Family

8.7K 817 37
                                    

Tafiya kawai Al'ameen yake yi  amma baisan inda yake jefa kafarsa ba. Zai iya cewa tunda yazo duniya bai taba fuskantar wani abu makamancin wannan ba. Bayi, dogarai da ma'aikatan gidan suna ta kawo masa gaisuwa amma bai masan suna yi ba har sai da yasa kafarsa a farfajiyar gidan. Ya daga fuskarsa sama yana jin  fresh air tana dukan fuskar tasa, a hankali ya sauke doguwar ajjiyar zuciya sannan ya bude idonsa yana karewa inda yake tsaye kallo. Sannan ya taka a hankali ya tafi inda motar da yazo da ita take. Ya tayar da ita, ya dau hanyar komawa gida sai kuma ya dauke kan motar zuwa gefe yayi packing. Ya fito ya hau saman motar ya kwanta rigingine ya yi pillow da hannayensa ya rufe idonsa. That was his favorite position na yin tunani.

Sosai, ya fahimci maganar da Takawa ya gaya masa, ya fahimci tarkon daya dana masa. Zabi ya ba shi amma zabin dauki inga hankalinka ne. Ba zabi ya bashi tsakanin crown da Humairah ba, a'a, zabi ya bashi tsakanin Humairah da Family. In har ya zabi Humairah to Takawa ya samu hujja akan sa cewa ya zabi mace akan all what his family stands for. And then, in ya fito fili ya zabi Humairah his parents will be disappointed in him, very disappointed. Tunda suka haife shi training din da suke yi masa kenan, to be the crown Prince of Abuja, to one day sit on the throne. Idan ya zabi Humairah tamkar ya debi kasa ne ya watsa a idon mahaifansa, and that is something he will never do. In ya zabi Humairah the crown will be taken from him and be given to one of his brothers, but who? Bassam? Daga iyayensu har sauran dangi sunsan cewa Bassam ba zai iya ba, saboda shi Bassam dan a shana ne aji dadin rayuwa, sau da yawa yana cewa wai shi tausayin Al'ameen din yakeyi yana kuma murna daya kasance bashi ne Al'ameen din ba, danshi sarauta haihuwarsa tayi amma ko a jikinsa baya jinta. Ko kuma Abdallah? His physically challenged brother? In ya zabi Humairah tabbas yaso kansa da yawa, shi kadai ne zaiyi benefiting tunda ita kanta yarinyar ba wai sonsa take ba. Zai bata goma ne ba tare daya gyara daya ba. Amma kuma zai iya? Anya zai iya rayuwa babu Humairah kuwa? Daga inda yake yana hango quarters din bayi, suna ta harkokinsu, sai kawai yaji yana envying dinsu, sune bayi but at least they are free to choose wanda suke so su aura among themselves.

Sai da rana ta tarar da inda yake sannan ya tashi ya koma mota ya karasa gida. Yana packing Bassam yana fitowa daga gidan, daga dukkan alamu makaranta zai tafi. Tun daga yanayin fitowar Al'ameen daga mota Bassam ya san babu lafiya. Ya karaso kusa dashi da sauri yace "Ya Ameen lafiya? Are you ill?" Al'ameen yayi masa kallo daya ya wuce shi, sai kuma ya juyo ya dan bubbuga kafadarsa yace "well-done Bassam, aikinka yayi kyau kayi kokari" ya juya ya cigaba da tafiya, Bassam ya kuma tarar gabansa yace "Ya Ameen daga ina kake wai? Me ya same ka?" Al'ameen ya dan yi masa karamin murmushi yace "inda kaje kakai karata, daga can nake. Kuma ina yi maka albishir da cewa kaci nasara,  congratulation" Bassam ya fara gane inda maganar ta dosa dan haka sai ya fara kokarin kare kansa "Ya Ameen komai nayi dan kai nayi shi. Yarinyar nan bata dace da kai ba. Bata dace da future sarkin mu ba" Al'ameen yace "thanks to you, am no longer the future king, you are. Congratulations, enjoy the crown" ya tafi ya bar Bassam da sakakken baki.

Sam bai san maganar zata yi zafi har haka ba, shi tunani yake daga manya sunyi wa Al'ameen magana shi kenan maganar zata wuce. Da sauri yabi bayan Al'ameen din amma kafin ya tarar dashi har ya shiga dakinsa ya rufo kofa.

Ranar Al',ameen bai fito lunch ba, amma ba wanda ya damu saboda a dokar gidan zaka iya missing lunch, dinner ce dai ba'a missing. Amma da lokacin dinner din yazo shima sai ya zama kujerar Al'ameen empty ce. Nan fa Mami ta fara kiransa a waya but all his phones were switched off. Amma sai taga Daddy kamar bai damu ba, ta turo Bassam ya dubo ko motocin gidan babu wata amma sai ya tarar duk sunanan, hakan ya tabbatar mata da cewa yana gidan kenan, nan take ta aika Abdallah dakinsa yaje ya kirawo shi. Yayi knocking har sau uku babu amsa, sai ya gwada murda handle din ga mamakinsa sai yaga kofar ta bude. Duhu ne ya bakunci idanuwansa, fitila a kashe take kuma curtains gabadaya a rufe suke. Ya lalubi switch ya kunna, take haske ya gauraye dakin ya bayyanar masa da Al'ameen kwance a kan gado yayi rigingine kafafuwansa a kasa, idanuwansa a bude kuma tar a kan fuskar Abdallah, babu alamar bacci ko digo a cikinsu. Nan take Abdallah ya duburburce kafin yayi bayanin me ya kawo shi Al'ameen ya mike tsaye ya fara zazzaga masa masifar me ya kawoshi dakinsa? Daga alama ya manta cewa Abdallah ba ji yake ba, haka ya tunkudo Abdallah waje ya banko kofarsa harda saka key.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now