The Friends

10.3K 793 38
                                    


A palo ta tarar da Basma tana kwance tana chatting a wayarta, ta dago kai ta bita da kallo tace "daga ina kike ke kuma?" Bata amsa mata ba sai ta karaso ta ajiye plate din hannunta a gaban Basman sannan ta zauna ita ma ta dauki tea din ta fara sha, wani dadi taji, so refreshing ta lumshe idonta tana shakar kamshin tean. Basma ta mike zaune ta dauki kosan ta saka a bakinta tace "waya baki wannan" Humairah tace "ni na soya" Basma tace "what? Wai kina so kice min tun dazu kina kitchen tare da Ya Ameen? Ni tun da naga ya tafi kitchen din na dauka kin fita kin koma daki ko wani gurin. Tell me the truth, waye yayi wannan girkin?" Humairah tace "Ya Ameen ne yayi"

Basma ta bude ido, "wai kina nufin Ya Ameen ne da kansa yayi wannan abincin?" Humairah tace "a'a bashi ne yayi ba nice nayi" Basma ta harde hannayenta a kirjinta tace "wanne zan dauka a ciki, ke kikayi ko shine yayi?" Humairah ta danyi karamin murmushi tace "tare mukayi ni da shi" Basma tace "wait, what?" Mamaki karara a fuskarta. Humairah ta ajiye cup din hannunta tace "kinga, shi fa yana zaune, kawai gaya min abinda zanyi yake yi ni kuma ina yi, a haka har muka gama" Basma ta dan dake ta a kafada tace "that's my girl, you really made me proud tunda har kika iya zama dashi a kitchen daya" Humairah tayi murmushi kawai amma tana jinjina maganar a ranta, ya akayi ta iya zama daga ita sai shi har lokaci mai tsaho? Ya akayi kuma ko a ranta bata yi wani negative tunani ba ballantana taji tsoronsa? Ita ma bata san amsar ba amma tasan it has to do with yadda yake komai nasa a nutse, maganar sa a hankali cikin nutsuwa, haka movements dinsa, kuma da yadda yayi keeping distance between them dan tun da suka fara bai zo kusa da ita ba, in zata bashi abu ko zai bata bai taba bari hannayensu sun hadu ba. Ga kamshin turarensa mai sanyaya zuciya.

Shima Al"Ameen a nasa bangaren bayan yaje daki yana cin abinci kawai sai yaji abincin yayi masa dadi fiye da yadda yake yi masa ada. Mamakin ya akayi yayi enjoying his time with her yakeyi, ya dauka mu'amala da ita will be the most boring and annoying thing da zai taba yi a rayuwarsa amma sai yaga ba haka bane ba. Komai ya tafi smoothly ba tayi masa ihu ba ko wata hayaniya, she might be young and naive but she is very brilliant, kwakwalwarta tana ja sosai da sosai, dan duk abinda yake gaya mata tana yi ne exactly kamar yadda yace mata. Ya kalli gurin da suka sha kokawa rannan sai ya samu kansa da murmushi.

Kwana biyu haka ta cigaba da kasancewa, kullum Al'ameen in yana bukatar abu to Humairah yake sakawa, tun tana jin babu dadi har ta fara sabawa da taga yazo zata tashi ta dauko masa drinks tazo ta zuba masa ta mika masa, a hankali ta fara gane wanne drink yake so wanne ne kuma baya so. In abinci zai ci ma ita take zuba masa. Amma har yanzu dai baya baya take yi dashi, bata taba zuwa kusa dashi sosai kuma shima baya zama kusa da ita, daga baya baya dai.

Ya fahimci cewa the rules of zama lafiya da Humairah sune; kar ka yi mata tsawa, kar ka je kusa da ita, and never ever try to touch her. Ya kuma lura cewa, she is very religious, zai iya cewa bai taba ganinta babu mayafi ko hijab ba saboda she is very conscious of her body, in mayafi ne a jikinta daya shigo gurin zata fara gyara shi tana kara rufe jikinta, wani lokacin ma tashi take yi ta dauko hijab ta saka, ta riga ta saka a ranta cewa kowanne namiji kallonta yake yi.

Most of the times in bashi da aiki a office kawai sai ya dauko mota ya dawo gida dan yasan zai tarar da gidan babu kowa sai Humairah da Basma, nan zai zauna tare dasu yayi ta kokarin yi musu hira duk da ba iyawa yayi ba amma with Basma nothing is boring dan inta debo wani labarin sai ya dakatar da ita saboda yasan ba zai kare ba. Kokarinsa shine yaga Humairah ta basu wani labarin itama, something related to her past amma ko sau daya bata taba gwadawa ba. Shi kuma baya son ya tambayeta saboda kar tayi tunanin bugun cikinta yake so yayi.

Ranar nan ya dawo daga office da wuri kamar yadda ya tsira kwanan nan, amma yau ya taho da aikin wasu takardu daya ke so ya cike kafin gobe. Maimakon ya tafi part dinsa yayi aikin acan kawai sai ya samu kansa da zama a dining, part of him wants to do the work and the other part yana son zuwa suyi hira da humairah. Ya zauna dai ya fara aikin kamar gaske sai kuma ya kira wata a cikin yaran gidan ya aike ta ta kira masa Humairah, sai bayan 'yar aiken ta tafi kuma sai ya fara tambayar kansa mai yasa ya aika ayi kiranta? Me zata yi masa in tazo? Bata jima ba sai gata, ta tsaya daga dan nesa tayi masa sallama ya amsa ba tare daya dago ba, ta cigaba da tsaiwa a gurin sannan ya dago yayi mata kallo daya. Doguwar riga ce dark green a jikinta mai adon stones a kirji da hannayenta. Ta daura veil din rigar a kanta a matsayin dan kwali sai kuma tayi rolling farin mayafi, fuskarta fes babu kwalliya. Sai kawai yaji yana so yacigaba da kallonta.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now