Chapter 26

744 41 2
                                    




Kai tsaye office din ya nufa sai dai koda ya isa kasa murda kofar yayi wani irin kunya da takaici ne ya rufe shi,
" you can come in",
Yaji nafada daga cikin office din haka nan ya tura Kansa zuwa ciki,
" good morning sir"
Bai dago ya dubeshi ba yana duba wani files,
Bai kuma amsa shiba sam  wani iri Saal keji game da Mal.Abubakar,
Wanda kaf duniya cikin ma'aikatan companies dinsu Dadynsu ya yadda dashi fiye da kowa,
Kuma Amininsa ne sosai abokin shawararsa,
Cire glass dinsa yayi yakalla Saal dake tsaye tare da nuna mishi kujerar dake gabansa.

" A gaskiya Saal Yau ka bani mamaki sosai bantaba zaton zaka iya irin wannan aikiba,
" kuma karasa a inda zaka aikata wannan mummunan aiki sai gun aiki meyasa kayi hakan,
" baka tunani mahaifinka yazo ya tarar dakai cikin wannan halin",
Shiru Saal yayi yana bashi hakuri shiko Abba Sam baibi ta kan hakurin ba saima fada dayake ta Kara yimasa,
Sai daya gama mai fada sannan kuma yakoma ga yimasa nasiha me ratsa jiki kan abubuwan dayake aikatawa,
Karshe Saal godiya yamai yafita da tunanin sallamar sofie a aiki dan Sam baya Jin zata hakura tabarshi da wannan aikin Sam.

" beb akwai problem fa and I have to let you know",
Ramsey dake kwance Tana mika kallon faith tayi,
" wani irin problem kuma bayan anjima zaki rakani naje nayi yadda baba yace,
" kinsan matsala ta bata wuce ta nasama Saal a rayuwa ta bazan taba gajiya dayin asiri danshi ba",
Girgiza kai faith tayi " baba yakirani dazu yake shaidamun da na hanaki yin wannan aikin",
Dariya Ramsey ta sheke dashi " ta nan kika billo kuma you know I must do it to have him back",
" and tunda baba yace don't you shouldn't dan we don't know why he asked you not to ko".

" look faith idan rakiyace baki son mun fine but don't ask me that dan nothing can stop me",
Girgiza kai faith tayi cike da takaicin kawar ta,
" then I have nothing more to say but I am not in walh I am totally out of this" tafada tana daga hannu,
" fine" Ramsey tafada sanda faith tafita tsaki ta bita dashi,
" shegiya arniyar banza dama who cares can ta matse miki enemy of progress,
" yes of course kawae bataso nada Saal ne taganshi very cute and handsome gashi very rich",
Nan tayi ta surutan ta kan dole saitayi abunda takeso.

" SHAZMAH na cikin wani yanayi MAALIK nasame kane dan kasan meke faruwa",
Kallon Dattijuwar jinnun yayi  cike da tambayoyi da mamaki,
" basai ka tambaya ba zan fada maka koni WACECE sunana safiyya na kasance Ina rayuwa cikin kauyen da kukaje kwanaki,
" Wanda a nan na hadu da SHAZMAH kasancewa munjima da sanin zuwan ta yasa nayi alkawarin kare ta daga dukkan cuta",
Gyara zama MAALIK yayi dan son jin abunda safiyya keson sanar mishi game da SHAZMAH,
" ko kasan SHAZMAH tafara sauyawa ko Baka ga sauyi a tattare da itaba matsayin ta na mamiyota bata samun shiga ruwa yadda yakamata,
" ko kasan Tana tattare da jinin sarauta yakamata ka fahimci Tana da banbanci da sauran yan masarautar ku".

Tabbas MAALIK yaga sauyi a tattare da SHAZMAH kan yadda take nuna zata iya komai akan Saal,
" tabbas zaka fahimci haka kodan yadda take nunawa kan Saal Ina mai tabbatar maka in bata sama ruwa na kwana goma ba,
" za'a sama matsala dan SHAZMAH yanzu kullum sake juyawa take a kuma yadda bil'adama masu son Saal ke binshi da tsibbu,
" tabbas za'a iya rasa rai" da sauri MAALIK ya kalla safiyya,
" yanzu ya zamuyi dan kar abun yayi zurfi",
Ba cewa tsohuwar tayi sosai yake cikin fargaba da tashin hankali,
" ya zama dole na nema hanyar da zan dauke ta daga gidan nan",
Tunani yake sosai dan neman yadda zaiyi da SHAZMAH tun kafin yakasa controlling dinta.

Yau tunda tadawo school ta kwanta ita kanta innawuro kwana kin nan Sam bata gane kan SHAZMAH,
Wani irin fili ne Wanda banda kasa bakomai ga rana me zafi aciki,
Kafafunta banda zafin kuna ba abunda suke mata,
" SHAZMAH! SHAZMAH!! SHAZMAH!!!",
Da karfi ake kiran sunanta a cikin wannan filin me azababben zafi banda juye2 babu abunda take,
Bata hango alamun komai a cikin saharar,
Ita bata zauna ba ita kuma bata tsaya ba sam,
Ji tayi kasar Tana darewa kafin tayi wata2 taji tana nitsewa ciki kamar Ana cire mata namar jikinta,
Wani irin Kara tasa wanda lokaci guda ta farka daga wannan mugun mafarkin take idonta suka sauya colour.

MAALIK ne yayi saurin bayyana gareta inda yasa hannunsa kan idonta take suka koma dai2,
Sam bata San ma tanayi ba sake fadawa tayi kan bed din,
Tacigaba da bacci murmushi MAALIK yayi ya bace a dakin tabbas yasan lokaci yayi da zai dauke ta,
SHAZMAH bata tashiba sai kusan magrib dake innawuro tafita gidan wasu yan garinsu,
Mairo kuma aiki yamata yawa bata ma San SHAZMAH na bacci ba.

Toilet tashiga ta dauro alwala kamar yadda su innawuro suka koya mata ta gabatar da salolinta,
Bayan ta idar ne ta fita zuwa falo Saal na zaune akan kujera,
" innawuro!",
Jin muryarta yasa ya dago yana kallonta sosai tamai kyau " tabbas itace",
Abunda tafada kenan  yana kokarin mata magana ji yayi kamar wani abu na shiga jikinsa,
Lokacin ita kuma ta duba inda yake  ganin abunda ke shiga mishi Wanda shi baya gani,
Take taji duniyar ta ta sauya cikin kankanin lokaci ta bace a falon batare da yasani ba sakamakon ciwon kai daya sauka mishi take.

Tsaye take tana zuba abubuwan cikin dan rafin Tana kiran sunan Saal sanda SHAZMAH ta bayyana gabanta,
Cike da tsoro Ramsey ta yar da abunda ke hannunta,
Jikinta na bari ganin abunda bata taba gani ba,
Tana baya2 SHAZMAH nuna ta tayi da hannu,
" hakika kin kasance me son kanki kuma sannan me taurin kai dan haka ba sauran Dana sani",
Hannunta ta dago inda Ramsey ke rike da wuyanta da duka hannayenta tana kakari,
Alamun wahala idannunta sun firfito sosai,
Baa dau lokaci ba ta zube a kasa faruwar ta yayi dai2 da zuwan MAALIK gun,
Sai dai Ina yayi latti dan aikin gama ya riga ya gama tuni SHAZMAH tasa wata irin muguwar Dariya da bai santa dashi ba sam ta bace.

MASARAUTAR MAISUM

" hahahahahaha tabbas aikin Janna kyau boka",
Bogur dake kallon abunda ke faruwa da SHAZMAH da MAALIK kamar tv Yafada yana nunasu,
" yanzu na kuma yarda dakai boka dama kace akwai lokacin da plan dinmu zaiyi aiki,
" yanzu kaga Muna daga nan Muna controlling din rayuwarta ita da kwanciyar hankali har abada kamar uwarta",
Yakarasa yana dariya " uhm uhmm bai kamata mufara farin ciki ba dan tabbas duk randa SHAZMAH tashiga ruwa aikin ya warware",
Bogur tashi yayi zaune tare da gyara zamansa,
" Hakane kam amma nasan zaka iya hanata shiga tunda shigar ta ruwa rushewar aikin mune".

" Hakane kaje Ina bukatar ka yanko mun dan gashin SARINA zan hada ayi aikin dashi",
" to yanzu ma kuwa saina biya gunta zanje gida da safe zankawo",
Tashi bogur yayi yakama hanyar inda ya adana SARINA mahaifiyar SHAZMAH,
yana zuwa kogon aka bude mishi kofar da zai sadashi da gunta,
Banda gaidashi ba abunda ilahirin halittun dake gun keyi,
" SARINA!"
Jin muryar Wanda ta tsana a rayuwarta yasa tafara komawa da chain din dake daddaure da jikinta,
" Bakin mugu Azzalumi Ina nan inajiran ranar da kowa a wannan masarauta zai San kai waye",
Wata irin dariya yasa yana tafawa tsabar mugunta.

" SARINA Anya Zaki kai ga ganin wannan rana",
Murmushi tayi " Raina baa hannunta yake ba kaida bokan kana hannun Allah yake",
Tafada cike da bacin rae wani irin mugun cafka yakai mata,
" SARINA bazaki fasa kiran sunan ubangijin bil'adama a nan bako ko kinmanta nan masarautar daban da can",
Dariya tayi " Bogur Allah yana ko ina shiga halicce bil'adama ya kuma Haliccemu du.....",
" dakata hakika ina bala'in sonki SARINA amma kika ci amanata kika shiga duniyar bil'adama,
" nikuma bazan taba barinki hakan ba bazan kashe kiba SARINA amma bazaki daina fama da azaba ta ba kuma inaso kidaina kiran sunan duk abunda kika sani daga wancan duniyar dan bazai taimakeki a nan ba",
Bata kuma magana ba dan tasan ba abunda bogur baiso irin yaji bil'adama yankan gashin ta yayi kadan Tana kallo yabar gun,
" bogur inama da zaka gane cewa SHAZMAH farka ce ta cikin ka bata wani ba",
Tafada tare da sakin wani irin kuka me ciwo.




                     Kucigaba da hakuri dani sai mun hadu a next page Insha Allahu👏👏👏

WACECE SHAZMAHWhere stories live. Discover now