Introduction

22.7K 1.2K 40
                                    

I seek for Allah's guidance in writing this book. Allah yasa ya amfani al'ummar musulmi baki daya. Allah yasa yadda na fara rubuta shi lafiya, Allah ya bani ikon gama shi lafiya Ameen.

Labarin littafin nan 'kagaggen labari ne (fiction) idan yayi kama da labarin wani ko wata to ina neman gafara, akasi aka samu amma ba dan shi ko ita nayi ba. Nayi amfani da sunayen 'yan 'uwana, amma hakan ba yana nufin labarin su bane ba.

Wannan littafin mallakata ne ni Maman Maama, ni ka dai na kirkiri labarin na kuma yi typing dinsa ni ka dai. Ban yarda wani ko wata ko wasu su dauki labarin ko wani ɓarin labarin suyi amfani dashi ta wata siga ba tare da sun nemi izini daga gare ni ba.

Kamar littafin *Maimoon*, *Aisha_Hamaira* sadaka ne ga duk wanda ya karantashi, na rubuta shine saboda in isar da wadansu sakonni zuwa ga al'ummar musulmi, duk wanda ya karanta shi ina rokon yayi min addu'ar fatan alkhairi duniya da lahira. Ban yarda wani ko wata ko wasu su siyar min da wannan littafin ba, ta hanyar bugawa ko kuma ta hanyar siyar dashi a matsayin document ba, duk wanda ya aikata daya daga cikin wadannan ya sani Allah yana kallonsa.

Duk wanda ya karanta wannan littafin ya karu da wani abu a ciki, ko kuma yaji dadi ta hanyar nishaɗi, ina rokon shi da ya yaɗa shi ta hanyar sharing ga 'yan'uwa da abokan arziki dan suma su 'karu ko kuma su nishadantu.

Ina neman afuwa ga wadanda suka fadi ra'ayinsu na kara romance akan na *Maimoon* afuwan, amma ba zan iya karawa ba saboda kada in wuce gona da iri, garin neman lada kuma in dauki alhaki.

Yawan votes, comments, da likes dinku shi zai kara min kwarin gwuiwar cigaba da muku typing, in ban samu support naku da yawa ba zan dauka cewa labarin bai samu karbuwa ba, kuma hakan zai sace min gwuiwata.

Wanda yake da complaints ko suggestion zai iya dropping a comment box, insha Allah zan duba kuma zamu samu fahimtar juna.

Babu tabbas ɗin za'ake samun update kullum. Amma zanyi iya kacin ƙoƙari na.
Na gode.

Vote and comment

Aisha_HumairahOù les histoires vivent. Découvrez maintenant