Dr Mahdi

8.7K 893 31
                                    

Aisha tana faduwa kasa gaba daya suka yo kanta suna salati, aunty kuka take kamar ranta zai fita "innalillahi wa inna ilairir raji'un, wannan yarinya ubangiji Allah ka dube ta da idon rahama, wannan masifa Allah ka yaye mana ita". Hafeez ne ya fita da gudu ya nemo taxi yazo ya kinkimi Aisha Aunty da Zahra suna binsa a baya. Asibitin Murtala suka kaita emergency, nan take aka karbe ta aka fara bata taimakon gaggawa amma shiru bata farfado ba. Gashi suna ta complain din bp dinta yayi kasa da yawa dan haka Aunty ta nemi izinin a tura su asibitin Malam (AKTH), tunda acan Aisha take ganin likita.

Nan take kuwa aka rubuta musu takarda aka tura su can. Shima emergency aka kaita har saida ta farfado ta fara numfashi normal sannan aka kirawo doctor dinta ya dubata yace a mayar da ita inda yake shi zai cigaba da kula da ita. Ranar dai sai dare sannan Aunty ta samu ta zauna, sai a lokacin ta kira number din Abba taji ta a kashe, har tayi niyyar hakura sai da safe sai kuma ta ce bara ta gwada wayar gwoggo. Bugu daya ta dauka dan tana da number dinta itama, cikin muryar kuka ta fara magana "Bilkisu ya muka ji da wannan bala'in daya same mu? Yau naga tashin hankalin da ban ta ba ganin irinsa a duniya ba, wai yarinyar nan ita ce zata iya daukan wuka ta biyo abokiyar zamanta wai sai ta halaka ta?" Aunty tace "ban gane ba, akace min Kamal ta chakawa" tace "eh, ai shiga yayi tsakaninsu, abokiyar zaman tayi niyyar illatawa ita da abinda yake cikinta, shine mijin ya shiga tsakani ashe rabon shi zata illata" Aunty ta runtse idonta tana kiran sunan Allah, sannan tace "yanzu tana ina?" Gwoggo tace "waya sani ne? A gaban mutane abin ya faru dan haka kafin a tafi dashi asibiti har 'yan sanda sun zo, tana jin jiniyarsu ta dauki 'yarta ta gudu babu wanda ya ganta, tun safe ake nema kuma shiru babu labari, duk gidajen kawayenta anje bata nan" Aunty tace "to ya jikin Kamal din?" Tace "da sauki za'a ce dai, amma likita yace babu tabbas dan wukar ta shigeshi sosai. To ba wannan bama, Zayyan yana gurin 'yan sanda sun rufe shi" da sauri Aunty tace "saboda me?" Tace "saboda Khadija ta gudu, kuma shine yafi kowa kusanci da ita shine suka zo har gida suka saka masa ankwa suka tafi dashi a gaban mutane" sai kuma kuka "ni sadiya yau naga tashin hankali, sunce ba zasu sake shiba har sai yarinyar nan ta kawo kanta da kanta, in ba haka ba kuma shi za'a yankewa hukuncin da za'ayi mata, yanzu in yaron nan ya mutu bansan me zasu yi wa Zayyan ba" nan kuma sai ga aunty ta koma bawa gwoggo hakuri har sai da ta daina kukan sannan tace "ina Aisha? Tasan halin da 'yar uwarta ta jefa mahaifinsu a ciki kuwa?" Aunty tace "Aisha babu lafiya, muna asibiti da ita ma yanzu bata ma san waye yake kanta ba, dama shine dalilin neman da nayi miki dan in gaya muku halin da take ciki" gwoggo ta sake sabon kuka "Zayyan yana ganin bakaken ranaku a gidan sa, wannan wacce bakar haihuwa yayi ne lokacin daya haifi Khadija?" A haka dai suka yi ta jajanta abin sannan sukayi sallama.

Tana gama wayar sai ga abban Zahra tare da zahran ya kawo ta da abinci sannan yace aunty tazo su tafi gida in yaso ita zahra sai ta kwana tare da Aishan, saboda itama auntyn tana bukatar hutu. A hanya take yi masa bayanin abubuwan da suka faru, ya jinjina lamarin sannan yayi alkawarin gobe insha Allah zaije dutsen da kansa ya duba Kamal sannan ya police station ya binciki yadda lamarin ya ke.

Washe gari da rana Aisha ta farfado, ta jima tana bin dakin da kallo sannan tunanin ta ya fara dawowa, ta tuno duk abinda ya faru da maganganun da taji Aunty tana yi akan Kamal da Khadijah, ta lumshe idonta tana tuno zuwan da Kamal yayi gurinta shekaran jiya da abinda ya gaya mata, yace yana son yayi mata bayani amma bata bashi dama ba, yanzu kam koma wacce magana ce zai gaya mata ya tafi da kayarsa lahira. She loved him and she also hated him, bata san wanne ne yafi karfi ba a tsakanin love da hate din, amma dai tasan duk biyun tana yi masa su masu tsanani. Kuma duk ta rasa guda biyun saboda 'yar uwarta, saboda Khadija. Khadija.

Ta runtse idonta saboda wani irin sarawa da kanta yake yi, har wani dishi dishi take gani a idonta. A hankali tunaninta ya fara tsayawa har sai da taji kanta ya zama empty bata iya tuna komai, ta mayar da idanuwanta ta rufe.

Wannan karon Aisha tafi ko yaushe dadewa a asibiti dan kwata kwata doctor din daya ke dubata kasa gane abinda yake damunta yayi, taki yin magana ballantana ya fahimci matsalarta, bata uhm bata uhm uhm, babu cin abinci sai ruwa da ake kara mata, ko tashi bata iyayi sai an kama ta. Gwoggo tazo ta duba ta har ta kwana biyu sannan ta koma, a lokacin take gayawa aunty cewa har yanzu ba'a ga Khadija ba, Kamal yana asibiti amma jikinsa da sauki yanzu, abba kuma har yanzu yana rufe sunki sakinsa sunce sai Khadija ta kawo kanta tukunna, gwoggo tana kuka tace "kuma wallahi nasan yarinyar nan ba zuwa zata yi ba, kome zasu yi masa ba zata zo ba. Har babur dinsa aka siyar aka kaiwa 'yan sanda cin hancin ko zasu sake shi amma sun karbe kudin kuma sunki sakinsa".

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now