The Prostitude

7.3K 712 26
                                    

"Ya bude min kofar side dinsa na shiga na zauna ina jin dadin laushin seat din da sanyin ACn.  Na gaji sosai. Ya dube ni yace "you look terrible. Daga ina kike haka? Ina kuma zaki je da baby a hannu?" da farko kamar bazan gaya masa ba saboda ina jin tsoron kar ya kai ni gurin 'yan sanda amma daga baya sai na gaya masa.  Taimako nake nema ido rufe a lokacin.  Kuma ya taimaka min,  bai kaini gurin 'yan sanda ba sai ya kaini masaukinsa,  hotel,  ya sanar dani cewa wani aiki ne ya kawo shi dutse, zai dan kwana biyu kafin ya tafi.

Ranar sam banyi bacci ba,  dana rufe idona Kamal nake gani, gani nake kamar zaiyi fatalwa yazo ya kamani cikin dare. Da safe Dr zai fita na roke shi dan Allah ya bincika min maganar Kamal, maybe ma bai mutu ba. Kafin ya fita yayi mana order abinci har na rana. Sanda ya dawo ya tarar dani kamar tababbiya saboda tashin hankali, ko kwakwkwaran motsi naji sai in tsorata in dauka zuwa akayi za'a tafi dani, in naga inuwa kuma sai inyi tunanin fatalwar Kamal ce, ga Humairah ta dasa min rigima tana neman babanta,  dama ya sabar mata kullum suna tare. Dr yana zuwa na tambaye shi abinda ake ciki sai ya cemin yaje har gidan ya tarar ana zaman makoki, yace an baza police ko ina an rarraba musu hotuna na suna ta nema na.

I cried, I cried for myself and for my daughter, nasan wannan farkon wahalar rayuwar mu ne. Amma sai Dr ya saka ni a gaba da rarrashi, ya nuna min cewa ba farkon wahala ta bane ba karshen ta ne, yayi min alkawarin in ya gama abinda yakeyi tare zamu zo Abuja, zan zauna a hannunshi inyi takaba sannan sai muyi aure a can, shi zaiyi amfani da dukiyar sa ya kashe maganar Kamal shikenan sai in cigaba da normal rayuwata.

Na tuna masa da abinda yayi min a baya, yayi min alkawarin aure amma ya yaudare ni ya cimma burinsa ya gudu ya barni. Sai yace ai lokacin ya ki dawowa ne saboda yasan bayan abinda ya faru tsakanin mu ba lallai bane iyaye na su ba shi ni, amma yanzu sai munyi auren ma zamuje gida dan haka babu yadda za'ayi damu. Duk da cewa Dr yana da shekaru amma yana da kudi,  wayewa da kuma kyau, dan haka sai naji tamkar faduwa ce tazo dai dai da zama. Na saki jiki dashi. Na yarda da duk karyayyakin da ya shirya min.  Saboda ni wawiya ce. Ni doluwa ce. Ni sakarai ce. Ni dakikiya ce. Ya ja Humairah a jikinsa ya siya mana kayan sakawa da kayan bukatu wanda zasu ishe mu kafin ya gama mu tafi Abuja. Hmmm. Wai ni zan tafi Abuja, wai ni zan auri minister. Dan haka na zage nayi ta bashi duk abinda yake so shi kuma yana karba. Ina tsoron kar in ki yace ya fasa. Ai aure zamuyi.

Sai dana kwana goma chif a dakinsa,  ko kofar daki ban taba fitowa ba saboda tsoron kar a kamani. Ranar nan tun ina bacci ya fita, sai daga baya ya kira ni a waya yake cemin ya fita emergency kira amma zai dawo in an jima. Bai dawo ba. Hankali na ya fara tashi na kira wayarsa kuma a kashe. A zuciyata nasan ya gudu ya barni, again, amma kuma naki yarda. Cikin fargaba na tashi na duba inda yake ajiye kayansa na ga wayam. Nasan ta faru ta kare anyi wa mai dami daya sata. Kuma dan wulakanci bai ajiye min ko nera daya ba"

Na zauna na saka Humairah a gaba ina kuka itama tana tayani, na tashi na hada mana 'yan kayayyakin da ya siya mana a leda tunda dama a leda ya kawo mana ko matsayin jaka bamu samu ba ballantana akwati. Na zauna ina jiran dare yayi in fita dan ina tsorin fita da haske dan kar a kamani. Kuma nasan dare yanayi masu hotel din zamu zo su fatattake ni.

Bayan Magrib kawai sai ga wani yazo wai yana nemana,  wai Dr ne ya turo shi yace ya bani hakuri ya gaya min cewa kiran gaggawa akayi masa shi yasa ya tafi Abuja ya barni, bai tafi dani ba saboda bai gama shirin zuwana ba,  amma in yaje yanzu zai nema mini gida sannan ya gayawa iyalinsa labari na sannan ya aiko a dauke ni. Ni kaina nasan karya yake yi,  ta ya za'ayi mutum mai kudi kamarsa yace zai je ya nemi gida? Gida je nawa yake dasu? In ma babu gidan ba sai ya ajiye ni a hotel ba? Ko ya kama min rent?

Dan sakon ya kara da cewa, wai Dr yace ya dauke ni daga nan,  tunda bai kamata ya barni a hotel ba, ya kaini gidan wata 'yar uwarsa in cigaba da zama a gidan har sai ya kammala shirinsa sai yazo ya daukeni. Babu yadda zanyi saboda in ban bishi din ba babu inda zanje, ko kuɗin motar da zai fita da ni daga garin bani da su. Haka muka shiga mota muka tafi. Na ga yana shirin barin gari na tambayeshi yace ai dama matar ba'a garin take ba. Nasan cewa something was wrong. Amma ban san cewa wannan was the beginning of wata irin muguwar rayuwa for me ba."

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now