The Ghosts of the Past

8.1K 771 21
                                    

Aisha ta share hawayenta tana tunani a ranta, wannan wacce irin mata ce? Wacce irin baiwa Allah yayi mata haka ta iya tsara magana yadda tasan dole zata shigi mutum, idan tana kallonka kamar she is not looking at you but looking into you, idan tana yi maka magana kuma zakaji tana taba zuciyarka ba wai kawai kunnuwanka ba, sai yanzu Aisha ta fahimci abinda Dr Mahdi yake nufi da yace ba allura zata yi mata ba magana kadai zasuyi, gashi yanzu maganar kadai sukayi amma maganar tafiye mata alluran da akayi wata da watanni ana yi mata.

Ranar baccin da Aisha tayi kadan ne tana tunanin duniya da rayuwarta da kuma abubuwan da suka faru a cikin rayuwar tata. Har kusan assuba ta hakura da baccin ta tashi ta yi alwala tazo tana sallah har akayi sallar asuba sannan tayi ta gabatar da addu'o'in ta gode wa Allah daya bata ikon ganin haske ya yaye mata duhun idanuwanta sannan ta nemi jagorancin ubangiji akan dukkanin abubuwan da zata cigaba da fuskanta a cikin rayuwarta. Tana nan zaune akan sallaya har gari ya fara haske, har ta fara jiyo hayaniyar mutanen gidan sun tashi suna shirin fita.

A lokacin ta yanke shawara guda daya, shawarar itace; zata koma dutse gurin abbanta, zata nemi Kamal su zauna suyi magana, za kuma tayi magana da Abban ta shima, saboda ta fahimci cewa a rayuwa in dai har kana son kayi facing future dinka you have to visit the fast and make peace with it, in ba haka ba ko kayi gaba fast din zai yi ta hunting dinka ya hana maka nutsuwa, ta tashi ta shiga wanka ta fito tana shiryawa wata yarinya ta shigo ta kawo mata abincin breakfast, ta zauna tana ci Abdallah ya shigo da gudu da uniform a jikinsa yana yi mata magana da hannu, ta tsaya kawai tana kallonsa, ya gane ba fahimtarsa take ba sai ya karaso yayi pecking dinta a cheek ya fita a guje, ta yi murmushi tana shafa gurin tana jin son yaron da tausayinsa har cikin ranta.

Ta gama cin abincin kenan sai ga Mami ta shigo da alamar ta gama shiryawa fita zatayi. Aisha ta gaisheta ita kuma ta amsa da usual fara'ar ta ta zauna a bakin gado tace "Aisha zan fita, ina ganin ba sai mun fita tare ba dan bana jin kina da sauran issue da asibiti, na gaya wa Dr Mahdi kina gidana dan haka in ya taso daga office zai zo ya dauke ki. Ban san menene plan dinki for the future ba amma ina son ki sani cewa am here for you, duk sanda kike neman shawara ko kuma wani taimako be it na kuɗi ne ko favor ko kuma in kina neman someone to talk to ina fatan zaki zo wajena" ta zaro card dinta ta mika mata tace "ga phone number dina nan, am available 24/7"

Aisha tayi godiya sannan ta gaya mata shawarar data yanke na komawa dutse tayi facing fast ghosts dinta, Mami ta gyada kai tace "hakan ma yayi, ni kuma ga tawa shawarar. Idan kin gama da dutse ina son ki dawo nan, ina son ki koma makaranta tunda kince min kin fara karatu kika ajiye. Babana shine VC na university din nan garin, If you want I can talk to him sai ya aika can dutsen a turo masa transcript dinki sai kawai ki cigaba da karatun ki anan. Zaki iya zama anan tare dani, zaki iya zama gidan Dr Mahdi sannan zaki iya zama a hostel. The choice is entirely yours. Just know that we will all be here for you whenever you need us" Aisha ta dago kai tace "amma Mami ba kya ganin kamar it is a little bit late in koma makaranta? Am almost 25years fa yanzu" Mami tayi tsaki tace "wanne irin late kuma? Ai yanzu shine perfect time dinki na karatu. Baki san cewa akwai matan da suke yin aure su hayayyafa sannan su fito su koma makaranta ba? Akwai wadanda ma suke hada wa da auren da haihuwar da karatun kuma suyi su zama successful. 25 years to too young I tell you. Rayuwar kima ko fara wa bata yi ba. Don't ever think you are too old for anything".

Aisha ta jinjina kai, itama tun jiya tana lissafin makarantar a ranta amma tana tunanin kamar chance dinta ya riga ya barta, amma yanzu ta samu courage. Ta ce " nagode Mami da duk kanin abinda kika yi min, I will never forget, insha Allah I will think about duk abubuwan da kika ce sannan kuma in gaya miki shawarar dana yanke" Mami ta mike tsaye tace "you do that, kiyi maganar da Dr Mahdi kuma kiyi da auntyn ki da abbanki, kowa kiji shawarar sa, sai ki auna ki yanke hukunci. Amma ina tabbatar miki da cewa, this is just the beginning of the beginning of your life". Ta fita ta bar Aisha tana kallon bayanta.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now