The Prostitute 2

8.2K 742 20
                                    

Wajen gidan na fita na tsara ina kallon yadda kowa yake harkokinsa, na lura unguwar gabadayanta ba unguwar mutanen kirki bace ba saboda duk inda na kalla sai inga daga masu shaye-shaye sai 'yan daudu masu siyar da abinci sai matan da kallo daya zaka musu ka fahimci karuwai ne. Banga wata mace mai hijabi ko wani namiji mai hula a kansa ba. Wa zai taimaka min da kudin dazan siyawa yarinyata abinci? Nima kaina yunwar nake ji. Na hango wata mata tana ta suyar wainar shinkafa, babbar macece amma daga ganinta tsohuwar 'yar bariki ce. Irin jibga jibgan matan nan da tashi ma da kyar suke yi. Na karasa gurinta na gaisheta ta amsa ba tare data kalleni ba, na durkusa a gefe nace "dan Allah ko zan iya samun bashin abinci muci nida yarinyata? Inna samu kudi insha Allahu zan biya ki" ta watso min harara da niyyar aiko min da zagi amma sai naga ta fasa tana kallona tace "sabuwar yarinyar Ladi ce ai" na bata rai nace "ni ba yarinyar ta bace ba" tayi dariya tace "in dai har kina gidanta ke yarinyarta ce, wannan kyan naki sai ta tsotse shi tas ta tabbatar baki da mamora sannan zata rabu dake" ta kalli Humairah tace "me ya kaiki shigowa bariki da karamar yarinya irin wannan?" nace "ni ba bariki na shigo ba, ni ba karuwa bace ba" ta dauke kanta ta cigaba da aiyukanta sannan tace

"kowa da haka ya fara. Kowa kika tambaya ƙalilan ne suka fito daga gidajensu da niyyar karuwanci. Yawancin mu laifi mukayi a gida muka gudu muna neman mafaka, waɗansu auren dole akayi musu suka yi tunanin gwara su shiga duniya, waɗansu kuma rashin gata ne yasa suka fara zaman kansu, wadansu mummunar ƙaddara ce ta faɗa musu, amma duk mun hada abu ɗaya, duk muna buƙatar abincin da zamu saka a cikkunan mu, duk muna buƙatar shimfiɗar da zamu dora kafaɗun mu, muna kuma buƙatar kayan da zamu saka a jikin mu. Babu kuma wanda zai taimaka mana da wannan, ita duniya da kike ganinta yanzu kowa kansa yasani, ko a tsakanin ƴan uwa ma ba taimakon juna ake ba ballantana bare. To ya zamuyi? Dole mu siyar da abinda muke dashi dan mu rayu. Amma rayuwar mu ba irin ta sauran mutane bace ba, rayuwar mu rayuwace mai chike da wulaƙanci, ƙaskanci da tozarci. Daga randa kika shigo bariki to duk wata daraja taki ta ƴa mace kin zubar da ita, babu wanda zai kuma kallonki da mutunci. Da ace matan da suke gidajensu sunsan ko menene a cikin bariki da ko me zasuyi a gida, ko me za'ayi musu, da ba zasu baro gidajensu ba. Amma baka sanin menene a cikinta har sai ka shige ta, in kuma ka shige ta shikenan ka gama da rayuwar 'yanci. Ka ɗigawa kanka tambarin da har abada ba zai gogu ba. Tambarin Karuwa."

Ta juyo tana kallona cikin ido tace "tun kafin lokaci ya kure miki gwara kisan inda dare yayi miki" cikin sanyin jiki nace "Ladi ba zata barni in tafi ba, tace sai na biya ta kudaden da take bina" bata kuma cewa komai ba ta cigaba da kula da customers dinta, duk wanda aka zubawa abinci sai Humairah ta bishi da kallo tana miƙa hannu tana gwarancin a bata taci. Naga abincin yana neman ƙarewa na ce "wallahi zan biya ki, dan Allah ki bani" tayi min kallon wulaƙanci kamar ba ita ta gama min nasiha yanzu ba tace "baki gama biyan Ladi nata bashin ba zaki karbi nawa? Dame zaki biya ni? Nayi shiru dan nasan bani da komai, tace "sai dai ki bani jinginar wani abu. In kin biya ni kudina in baki kayanki, in baki biyani ba kuma abin ya zama nawa" haka na tashi da sauri na koma dakina ina neman abinda zan bata. Na dauko wata doguwar riga a cikin kayan da Dr ya siya min sanda muna hotel na taho da sauri na kawo mata, da sauri ta warce ta cusa a cikin baccon kayanta da take gefe sannan ta zuba min waina da miya har da nama.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar min har tsahon sati daya. Kullum da daddare sai Ladi ta aiko min namiji ɗakina ya kwana dani, haka suke zuwa min babu kyautatawa babu lallabawa sai nuna zalinci da mugunta da fin ƙarfi, ai kuɗinsu suka biya suka siya. A cikin satin nan gabaɗaya na fita hayyacina, nayi kuka tamkar idanuwana zasu tsiyaye, nayi nadamar barin gida yafi cikin charbi bansan cewa nadama tana gaba ba. Kullum ina karbar abinci sau biyu a gurin Jummai mai waina. A ranar da sati ya cika ne naje da safe da niyyar karɓar abinci sai ta watsa min harara tace "Sai dai ki kawo wani abun kuma, kudin rigarki sun kare" Naji kamar in fashe da kuka, to ni mai zan bata yanzu? Dama kayan set uku yasiya min kuma na bata daya sauran biyun su nake samu nake sakawa, inna bata kuma yaya zanyi? Tsirara zan zauna ko kuwa? Na koma daki na gama dube dube na na rasa abin dauka, sai na dauko pillow guda daya na fito na kawo mata, ta karba tana jan tsaki haɗe da ƙunƙuni irin ba haka taso ɗin nan ba amma dai ta zuba min abincin na koma daki. Na saka wa Humairah a gaba tana ci ni kuma na zuba tagumi ina kallonta ina tunanin menene mafita? Na farko in nace zan gudu ma ina zani? In ina da gurin gudun ma kuma ina naga kudi? Da ace ma ni kadai ce babu Humairah da abin sai yafi zuwa min da sauki.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now