a next page dan cigaban labarin don't forget to comments and share👍

WACECE SHAZMAHWhere stories live. Discover now