Chapter 12

899 62 7
                                    



" Abunda nakeso dake yanzu shine wannan dan naki babba kinsan komai game dashi ko kinason na miki tuni ne kanshi",
Da sauri momy ta durkusa gaban boka " A'a bana son kai  tuni kan abunda yawuce komai kakeso kaban umarni zanyi yadda kakeso",
Kallonta boka yayi cike da jin dadi " hahahahahahahaha da farko yaron nan naki kiyi kokari kar me magani Wanda yasan kan abubuwan da ku bil'adama baku gani yaganshi"
Murmushi momy tayi " wannan aikin ae me sauki ne duk yadda lake so kamar anyi anga...",
" dakata banga ma fada miki sauran bukatuna ba",
Cike da tsoro ta dago kanta Tana kallonshi,
" SHAZMAH!"
Yafara cikin wata iriyar murya momy tai saurin dagowa " SHAZMAH kuma",
" kwarae SHAZMAH indai kinaso bukatunki su cika kicigaba da yadda kike yazama dole kisan duk yadda zaki yi SHAZMAH tashiga ruwa",
Dagowa momy tayi da alamomin tambayoyi kan fuskarta " kar kiyi tambaya kiyi kawae abunda nakeso shine tsirarki",
" hahahahahaha" ya bace mata but tashi tayi ta koma kan dan gadon cike da tambayoyi,
" meya hada boka da  SHAZMAH meyasa yakeso tashiga ruwa koma meye,
" tabbas yazama dole nayi yadda yakeso kodan samun fadata a hannuna inma kasheta yakeso zanyi",
Murmushi tayi tana girgiza jikinta " lallai nazata bazan kuma samun dama ba gata ko tadawo".

Zama sukai kan dan dutsen dake gefen rafin suna kallon ruwan shiru sukai kowa yana tunanin abunda zaice ma dan uwansa,
" Amma Maryama nalura kawar nan taki bata son magana",
" meyasa kace haka",
Kallon SHAZMAH yayi wacce gaba ki daya hankalin ta baya kansu cike take da takaici,
Wanda bai wuce Tana ganin ruwa ba halin shiga Ba wannan ne damuwarta gaba daya,
" naga tunda na hadu daku bata kulani ba sai taso magana takeyi",
Murmushi innawuro tayi " dan dai bata sanka bane amma kabata dama zakaga sauyi",
Murmushi " toshikenan Aisha zanci gaba da bibiyarki harki saba kisake dani,
" inafata bazai dau lokaci har na koma birni bako",
Dariya innawuro ta kwashe dashi " bari na nuna muku wani abu",
Innawuro tafada tare da tashi inda tasauka can nesa dasu tafara hada duwatsu,
Gogan kuwa zuba ma SHAZMAH ido yayi wacce take kallon rafin kamar Tana saurar wani abu,
" ka..." ganin hankalinshi nakan SHAZMAH yasa innawuro murmushi " tabbas inda gaske Saal yaso SHAZMAH zasuyi soyayya me zafin gaske",
Kome ta tuna kuma saita bata rae " Uhm sai in wannan uwar tasa me shegen Jin kan nata ta yarda ma tukunna.

SHAZMAH sosai take sane da kallonta Saal yake duk wannan lokacin hakan yasa kirjinta ke bugawa,
" Saal Aisha kungani"
Tafada tana nuna masu hannunta da take dauke da duwatsu" karba nan ga naka",
Ya mika hannunsa ta zuba mishi a ciki sannan ta zuba ma SHAZMAH,
" bari na nuna muku yadda nakeyi idan nazo",
Jifa tayi da dutse cikin ruwan Tana dariya Saal harda tayata ihun " yeee" shima ya tashi da niyyar zasu jefa,
Aisha na kokarin jefa nata SHAZMAH ta rike hannunta,
Cike da mamaki su duka suke kallonta cike da wani irin yanayi mekama da tsawa yafara yima,
Innawuro magana " karki kuskura kijefa kinzata mutane kadai suke rayuwa a cikin duniya,
" baki tunanin me zaki jefa me zaki samu kwata2 inkika kashe wani abu a cikin ruwan fa",
Dariya Saal ya kwashe dashi " lallai Aishar tawa nada tausayi banda abun ki ae wannan bakomai bane dan ka jefa dutse ruwa",
Bata tanka mai ba ta sauka takama hanya kallon juna sukai sai kuma suka bi bayanta suna kiran sunanta,
Sam bata da niyyar tsayawa ta sauraresu,
Dakyar Saal yasha gabanta " Haba Aisha meyayi zafi Muna hirarmu munajin dadi zaki dau fushi haka iye kiyi hakuri kinji",
Yafada yana kama kunnensa yadda yayi abun haka nan taji ya burgeta nan ya cika ta da surutu,
Karshe dae harta saki jiki take samu su baki suke hira,
Saal sosai abun ya mishi dadi ganin zai sama bagas a kauye koya ne ta hadu a ganinsa zai rage zafin,
Zaman sa a kauye da ita bangaren innawuro tunanin yadda abun zaka re take duk randa Saal yagane da wacce yake tare basu koma gida ba sai guraren magrib saida suka tabbatar yaraka su giddan innan innawuro yatafi a zaure suka tsaya harya tafi kafin suka samu suma suka koma saida suka tabbatar bazai gansu ba.

4DAYS LATER

" yau kwanan mu dai2 har hudu agida duk yadda zanyi yarinyar nan tashiga cikin rafi abun yacitura,
"Har wanki nabata amma Ina komai bata iyaba gashi boka bazai taba mun sauki ba",
" hahahahhahahahha kidaina wahalar da kanki dan wannan babin angama dashi yau zata shiga ruwa",
" taya kenan"
Dariya ya kuma yi " wannan ba huruminki bane ki tsaya kiyi kallo zaki sha mamaki",
Yana kaiwa nan ya bace yabarta zaune sallama akayi,
Ganin wacce ke bakin kofar yasa momy sunkuyar dakai " ah lallai dole ki sunkuyar dakai Ni'ima tunda burinki kiwatsa mana kasa a ido",
Sosa kanta tahau yi irin borin kinyar nan " sannu da zuwa goggo rakiya" karasa shiga dakin tayi,
Ta nema guri ta zauna zata gaishe ta Inna rakiya ta dakatar da ita " yanzu ke Ni'ima abunda kike kinkyauta kenan ace ke ba ruwan ki damu yan uwanki dan iyayen ki basu raye,
" tunda kikai aure fa a kizo gida ba ga yan uwanki wadanda kuke 'yan uba amma Sam kinkisu,
" damu baki daya me muka taba miki da zaki mana haka kinzo zuwan farko amma sai dai muji labari haba haba sai yar uwar ki ke zuwa ko bata fada miki ba,
" ita Tana zuwa ganin gida amma ke Sam sai kace ba uwa daya like ba ko dake tace itama hakan kike mata",
Cike da mamaki momy ta kallah inna rakiya sai dai bataso tayi musu especially kan yar uwar ta da suke same uwa same father,
Nan Ina taita mata fada karshe sukai washe gari zata tagagga yan uwanta basu hakuri.

Zaune suke tsakar gida suna hira da innawuro sai gefe hadil dake fama da danne2 din wayar ta,
Yashigo da sallama ya warke sosai bazakace akwai abunda yake damunsa ba,
Dam taji gabanta yafadi haka kurum ta tsinci kanta da jin batason kallon fuskar shaheed,
Bayan sungaggaisa dasu hadil da innawuro ne ya kalleta " SHAZMAH taso kirakani ganin gari",
Yi tayi kamar bata Jisaba har saida innawuro ta mata magana yayinda hadil tagama kulewa,
" SHAZMAH!"
Taji ankira sunanta da irin muryar da tsohuwar nan ta taba mata daga cikin rijiyar nan,
Tsayawa tayi tana kallon rijiyar shima kallon rijiyar yayi cike da wani yanayi me wuyan fassara,
Sai ya juyo ya kalla SHAZMAH " jeki dauko gyalen maza mutafi kafin yamma tayi",
Juyawa tayi da sauri dan daukowa inda takarajin ana cemata " SHAZMAH karki bishi ba......",
Dif taji muryar ta dauke dama wannan karon wani iri taji murayr namata hakan yasa bata zargi komai ba tashiga ta dauko,
Da zasu fita tsayawa tayi tana waigar rijiyar shaheed ya mata tsawa " kefa nake jira",
Ajiyar zuciya tayi suka fice tafe suke bawanda yake ma dan uwansa magana inda taga sun tunkari hanyar,
Rafi dake yanzu tasaba fita itada innawuro da Saal zuwa rafin.

Direct ya wuce gaban rafin take taga yanayin gurin na sauya mata gani tayi yafara sa kafansa cikin ruwan,
" shaheed! Shaheed!! Shaheed!!! Karka shiga kazo mutafi",
Tafada cike da tsoro da fargaba especially tunawa da tayi tunda tazo garin komai nata yaki amfani,
Juyowa yayi yana kallonta yana dariya " hahahahaha" kwayar idonsa blue suka koma ga wani haske da suke tuni ta tuna da rikiyar nan,
Tabbas tayi wauta da bata saurara maganar tsohuwar ba,
" kinaso kitaima keshi kamar yadda ya taimakeki ko tokishigo cikin rafin kitaimakeshi",
Aka fada cikin wata murya tare da kara fecewa da dariya,
Ji tayi Ana tumbul tumbil acikin ruwan Ana " Ataimakeni dan Allah please help me",
Da muryar shaheed taga ruwan na shanyeshi yana juyi da gudu ta isa bakin rafin,
Batare da bata lokaci ba tafada cikin rafin tuni komai na jikinta yafara sauyawa...........,,,



                     To be countinue soon.....
     Don't forget to share and vote for more.👌

WACECE SHAZMAHOnde histórias criam vida. Descubra agora