Five minutes din daya gaya mata ita ya dauka, daga ganin yadda yake haki tasan cewa da gudu ya hawo stairs din. Yana zuwa ya fara jera mata sannu, da hannu tayi masa alamar ya bata rigarta ta saka, ya dauko ya saka mata ba tare da ta saka komai a ciki ba. Ya dauko jakar asibitin su sannan ya kamata ta mike suka fara tafiya a hankali, in ciwo yazo a tsaya a huta yana mata sannu yana shafa mata bayanta, sai ya lafa sai su cigaba. Kafin suje asibiti already ya kira ya fada cewa gasu nan a hanya, dan haka kafin suje har an fito da gadon marasa lafiya ana jiran su. Ko dai dai da minti daya Nura bai bar side din Aisha ba har dakin haihuwa, dayake dakin single room ne daga ita sai shi sai mai karbar haihuwar, yadda take hada gumi shima haka yake hadawa rigarsa ta jike sharkaf da gumi, in tayi masa wani rikon kuwa ji yake kamar zata balla shi amma haka yake hakura dan yasan ita ciwon da take ji yafi na karaya zafi. Da yaga abin babu sassauci yace da midwife din ko zata yi mata wata allurar da zata tsayar da haihuwar ta dan samu ta huta, matar tana yi masa murmushi ta gaya masa it is not possible, already ta kai 9cm yanzu dan haka minti kadan ya rage mata. Mintuna kadan din kuwa Aisha ta fara nishi, ranar Nura yaga tashin hankali, midwife din tace masa yazo ya leka ya gani in yana so, da sauri ya girgiza mata kai, Nura ya kara imani sosai ya kuma kara son mahaifiyarsa (maza a daure ake shiga labour room gurin haihuwar matan ku). Na farko yana fitowa aka dan dake shi ya chanyara kuka aka dora shi akan kirjin Aisha, ga mamakin Nura sai yaga ta saka hannu ta rike abinta, tana kokarin haihuwar na biyu amma tana rike da dayan, uwa kenan.

Ana dauko na biyun Nura ya kai hannu zai karba baki har kunne amma Aisha ta hana shi, haka ta hada duk biyun ta rungume. Shi so yake yi ma ya leka yaga mata ne ko maza ne amma ta hanashi, matar tana tayi masa dariya tace "congratulations, you have very cute identical twin boys" Nura hamdala kawai yake yi yana karawa, a lokacin ya fahimci mai hausawa suke nufi in sunce mutum yana farinciki kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha, dan yasan da za'a zuba masa ruwan a kasa da tsaf zai kafa bakinsa ya shanye.

Bai samu daukar babies din ba har saida aka zo za'a gyara Aisha dole ta bashi su ya rike. Kallonsu yake amma ya rasa dawa suke kama, sun dauko best features of Aisha sun kuma dauko best features of Nura, dan haka sai suka fi su kyau, dan shi badan a gabansa aka haifesu ba ba zai yarda cewa 'ya'yansu bane ba, kyawawa ne sosai, farare tas kamar ba Aisha ce ta haife su ba, kamarsu daya kamar an tsaga kara dan badan tag din da midwife din ta saka musu a hannayensu ba da ba zai iya gane wannene Hassan wannene Hussain ba.

Bayan an gama shirya Aisha ne aka yi mata allurar bacci dan ta samu ta huta, sannan aka karbi babies din aka shirya su suma cikin kayan sanyi ash colour daya mai adon light blue daya kuma dark blue. Nura ya karbe su ya jera su a gaban Aisha da take ta bacci ya dauke su a hoto. Hoton yayi kyau sosai, sai Nura yaga kamar ma Aisha kara kyau tayi yau din duk da wahalar da tasha. Ya sunkoya yayi mata kiss a lips dinta, ta dan bude ido cikin bacci ta kalle tayi masa murmushi cikin magagin bacci tace "Hubby" yace "yes Wifey, ya jikin?" Ta kalli babies din gabanta tace "ka gansu masu kyau kamarka ko?" Ya lakuce mata hanci yace "kin fisu kyau ai. Now go back to sleep".

Sai da Nura ya gama cike ciken takardun asibiti sannan ya zauna ya dauki wayarsa ya kira Nigeria. Sanda ya gama wayar kasa tantancewa yayi waye yafi murna tsakanin Aunty da Inna, dan duk su biyun cewa sukayi lallai tahowa zasuyi. "wannan wacce irin haihuwace ko labarin ciki bamu dashi sai dai muji labarin haihuwa? Kuma mazaje har biyu sannan ace ba zan zo in gansu ba?" Inji aunty muryarta cike da farin ciki marar misaltuwa, yace "ayi mana afuwa, insha Allah dana samu hutun karshen shekara zamu taho gaba daya. Kinga kafin nan sunyi arba'in sun danyi kwari" Aunty dai ba'a son ranta ba, tace "ni dai da nasan da cikin nan ai da tuni nace ta taho gida ta haihu a gaban mu, yanzu waye zaiyi mata wankan jego kuma? Ga 'ya'ya har biyu a garin da baku san kowa ba?" murmushi kawai Nura yayi dan yasan cewa Aisha is very capable of kula da kanta da yaranta ko da kuwa ace babu taimakon sa, ballantana shima wannan experience din babu abinda zai wuce shi, dan tun kafin haihuwar har videos yayi downloading na yadda ake kula da babies, yi musu wanka, saka musu kaya, bottle feeding, chanza musu diapers da sauran su.

Aisha_HumairahTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon