Haunted 2

7.7K 813 71
                                    


Humairah bata san komai a girki ba, a yarintarta ta san kullum siyan abinci suke yi ita da mamanta, su siya da safe da rana da daddare, rana ku kadan ne in suna da kudi suke dafa tea da kwai ko su dafa noodles su ci. Idan mamanta ta samu kudi sosai takan siyo musu kayan tea, cornflakes, goldenmorn ta ajiye musu suyi ta hadawa suna sha. Amma bata taba ganin Mamanta ta siyo danyar shinkafa ko taliya ba, bata taba ganinta a kitchen tana girki ba.

A lokacin zamansu gidan Mr Ojo kuma musamman ya samo musu cook ya ajiye musu saboda ta ringa yi musu girki, matar da jinin Humairah sam bai hadu da nata ba, sam Humairah bata son ta dan a zamanta a gidan zata iya kirga lokutan da suka yi magana. Ita ma data fahimci Humairan bata sonta sai ta daina kulata, aikinta kawai shine ta shirya musu lafiyayyen abinci ta jera a dining tayi tafiyarta. Da safe kuma kullum breakfast din Humairah tea and bread ne, abincin cikin lunch box dinta kuma lemo ne da biscuit, wanda da kanta take dauka dan mamanta mostly tana bacci sanda take tafiya, wani lokacin ma kuma bata gidan.

Sai da ta fara girma sannan take yin dabarar ajiye sauran abincin dare a fridge, da safe sai ta dumama ta tafi dashi makaranta. Bayan ta bar gidan Ojo kuma abincinta shine sauran abincin da mutane suka ci suka rage a gurin masu siyar da abinci, wani lokacin kuma inta samu tayiwa masu abincin wanke wanke sai su dan zuba mata taci, sometimes in ta rasa abinci har bola take bi tana neman abinda zata saka a cikinta saboda azabar yunwa, sometimes har mutane take bi tana neman su taimaka mata da abinda zata saka a cikinta, sometimes har...... Tayi sauri ta kawar da wannan tunanin daga zuciyarta. "Ya rabbi, kar ka mayar dani cikin rayuwar da nayi a baya".

Ta maida hankalinta gurin Aisha da take ta hidimar hada abinci, ko me take hadawa oho? Ita dai Humairah kallonta take tana lura da yadda take aikinta with ease and expertise of a professional, daga gani kasan tasan abinda take yi, a ran Humairah tana ayyana ina ma itama wata rana ta iya girki irin haka? Ina ma wata rana ta ganta a gidan mijinta tana yiwa family dinta girki kamar haka. Sai kawai ta samu kanta dayin murmushi. Aisha ta juyo tana kallonta tace "da fatan kina ganin duk abinda nake yi, dan wata rana kawai zaki ji nace 'Humairah shiga kitchen ki hada mana dinner'"

Humairah ta sake murmushi kanta a kasa, a ranta tace 'Allah Ameen'. Daga nan Aisha ta fara involving dinta a cikin aikin, dauko min kaza, yanka min kaza, soya min kaza, zuba gishiri a kaza, a'a yayi yawa dan rage, a haka dai har suka kusa kammala aikin su, tun kafin su gama gabaki daya kamshi ya cika Humairah yawu sai taruwa yakeyi a bakinta amma bata so tayi taste kar taje tayi laifi. Suna haka Basma ta shigo gidan da sallamarta, suka amsa mata daga kitchen din dan haka ta shigo har kitchen din ta jawo stool ta zauna ta gaishe da Aisha sannan Humairah ma ta gaishe ta. Tana dariya tace "uztaziyya Humairah, wato har kitchen ma da hijab ake zuwa? Allah ya bamu ya taku" Aisha tayi dariya tace "eh, ke gashi nan fita unguwa ma da mayafi kike fita" tace "haba aunty, mayafin nawa ai ba karami bane ba, kuma kayana ba matsatstsu bane ba. Ki barni kawai na shana" Aisha tace "an barki, ai gwara da daddyn ya ce aure zaiyi miki ni naji dadi sosai. Kije can ku karata ke da mijin" Humairah dai tana tsaye tana ta kallon yadda suke hira tamkar kawaye, lokaci lokaci suna dan sakata a maganar a haka har suka kammala hada komai.

Basma bata tsaya jiran akai abinci dining ba tayi serving kanta sai kuma ta dauko spoons guda biyu ta jawo humairah kan carpet suka fara ci tare, Aisha ta kawo musu gudunmawar drink, sai kuma itama ta koma kitchen ta dauko nata spoon din tayi joining dinsu. Suna ci Basma tace "Ni kam aunty Aisha in na tafi kano zan yi missing girkin ki" Aishat tace "ai na gaya miki, ki taho nan ko wata daya ne muyi tare kafin lokacin bikinki, ni kuma nayi miki alkawarin zan koya miki abinciccikan da sai kano emirate sun jinjina miki" Basma tace "kinsan Daddy ba zai barni ba wallahi, amma zan sa Mami ta lallaba min shi ko sati daya ne ya barni inzo inyi, wallahi ina son koyon girki irin naki, abincinki special ne a ko'ina".

Bayan sun gama ne Aisha tace "da mota kika zo Basma?" Ta amsa da eh, tace "please ki kai Humairah gurin tailor dinki ta kai masa dinkunan ta, naso inyi mata da kaina amma bani da time ne kuma bata da kaya isassu" Basma ta bude ido tace "lah, kinga na manta ma, na taho mata da kaya suna mota, bara in ce a shigo dasu".

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now