Admission

9.3K 799 7
                                    

Result ya fito, Khadija Zayyan (Aisha) ta sami 7 credit 2 passes, ita kuma Aisha Zayyan (Khadija) ta sami 1 credit a hausa, da kuma 1 pass a Islamic studies, sauran kuma duk fail ne.

Daga Umma har Abba sunyi mamakin wannan lamarin, dan duk sun san Aisha ce mai kokari ba Khadija ba, Abba yace "haka Allah yake lamarinsa, dama kuma ita SSCE sa'a ce, wanda ake saka ran zai ci bashi yake ci ba" ya juyo yana kallon A'isha yace "kiyi hakuri, wata shekarar in Allah ya kaimu sai kiyi resitting, in Allah yasa kina da rabo sai kiga kin ci" Aisha tayi shiru bata ce masa komai ba amma a zuciyarta bata so, saboda bata son ace zata cigaba da makaranta.

Khadija kuwa ranar kamar zata sume dan murna, nan da nan ta dauki waya ta fara kiran ƙawayenta tana basu labari, kowa sai da yayi mamaki tunda babu wanda yasan abinda suka yi ita da Aisha.

Da yake Abba yana da hanya a sama, bai sha wahala wajan samarwa Khadija admission a federal university, dutse ba. Amma kafin ta fara zuwa sai ya zaunar dasu ita da Aisha yace "ni a sona so nayi kuna gama secondary school in aurar daku, dan haka ke Khadija shiga makarantar nan ba wai yana nufin shikenan babu maganar aure ba, ina son a cikin samarin da suke ta yi mana zarya a gidan nan ki fitar da miji, ayi miki aurenki kina karatunki. Ke kuma Aisha kema ba zama zakiyi kuna jerawa ke da Rabi'a ba, kema miji zaki fito dashi inyi miki aure in huta, in da rabon zakiyi karatun sai kiyi a gidan mijinki"

Khadija ta turo baki tace "ni fa Abba duk masu zuwan babu wanda nake so, su kadai suke abinsu, ni babu wanda yayi min a cikin su" Abba yace "to duk wanda ba kya so ba sai ki sallame shi ba? Ni bana son neman magana. Gaba ki dayanku na baku shekara daya, lokacin da Aisha zata sake zana jarabawa ke kuma zaki shiga level 2 a lokacin nake so in aurar daku gaba ki daya".

Ita dai Aisha bata ce komai ba, amma gaba daya hankalin ta ya tashi. Suna komawa dakinsu Khadija ta fara mita "yanzu ya za'ayi ace wai aure za'a yi min, ni gaskiya tauye min rayuwa za'a yi, wanne irin aure kuma ana zaune kalau? Ni wadannan kuchakan samarin nawa babu wanda zan iya aura a cikin su".

Aisha ta saki baki tana kallonta, a ranta tace "kukan dadi kike yi Khadija, ni da babu wanda ya taba cewa yana sona ina zan iya fitar da mijin aure?" A fili kuma tace "haba Khadija, ke kuwa yanzu duk samarinki kice babu wanda zaki iya aura?" Aisha ta tabe baki tace "duk babu wanda yayi min da aure, perfect mr right nake nema" Aisha tayi murmushi tace "kar ki manta Khadija, no body is perfect, babu yadda za'ayi ki samu miji perfect tunda dai kema ai you are not perfect" sai kuma Khadija taji haushi wai Aisha tace she is not perfect, ta mike tsaye tana juyi tana girgiza jikinta tace "gaya min me na rasa a matsayina na mace? Ko da yake ke tunda bashi ne dake ba ba zaki fahimta ba, ke babu wanda ya taba cewa yana sonki ballantana ki fahimci mai maza suke so a tattare da mace. Duk hassadar mai hassada sai dai ya ganni ya kyale" daga haka ta juya ta ficewar ta.

Aisha taji zafin maganar Khadija amma in da sabo ta saba, kullum a haka suke, kullum sai Khadija ta fadi wata maganar da zata nuna wa Aishan cewa ita ba kyakykyawa bace ba.

A ranar da daddare Khadija ta fita zance, Aisha kuma tana daki ta idar da sallah ta gama karatun alqur'ani, ta nade sallayar ta fita da niyar zuwa dakin Umma, dama haka take yi kullum in Khadija ta fita zance, Abba kuma yana majalissa, sai ta tafi dakin Umma su zauna suyi ta hirar su har sai Abba ya dawo ya koro Khadijah gida sannan suje su kwanta.

Tana zuwa kofar palon Umma kafin tayi sallama sai taji maganar Ummansu "ni Aisha nake tausayawa maigida, ita ba saurayi ne da ita ba, Aisha bata taba yin saurayi ba, gashi kace mata ta fitar da miji" Abbansu yace "ai shi yasa na basu shekara daya, duk da dai nasan ba lallai ne ta samu miji a cikin shekara daya ba, bana so ne taji babu dadi ace an fara yiwa kanwarta maganar aure ita ba'ayi mata ba, amma na tabbatar sai na aurar da Khadija kafin Aisha"

Umma tace "addu'ah zamuyi ta yi musu, Allah ya fito musu dana gari gabaki dayansu, ai abin ba'a tara samarin yake ba, sai kaga ita mai samarin bata samu mijin aure ba ita wacce bata dasu ta samu" Abba ya danyi dariya yace "Rabi'a kenan, ke baki san abinda duniya take ciki ba. Ai juma'ar da zata yi kyau tun daga laraba ake gane ta, in bamu dage da addu'ar ba Aisha tare zamu tsufa da ita a gida, a karshe ma in ba Allah ne ya rufa mata asiri ba sai dai mu samu wani a dangi mu lallaba shi mu hada su" Umma tace "insha Allah zata sami miji da kanta, ai ba kyan fuska kadai ake dubawa a aure ba, har da kyan hali, kuma Aisha tana da hali mai kyau" Abba yace "a zamanin yanzu maza basu fiya duba halin ba, sunfi son macen da zasu ke jin dadi in sun kalleta, Aisha kuma bata cikin wadannan matan".

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now