Loneliness

9.1K 842 41
                                    

The day had been a bad day for him so far. Tun sanda ya tashi daga bacci ya shiga toilet da niyyar yin wanka, yana kunna shower yaji ruwan sanyi ya zubo masa, da sauri ya kashe. Ya duba yaga ashe water heater ba ta yi, ya kunna fitila ita ma yaga bata kama ba. Yaja dogon tsaki dan yasan abinda ya faru. Power units dinsa ne ya kare. Ya kuma yin tsaki yana jin duk ransa ya baci. Wai me yasa abin nan baya yiwa mutum alarm ne in ya kusa karewa? Wani barin na zuciyarsa ya gaya masa 'da kana da mata ai da ta taya ka dubawa' yayi saurin kawar da maganar daga ransa. Dole haka ya kwakwkwara ruwan sanyin ya fito yana karkarwa. Da sauri ya shirya, har zai fita ya juyo ya kalli bedroom din nasa, kaca-kaca. Ya kalli agogon hannunsa yaga already ya makara.

Da dan saurinsa ya shiga kitchen ya jawo kettle da niyyar dafa tea sannan ya tuna bashi da wuta, ya kara buga wani tsakin ya ture kettle din ya fice. Mota kawai ya shiga mai gadi ya bude masa gate ya fita, yana tunanin ya tsaya a wani gurin yayi breakfast ko kuma ya zarce office kawai yayi order daga can? Ya duba agogon hannunsa yaga 8:30, yana da lecture da students by 9 dan haka dole ya hakura da cin abincin. Amma sai me? Baiyi nisa da gidan ba motar shi ta fara misbehaving sannan ta mutu, yayi cursing under his breath sannan ya buga steering da hannunsa. Sai kuma ya mayar da kansa ya kwantar a jikin kujera ya lumshe idonsa yana tunanin rayuwarsa. It is a total mess. Mutane suna ganin tamkar bai damu da rashin aurensa ba amma shi yafi kowa damuwa. Musamman yanzu da shekaru suka ja masa. He is tired of being alone. He felt so lonely kullum. In yana gida he is alone, in ya zo office ma dai alone yake zama.

Tun farkon rayuwarsa bashi da friends, babban friend dinsa shine Takawa. Shine babansa shine abokinsa shine role model dinsa, tare suke zuwa ko'ina tare suke yin komai. Life had been so good then, but then lokaci daya everything ya tarwatse. Komai ya lalace. Rana daya babansa ya juya masa baya ba tare da yasan dalili ba, sannan daga baya rana daya aka kirashi aka bashi wata tatsuniya cewa babansa ba shine babansa ba. Cewa shi din ba dan sunna bane ba, dan gaba da fatiha ne, shege ne.

He can't even begin to describe the feeling. Babu wanda zai gane sai wanda ya shiga ko yake cikin situation irin nasa. Badan zuciyar musulunci ba da babu abinda zai hana shi daukan ransa a lokacin. Yaji ya tsani kansa, ya tsani rayuwarsa and most importantly ya tsani mahaifiyarsa. Gani yayi itace silar komai. Dan haka ya yanke duk wata alaka da ita kamar yadda Takawa ya yanke duk wata alaka da shi. Step brother dinsa da da yake yiwa kallon kaskantacce wanda ba zai zama komai a rayuwa ba shi ne ya dauke shi ya mayar dashi gidansa ya zaunar dashi ya bashi shawarwari masu kyau sannan ya mayar dashi makaranta, makarantar da da baiyi ba saboda yana ganin yin nata bashi da amfani.

Tun daga lokacin ya dukufa karatu, mostly saboda ya mantar da kansa halin da yake ciki. Amma hakan ya gagara. He became bitter. Kullum cikin kunci kullum cikin fada da mutane saboda yana ganin kamar kowa daya kalleshi zai ga sunan shege a rubuce a goshinsa. A haka har ya gama first and second degrees dinsa sannan yayansa wanda zuwa lokacin ya zama daya daga cikin wadanda ake ji dasu a Abuja ya nema masa aiki anan university din da yayi karatu, with his name and the backing of his brother bai sha wahala ba ya samu aikin. Then he decided to move out of the palace. So yake yayi nesa da duk abinda ya shafi sarauta, maybe ko hakan zai rage zafin da yake ji a zuciyarsa a duk lokacin da yaga babansa da ba ubansa ba, so yake ya sake sabuwar rayuwa as the bastard that he is. Still wannan brother din nasa daya raina a baya shine ya gina masa gida kyauta ya bashi bayan yayi iya kokarinsa na ganin ya hana shi tafiya ya kasa, amma da yaje yiwa Takawa sallama ya gaya masa kudurinsa na barin palace sai cewa yayi "to" kawai.

Shi kuma wannan ya sashi ya kara zuciya da duk abinda ya shafi gidan, hatta motocinsa da yake hawa sai ya ajiye keys dinsu ya rataya jakarsa ya fice ba tare da waige ba. Shin dama soyayya a jini take kawai? Shin dama dan da ka rike tun yana jariri har zuwa girmansa bai zama danka ba? Ina shakuwar take ina kuma soyayyar take?

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now