Facing the Challenges

8.5K 969 50
                                    


Automatically hannun Al'ameen ya kamo na Humairah ya rike, bata hana shiba saboda rike hannun nata da yayi ya kara mata karfin gwuiwa da kuma assurance cewa yana tare da ita. Daddy ya karaso yana karewa fuskokinsu kallo ya sake maimaita tambayar da yayi "menene yake faruwa anan?"

Bassam ya karbe hannunsa daga rikon da Al'ameen yayi masa sannan yayi taku biyu baya yana sunkuyar da kansa, jin babu amsa daga samarin nasa ya saka Daddy ya maida kallonsa kan Humairah, ya gane ta, wannan yarinyar ce da Aisha ta dauko daga orphanage din sa. Yayi noticing yadda ta rike rigar Al'ameen da kuma yadda ilahirin jikinta yake rawa, babban abinda ya fahimta a gurin shine a tsorace take, sai dai bai san tsoron me take ji ba amma ya fahimci tana ganin Al'ameen ne kariyar ta daga abin tsoron na ta. Kafin ya sake magana   Mami ta riga shi. Tace tana kallon hannun Al'ameen wanda ya rike na Humairah dashi "sake ta" babu musu ya saki hannun yana jin zuciyarsa tana kara nauyi. Sannan tace da Humairah itama "kema sake shi" a hankali Humairah ta chika rigar Al'ameen, sannan Mami tace "wuce ki tafi daki" bata bukatar a sake mata magana, da sauri sauri tayi part din Mami, tana shiga daki ta kifa cikinta akan gado ta fara rera kuka mai tsuma zuciya. Ansha zaginta a baya, ansha ci mata mutunci fiye da abinda bassam yayi mata, amma me yasa take jin na Bassam din kamar yafi na kowa zafi? Aunty Aisha tayi gaskiya, aurenta da Al'ameen ba zai yiwu ba, in ma ya yiwu to ba mai dorewa bane ba tunda gashi tun yau an fara tambayarta waye ubanta? Ta mike zaune tana share hawayenta da bayan hannunta, waye ubanta? Itama bata sani ba. Bata san koda sunansa ba, bata san ko yana raye ko ya mutu ba, bata san ma ko ya san da ita ko bai san da ita ba. Taji zuciyarta ta kara karyewa, waya sani ma ko ita kanta mamannata bata san waye babanta ba? Ta rufe fuskarta tana sake sabon kuka, wannan karon amma ba kukan zagin da Bassam yayi mata bane, wannan karon kukan tausayin kanta ne. Kukan tausayin rayuwarta ne.

A Palo kuma, Mami ta na ganin shigar Humairah daki itama ta juya ta koma kitchen. Ta kori Humairah daga gurin ne saboda koma wanne hukunci Daddy zai yanke bata so yayi a gaban Humairah because she is not part of the family. This is a family crises and it is suppose to be a family matter.

Raising the children had been hard on her. Al'ameen akwai taurin kai amma baya shiga mutane ma ballantana har ayi rigima dashi, dan haka ba zata iya cewa ga abokin fadan Al'ameen ba. But Bassam, Bassam have inherited zafin zuciyar babansu, tun suna primary in dai aka kawo complain daga school to Bassam ne. Bassam har da abokan Al'ameen fada yakeyi sai yace wai yaga suna yiwa Al'ameen din wani gani gani basa bashi respect din daya dace. Al'ameen ne babba, amma Bassam gani yake kamar Al'ameen din is too soft dan haka shi shine mai kula dasu.

Wannan ne ma yasa Daddy bai fita dashi kasar waje yayi karatu ba kamar yadda ya fitar da Al'ameen, yace gwara ya zauna anan a gabansu yayi karatun suna kallonsa, maybe in zaiyi masters sai ya fita din, if ya kara hankali kafin nan. That was exactly what happened with Humairah. Shi Bassam a ganinsa he was looking out for his brother, tunda yana tunanin Humairah zata cutar da dan uwansa ne. 

Tana jinsu suna tsarawa, Bassam raising his voice, Al'ameen kuma baya magana sai an tambayeshi, a gabanta komai ya faru amma bata son shiga maganar, bata son radar ra'ayinta saboda ra'ayin nata ba lallai ne ya zama shine choice mai kyau ba, gwara tayi shiru, gwara tayi addu'a. Tana jin Daddy ya fara fada at the top of his lungs  but she did not intervene, ta yadda da mai gidanta, tasan zai yankewa kowa hukunci dai dai da laifinsa.

"Daddy yawo take tana fada wa mutane wai yace zai aureta, she is ruining the reputation of this house"

"Kai Al'ameen karya take maka?"

"Ba karya tayi ba Daddy"

"Daddy kaji fa, that girl is a witch, aure fa yake cewa"

"to ina ruwanka? Kai yace zai aurawa ita ko kuma kaine kake da ikon daura masa aure?"

Aisha_HumairahTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang