One Family

8.6K 784 31
                                    

Washegari, kamar yadda Abbas ya yi wa Al'ameen alkawari haka yayi, yana tashi daga gurin aikinsa direct ya zarce palace gurin takawa. Kamar kullum cikin 'yan watannin nan, a zaune ya same shi a palonsa na ciki inda nan ne gurin zamansa kullum, nan ne inda yake ganawa da duk wani bako makusancinsa sai dai in bakon wanda ba za'a iya shigowa dashi ciki ba kuma babban mutum ne wanda ba zai ki ganinsa ba sai ya fito palon waje ya ganshi, amma zuwa fada kam sam ya daina ya barwa tilon dansa, Sultan.

Abbas ya durkusa ya gaishe shi cikin ladabi da biyayyar da akayi masa tarbiyya da ita tun jarirantakarsa, kuma for the first time shima yau sai yaga ya samu fuska mai kyau a gurin marikin nasa, daga dukkan alamu yau sarki Sadiq raha yake ji dan haka cikin sauki ya gabatar masa da sakon Al'ameen. Sarki Sadiq ya tashi zaune daga kashingiden da yake ya harde kafafuwansa yana kallon Abbas yace "kira min shi kace yazo yanzu" da sauri Abbas ya dauko yawarsa yayi magana urgently da Al'ameen sannan ya kashe yace "gashi nan zai karaso yanzu" sai kuma suka yi shiru, kan Abbas a kasa yayin da sarki Sadiq ya ware idanuwansa a kansa yana studying dinsa, he clearly looked disturbed kamar wani abun yana damunsa.

Yace "kai kuma fa?" Abbas ya dago kansa yace "na'am?" sarki Sadiq yace "kai kuma yaushe zakayi aure?" Abbas ya danyi murmushi wanda bai kai ciki ba amma baice komai ba, yana tuno da wayar da sukayi da likitan babansa dazu da safe inda yake tabbatar masa da cewa lung cancer ce take damun baban nasa. Sarki Sadiq yace cikin hade rai "ya kamata kasan me kake ciki hakanan, you are no longer young and you are not getting any younger. So kake in tsufa ya kamaka ka kasance kai kadai a gidanka babu mai taimaka maka?" Abbas ya tuno da yadda mahaifinsa yake zaune shi kadai a gidansa kamar maye, he definitely don't want to end up like his father. Yace "za'ayi, Allah ya taimaki sarki, very soon insha Allah" yace "good for you. Cikar mutum shine ya zama yana da iyali, aure kuma shine cikon addini".

A lokacin Al'ameen ya shigo, yayi gaisuwa sannan ya koma gefe ya zauna. Takawa yace "munji sakonka a gurin kawunka, kuma munji dadi sosai Allah yayi maka albarka. Yanzu hakan baya fi maka ba? Ka kyautatawa kanka ka kuma kyautatawa zuri'ar ka? Muma ka kyautata mana" aka danyi shiru sannan yace "ita wannan din a ina take?" Al'ameen yace "a Yola take Allah ya taimaki sarki" yace "to sai ka gaya mana sunan wani a danginta a Yola din, ko kuma sunan unguwarsu, yadda zamu samu a bincika mana asalinta sosai" Al'ameen ya shafa kansa yana tunani, dan shi kam bata taba gaya masa sunan unguwar su ba, kuma babu sunan wanda ya sani sai sunanta sai kuma few of cousins dinta da takan bawa waya su gaisa sanda take can. Amma kuma ba zaice bai sani ba dan haka yace "Kakanta, wanda ya haifi babanta sunansa Alh Usman Muhammad Gidado" Takawa yayi sauri ya kalleshi yace "Usman Muhammadu Gidado Illeja?" da sauri Al'ameen ya gyada kansa, he remembered her mentioning something like that, fuskar Takawa ta washe ya koma ya kashingida yace "ah to alhamdulillah, nasan Alhaji Gidado sosai, yana daga cikin shugabannin kungiyar fulani ta Miyatti Allah, mu kan hadu dashi a gurin tarurrukan da suka shafi harkar fulani. Family dinsu sunyi suna a garin Yola saboda rikon al'adar su da kuma yawan su. Mutumin kirki ne wanda Allah yayi wa arzikin dukiya da iyali"

Ya juyo yana kallon Al'ameen da yake gefe yana ta zuba murmushi yace "babu komai. Zamu neme shi muyi magana" ya juya kan Abbas yace "kai kuma sai ka samu yayanka ka gaya masa abinda ake ciki" daga nan yayi shiru, dan haka duk suka yi sallama suka tashi.

A waje ne Abbas ya saka Al'ameen a gaba da tsokana wai ya kasa rufe bakinsa. Suka shiga mota a tare suka tafi gidan Daddy.

A gidan Nura kuma, yau ne Kamal zai ga Sultan. Dan haka tunda safe Aisha ta kira Mami ta tambayi time din da zasu same shi agida ita kuma ta gaya mata da yamma. Dan haka yammar nayi bayan an dauko yara daga school sai suka shirya gabadayansu da niyyar zuwa gidan Mami amma sai Khadijah ta zuƙe tayi kwanciyarta a daki tace bata jin dadi. Babu wanda ya matsa mata dan duk sun san zuwan nata ba wani amfani ne dashi ba in Kamal yaje yayi godiya bisa rakiyar Aisha da Nura ma ta wadatar. Ita kuma Khadija a nata bangaren taki zuwa ne saboda she was not ready, physically and mentally, saboda tasan alakar Humairah da Al'ameen dan haka taji a ranta cewa bata shirya haduwa da su ba musamman Al'ameen dan ta san ya san ita wacece.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now