Chapter 7

977 67 3
                                    



" bogur lafiya",
" SHAZMAH kinyi abunda yasa na bayyana batare da na shirya ba",
Cike da mamaki take kallonsa Sam fuskarshi ba walwala kamar yadda tasaba ganinshi,
" lafiya menayi",
" gimbiya kidaina shiga cikin sabgar bil'adama da aljanu",
Tabe fuska tayi wannan karon " baka ganin cutar sa yakeyi"
Murmushi yayi wannan karon " shima sashi akayi aikinsa yake yi",
Cike da mamaki take kallon bogur,
" wazai sashi shiga jikinsa dan ya cutar dashi",
" Bil'adama da kansu suke jawo ma kansu wannan",
Ya bata amsa sai dai Sam bata gamsu da amsar saba,
" kana nufin dan uwansa bil'adama ya aikoshi",
Murmushi yayi yana kallonta " akwai abubuwa tabbas da dama da baki sani ba kan bil'adama wanda sai a hankali Zaki fuskanci hakan,
" bil'adama suna da son kansu basu damuwa da junansu koda hakan zaijawo cuta ga jininsu ko wani nakusansu,
" bazan fada miki waya aiko wannan jinnun ba amma nasan a yan kwanaki Zaki ga komai kamar yadda kika kare shaheed daga Sharon yar uwar sa",
Zaro ido tayi cike da tsoro da ban mamaki " kasan wannan ma bogur",
Murmushi yayi me sauti " Ina sane da duk abunda kike ciki yanzu haka masarautar mu nan a hautsine yake Ana nemanki".

Dafe kirjinta tayi cike da tsoro " safwana!" ta ambata cike da tsroro,
" karki ji tsoro bazata taba gano inda kike ba saboda baki cikin wannan duniyar aiki ne babba gano ki a duniyar bil'adama ki kwantar da hankalinki",
Yana kaiwa nan ya bace SHAZMAH kuma tsorone ya cika ta,
Jikinta har bari yake tsabar tunawa da safwana  Wanda tuni hakan ya haifar mata da zafin jiki,
Tuni ta kwanta tsakiyar dakin jikinta na bari wani irin azababben zazzabine ya rufe ta nan da nan,
Inta rufe ido ba abunda take gani sai cikin duhun da safwana ta ajiye ta da irin horon da tayita bata.

Fitowa yayi cikin kayan gym din nasa Wanda duk Wanda ya kallesa sai ya kuma,
Manne earpiece dinshi yayi a kunnensa tare da sa kidi ya nufi kofar shiga yayi pushing glass door din ta bude,
Abunda idonsa ya hango masa tashin farko yasa ya cire earpiece din daga kunnuwansa,
Kyawawan idanunsa ya watsa mata yana kallon yadda body dinta ke jujjuyawa kan bike circling machine din,
" hi handsome",
Wata budurwa dake gefenta tafada tare da tashi ta nufi inda yake,
Binta da kallo tayi taga Wanda ta gani din,
Murmushi yayi tare da taku zuwa inda budurwar take " hi cutie" yafada tare da dan jan kumatunta,
" kwana biyu baka zo ba lafiya handsome dina",
Tafada tana kare mai kallo " kinsan sometimes dole a dan huta ayi concentrating kan wani abu",
" yes you are right anyway way you are still looking so handsome"
Tafada tare dan jan kumatunsa,
Ganin eyes dinshi tayi baya kanta hakan yasa takai kallonta inda yake duba,
" oh boy you are very naughty"
Tafada tare dan bugun sa tana nuna mai inda yake kallo Tana murmushi dan fuskewa yayi tare da canza direction.

" Sofie!"
Yaji yakira sunan da sauri ya juya suka hada ido da sofie din,
Budurwar dariya tayi " zo nayi introducing dinka ga our new member",
Binta yayi suka karasa inda sofie din take tashi tayi da sauri dan dama Tana dan basarwane,
" good morning Sir"
" morning how are you ya gajiyar aiki hope jiya ban baki wahala ba",
" bakomai sir ae aikin kenan",
"Hye! Hey!! Wait of"
Tafada sanda tashiga tsakiyarsu " a ina kuka San juna",
Murmushi su duka sukai " I am his sacretary"
" wow that gud" tafada tana kallon Saal Wanda yadan juya a dole irin jan ajin nan,
Rike hannunsa tayi " muje I need to see you",
Bai musa ba yana kallon sofie wacce takoma tamaida earpiece dinta taci gaba da abunda take,
" why kike son ganina Alisha"
Murmushi tayi tana kallonsa " Saal we both know each other so well I hope your eyes are not on her because she is damn hot",
" seriously Alisha you shouldn't have waist your time in becoming a model dan Sam detective yakamata ki karanta",
Dariya sukai su duka.

" but why do you ask bayan kinsan inason irin type dinta"
Kallonsa tayi batare da ta bashi amsa ba " oh shit don't tell me she is yours dan nasan you are always interested in girls",
" no no please karka soma dan Sam ba type dina bace",
" amma Alisha baki tsoro yakamata ki hakura da wannan harkar kinsan ba abu ne mekyau ba",
Harara ta watsa mishi " to Mr.preacher mind your business kaima ae abunda kake da mata ba abune me kyau ba anyway go and give her a helping hand dan dama nagaji she is given me headache tun sassafe",
Murmushi yayi " gaskiya dama daci gareta anyway nima I need someone that could preach me",
Harararsa ta kuma yi " owk owk natafi" murmushi tabi bayansa dashi.
Alisha friends ne da Saal tun secondary school itama parent dinta nada kudi sosai,
Halayyar su ce tazo daya dan inkaga suna wasa da dariya to tsakaninsu ne Alisha,
Yan gidansu da iyayensu sun San juna suna mamakin yadda suka shaku amma in zancen soyayya yatashi babu shi tsakaninsu,
Sai dai shi he is soft a heart especially in heart issues but she is not dan bata forgiving din duk Wanda yataba ta,
Kowa yasan sirrin junan dan uwansa da halinsa hakan yasa ba matsala tsakaninsu amma suna da kyamar mutane especially talaka kona kasansu wannan kenan.

" shaheed me kake shirin yi kan batun yarinyar nan SHAZMAH",
Kallon Dadynsu yayi tare da maida kallonsa ga momy wacce zuciya ke sama,
" Alhaji wannan har wani abu ne da saika tambaya kawae yaje ya maidata inda ya dauko",
Hararta dady yayi yace " shaheed kai nake saurare",
Sunkuyar da Kansa kasa yayi tunawa da hirarsu da SHAZMAH da yayi inda ta shaida mai bata da kowa iyayenta basa raye bata San kowa ba,
Dan asalin su ba yan Nigeria bane dagowa yayi ya shaida ma dady duk abunda ya sani,
"Allah Sarki to bakomai saita cigaba da zama a nan din amma zan kira commissioner in mai bayani duk yadda mukai shikenan",
Tashi momy tayi " Sam bazai yuba ya zaka ce ta zauna yarinyar da bamu San asalin ta ba kuma kafa duba kaga yanayinta,
" sam banajin mutunce koma mutunce din ae zaiyu mayyaceko wani abun bada yawuna ba",
Shaheed Jin mahaifiyar sa ta dage yasa shi tsoro dan tunda yataso dady baitaba ma momy musu ba bare kan wannan maganan,
" inba da yawunki ba nida yawuna tunda dake da dukkan abunda ke cikin wannan gida karkashin ikona kuke sai kiyi",
Yana kaiwa nan yatashi yabar falon mamakine sosai shaheed yake bashi kadai ba ita kanta tsoro ne ya dirar mata da mamaki,
Mairo dake kwashe kaya kan dinning itama sabolo tayi wannan abune da sai yau tafara gani.

Da sauri tabar falon momy dakinta ta wuce direct saman gadonta tahau tasa hannu saman drawer dinta,
Wani akwati ta dauko ta sauke har lokacin zufa take gabanta na faduwa da sauri2,
Ta bude cikin akwatin inda wasu abubuwa masu kama da kayan tsafi suka bayyana aciki,
" what!"
Tafada tare da zaro ido wani kwalba naga ta dauka Wanda ke daure da jan kyale,
Wanda yake a bude saman " hehehe waya shigo ya bata mun aiki bayan Sam bamai shigo mun daki",
Maida komai cikin akwatin tayi tarufe tare da mai dashi saman inda ta dauko shi,
" dole na koma wajen boka",
Jawo wayar ta tayi tafara kira ringing na uku aka dauka,
" dakatar ba zancen Sallama kishirya gani nan zuwa akwai babbar matsala zamu daji",
Tana kaiwa nan ta katse inda ta raruma abubuwan da take bukata tafice saida ta tabbatar tasama dakin kwado kafin tawuce.
" uhmm hmmm itace"
SHAZMAH tafada dan duk abunda yake faruwa a idanunta yake faruwa to amma tambayar ta,
Ina zata tunda taji Tana gun nima kuma daji,
" a ina bokan bil'adama yake",
Shiru dan bata da amsa " dole zan bita amma bazan iya binta Tana ganina ba kuma bogur ya hanani ba cewa Sam",
Tunani ne ya isheta sosai ta rasa yadda zatai can kuma sai tace " bakomai inya bata tata agun nasu koya turo zan gani zata dawo",
Da wannan hankalin ta tasamu ya kwanta.

   Next page teaser:  " yazama dole nadau revenge kan abunda Saal yamun and I won't have it withought your help sofie",
Murmushi sofie tayi takuma shigewa jikin Alisha " don't worry anything for I will make him pay for it for sure just kibar ni dashi zaiyi kuka",
Murmsuhi Alisha tayi " nasan Zaki iya" tashi sofie tayi,
" amma naga you are close meya miki haka" tabe baki Alisha tayi " koma meye Zaki sani with time" "ok" 😣😣😣


                        Sai mun hadu a next page keep following don't forget to share and  vote.....👌👍

WACECE SHAZMAHWhere stories live. Discover now