Changed 2

7.7K 783 58
                                    

Salam all. Kafin mu cigaba zan danyi yar magana kadan. Akwai da yawa da suke zancen cewa su basa son labarin khadija, sunfi son a cigaba da labarin Humairah da Al'ameen. Wato kunfi son labarin soyayya ko? Lol. To shikenan, amma ina so ku sani, kusan rabin lessons din cikin littafin Aisha_Humairah yana cikin labarin khadija. Mutane suna karatun littafi ne saboda dalilai da dama, wadansu dan nishadi, wadansu dan debe kewa wadansu kuma dan su karu da wani abu. Ni kam a bangare na na fara rubuta littafi ne ba dan nishadantarwa ba, yes, dole a samu nishadantarwa a cikin kowanne labari, amma babban dalili na shine dan in ilmantar, dan inyi amfani da kirkirarrun labarai wajan isar da wadansu kananan sakonni gurin al'umma, dan inyi sharing dan abinda na sani akan rayuwa da sauran al'umma, with hope din koda mutum daya ne a cikin daruruwan mutanen da zasu karanta ya chanja wani hali nashi marar kyau zuwa kyakykyawa. Dan haka zamu karasa labarin Khadija. In baka so you can skip this episode ka fara daga next.

Matsala ta shine ban iya takaita labari ba, na fi son in bayar dashi in details yadda za'a fahimci abinda ya faru sosai. In kun lura tun daga kan #MAIMOON har zuwa #AISHA_HUMAIRAH, kowanne character yanada background story dinsa, kowanne character in dai har yayi playing wani role to sai na kirkirar masa labarin sa dan a san dalilin da yasa yayi abinda yayi, because I believe that there is a story behind every person.
Abu na gaba, masu tambayar labarin Ameer. Kuyi hakuri, nayi muku alkawarin in dai muna raye zan baku labarin Ameer, and you will like it insha Allah.

Yanzu zamu dora daga inda muka tsaya.

"Prison din da aka kaini prison ce wadda ake ajiye masu manyan laifi a ciki, masu laifin da ya kamata ace an yanke musu hukuncin kisa amma rashin cikakken evidence ya sa dole aka bar su da ransu. Dan haka babu wanda ya damu ko mutum ya mutu ko yayi rai. Wahala kawai ake sha a cikinta ba kadan ba. Musha wahala a hannun hukuma sannan musha wahala a hannun 'yan uwan mu prisoners. Yawancin su daga arm robbers, sai killers, sai manyan drug dealers. Dan haka sun san takan mugunta iri iri. Akwai abinci kullum za'a raba a bawa kowa amma ni dai nakan yi kwana biyu ko fiye da haka ban ci abincin ba, saboda da zarar na karba wata zata zo ta kwace kuma babu yadda zanyi, wani lokacin sai dai ana bani inyi sauri inyi lona kafin a karba. Kullum muna cikin aikin wahala, mune fasa dutse a tsakiyar rana, mune noma, mune zuwa kwasar kashi sharar bola da dukkan nau'ikan ayyukan da ban taba tunanin zan yi suba. Wani lokacin in muna aikin sai in tuno da sanda umma take sakani aiki nake kin yi, in yinwa da kishirwa sun ishe ni sai in tuno da irin abinciccikan da kike dafa mana har in ringa complain cewa ni basu nake so ba, a lokacin ji nake nafi karfin duk wadannan abincin, saboda a lokacin da nayi waya za'a kawo min duk irin kalar abincin da nake so.

Tun da na shiga prison rabon kafata da takalmi, rabon fata ta da mai. Ana bamu damar yin wanka amma shima ba kida yaushe muke samun sabulu ba sai dai mu wawwatsa ruwa kawai akan dattin jikinmu mu fito. Bani da kawa, bani da abokiyar magana sai ni kadai. Wannan yasa na samu damar yin magana da kaina.

A shekarar farko. I was enraged. Gani nake kamar ni nafi kowa rashin sa'aa duniya. Gani nake life was so unfair to me. Gani nake kowa ta tsane ni a duniya. I hated everybody, my parents, you, my friends, gani nake kamar duk ku kukayi contributing zuwa lalacewar rayuwata. Sannan na tsani maza, gabaki dayansu. A lissafi na duk abinda ya faru dani sune sila, su suka lalatani, su suka sakani a karuwanci sannan daga karshe suka dangana ni da prison. Babu irin alkawarurrukan da ban dauka va na revenge akan maza.

A shekara ta biyu, as I kept thinking about life. I realized that, duk abinda ya faru dani babu ruwan kowa a ciki, duk abinda ya faru dani ni na jawo wa kaina. kullum ina gayawa kaina cewa karuwanci chose me, amma a lokacin sai na fahimci cewa ni ce na zabi karuwanci. Ni na zabi karuwanci tun lokacin da nake shigar banza nake zuwa makaranta. Ni na zabi karuwanci tun lokacin da nake bari maza suna tabani a makaranta, ko kuma in sunzo zance gurina. Nayi tunanin me yasa ke mazan banza basu biki ba? Mai yasa basu bi sauran matan da suka kame kansu ba? Mai yasa sai ni da ireire na suke bi suna lalatawa? Saboda mu muka gayyacesu. Daga ranar da kika ci kwalliya kika saka matsatstsun kaya masu bayyana surarki kika saka dan karamin mayafi wanda bai tufe komai a jikinki ba to tamkar kin dauki loudspeaker ne kina shela kina kiran mazan banza su zo gurinki. Wallahil azim duk namijin daya ganki da shigar banza kuma yazo yayi miki magana to ba mijin kirki bane, ba auren ki zaiyi ba, banza yaga tafadi yazo ya debi rabonsa yayi gaba. Duk namijin da zai aureki ba zai taba tabaki ba, ballantana har ya nemi yayi lalata dake. Su kansu mazan banzan in suka tashi aure kammalalliya suke nema, babu wanda zai so ya auri watsatstsiyar mata. Yes, shigar banza da rashin kamun kai yana attracting maza, amma mazan banza. Idan kin saka hotonki mai bayyana sura a social media, zaki ga kin samu daruruwan likes da comments, amma saiki duba kifa su waye masu likes and comments din? Kusan zaki ga duk bana gari bane ba, babu wanda a cikinsu zaki ce ya fito ya aure ki kuma ta fito din, in kuwa an samu wanda ya fito to ba lallai ne auren ya dore ba dan ba sanki yake ba abinda kika nuna a hoton shi yake so, da zarar ya samu kuma shikenan.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now