Destined for Greatness

8.7K 731 20
                                    

Nura bai bata lokaci gurin hada lefe ba wanda kusan rabin kayan tare da Aisha suka siyo su, komai tare suke zaba, in ya fara siyan kaya har sai tace masa ya bari haka sun isa shi kuma sai yace shi basu ishe shi ba. Kusan sati suka dauka suna abu daya, da ta gama lecture zasu fita sai magrib sannan zai kaita gida. Kuma duk fita sai ya sayi wani abun ya bata, ita har dariya abin yake bata, ta lura Nura mutum ne mai kyauta sosai dama can dan bashi halin yi mata kyautar ne amma yanzu kam masha Allah.

Yana gama hadawa aka kai, Abba yace akawo Kano gurin Aunty kawai ba sai an kai dutse ba, saboda yana so ya karrama auntyn kuma suma masu kawo kayan ya rage musu wahala. Ai kuwa Aunty taji dadi sosai nan da nan ta kira sauran 'yanuwan Umma na Kano suka zo karbar kayan lefen A'isha for the second time. Set biyu na akwati aka kawo kuma kowannen su a cike da kaya. Ba wai yawan kayan ne ya dauki hankalin mutane ba irin quality din kayan, komai ka daga abin kallo ne komai ka gani kasan me tsada ne mai class ne ba a gurin kowa ake samu ba sai manyan mutane. Watanni biyu aka saka bikin, saboda ana so ayi cikin hutun su Aisha.

Labari yana zuwa gurin Nura ya kara bazama neman gida. Aisha ma bata zauna wasa ba, itama ta shiga tayashi neman gidan ta internet tayi searching rent in Abuja. Nan take sai ga gidaje an turo mata iri iri, wadansu sunyi musu girma, wadansu sunyi tsada da yawa, wadansu kuma unguwar ce bata yi mata ba, tafi son su samu a kusa da makaranta tunda duk su biyun anan rayuwarsu take. A haka ta cigaba da bincikawa ba tare data gayawa Nura ba har Allah yasa ta samu abinda take so bayan kwana biyu. Unguwar tayi mata, kuma so far hotunan data gani na gidan suma sunyi mata. Ta kira Nura a waya ta tambayeshi ko ya samu gidan kuwa? Yace "ina fa, inna samu ai you will be the first to know" tace "to ga wani na samo mana, bara in baka number din agent din" mamaki ya hana Nura magana dan baisan tana nema ba. Bai je ganin gidan ba sai da yazo ya dauke ta suka tafi tare. Gidan bashi da nisa sosai da makaranta kuma bashi da nisa da bakin titi. Tun daga gate Aisha ta san gidan yayi mata.

Bashi da girma sosai sai dai yanayin gininsa ne yayi wa Aisha. Komai mai tsada ne a gidan tun daga gate sai 'yar karamar haraba mai rumfar mota daya sai kuma dan karamin balcony wanda zai sadaka da palo. Palon yana da girma irin mai hade da kitchen din nan ne, sai kuma one bedroom mai hade da toilet dinsa. Daga nan kuma sai ka hau stairs wadanda su kansu abin kallo ne yadda aka yi design din su sune suka raba palon da kitchen din, dan ta kasan suma aka shirya kitchen cabinet, stairs din spiral shape ne da golden railer. A sama shima palo ne kusan girman su daya dana kasa sai dai shi babu kitchen, sai kuma master bedroom, katon gaske da manyan tagogi na glass wadanda suka chinye bango guda na dakin, a cikinsa akwai closet da katon toilet. Masu gidan sun saka kayan toilet complete har water heater akwai, dakunan kuma duk da ACs dinsu, anyi tiling tun daga balcony har cikin bedrooms, ko wanne daki color din tile dinsa da paint da ceiling iri daya kuma daban dana wani dakin.

Tunda suka shiga Aisha take zarya, ta hau sama ta sauko ta shiga kitchen ta fito ta shiga bedroom din kasa ta koma sama tama rasa a ina zata tsaya, Nura ya jingina a bango ya rungume hannunsa yana kallon yadda ta kasa rufe baki sai santin gidan take, agent din gidan ya matso yana kokarin yi masa bayanin rent din gidan, Nura yace masa "we will take it" and that was it, ko negotiating ba ayi ba Nura ya karba saboda Aisha tana so.

Bayan Aisha ta koma gida ta zauna a palo tana ta bada labarin gidan Mami da su Bassam suna jinta, har yaran gidan suma suka zo sukayi joining ana ta hira. Aisha ta bayar da labarin gidan nan ya kai sau goma har sai da Atika tace "mu dai ki shirya ki rakamu mu gano wannan gida, dan in ba ganin sa mu kayi ba ba za'a daina bamu labarinsa ba". Casually Mami tace "ki karbi key din gidan, da weekend sai muje mu gano" ba tare da tunanin komai ba Aisha tace to. Ranar Friday ta karbi key din a hannun Nura, Saturday suka tafi ganin gida, ga mamakin Aisha sai taga har da Daddyn su Abdallah a zuwa ganin gidan, tunda suka tafi yake tsokanar ta amarya, ita kuma ta rufe ido.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now