The Price

9.4K 788 50
                                    

Washegari Kamal da iyalinsa suka koma Yola, zuciyarsu fal da farin ciki, bakunansu fal da labari. Da zasu tafi Humairah sai kuka, dan ji tayi sam bata son rabuwa dasu sannan kuma tana son zaman Abuja, suka yi tayi mata dariya. Ta turo baki tace "dan Allah mommy (maryam) ki bar min Amna" Maryam ta kama hannunta tace "to in na bar miki ita karatun zakiyi ko kuma rainonta zakiyi?" ta fara bubbuga kafa a kasa zata sa kuka sai Maryam ta jata gefe tayi mata rada a kunne, sai gata kuma tana dariya. Kamal yana kallonsu fuskarsa cike da jin dadin yadda Maryam take yiwa Humairah yace "me kika ce mata?" Maryam tace "ina ruwanka? It is a girls thing" suka kuma yin dariya sannan suka tafi cike da alhinin rabuwa da juna.

A ranar ne kuma da daddare Humairah tana shirin shiga wanka aka aiko wai ana kiranta a waje, tayi mamaki saboda ita dai babu wanda yake zuwa gurinta sai Al'ameen shi kuma dazu suka gama waya dashi kuma baice mata zaizo ba. Ta tura a tambayo waye sai akace mata kaninta ne. Da sauri ta mayar da kayan jikinta ta saka hijab taba jin excitement saboda tasan mutum daya ne zai fadi haka, Abdallah. Amma kuma tana mamakin yaushe yazo gari?

Tana fita compoud ta hango motar gidan Mami da mutum a tsaye a kusa da ita amma saboda ya juya mata baya bata ganin fuskarsa, sai dai kuma ta tabbata ba Abdallah bane ba. Sai data karasa tayi sallama sannan ya juyo. Bassam. Taji gabanta ya fadi sosai dan ita tun abinda ya faru tsakanin su rannan take jin tsoronsa. Kananan kaya ne a jikinsa kamar kullum, ear piece a kunnensa sannan hannayensa a rungume a kirjinsa. Sai daya cire ear piece din sannan ya amsa mata sallamar, yace "yayata" sannan yabi kalmar da wani kawataccen murmushi. Nan take sai taga ya koma mata Bassam din da ta sani a da, Bassam mai yawan murmushi kamar Mami kuma mai yawan tsokana kamar daddy. Sai ta kasa amsawa ta sunkuyar da kanta tana wasa da bakin hijab dinta. Ya jingina a jikin motar yace "zuwa nayi in baki hakuri Humairah, abinda nayi miki ban kyauta ba kuma na fahimci kuskure na ba tun yanzu ba. I thought I was looking out for my brother, for Ya Ameen. Amma na fahimci kuskurena ne tun lokacin da na fahimci he is ready to give up the throne for you. A lokacin nasan cewa soyayyar gaskiya ce yake yi miki, ba wai scheme kika shirya ba, amma kunya ta hanani inzo in baki hakuri tun a wancan lokacin, yanzu kuma na tabbatar cewa tabbas ke din zaki zama part of our family indai ba wani ikon Allan da bama fata ba, kuma familyn mu babu 'baraka a cikinsa, wannan ne yasa ya sakawa kaina courage din zuwa wajenki in dinke barakar dani na samar da ita. Kiyi hakuri please, ki manta wani abu mai kama da wancan ya taba shiga tsakanin mu. Kuma in na ce miki yayata ki ke amsawa" ya karasa maganar da sigar tsokana.

Kawai sai ta samu kanta da murmushi, how can she not forgive him? Tabbas lokacin abin ya bata mata ranta sosai amma kuma kamar yadda ya fada he was looking out for his brother, a lokacin ganinta yake yi tamkar wani disease da tazo zata gurbata rayuwar danuwansa. Ta dago tace "zan ke amsawa in dai har zaka ke durkusawa in zaka yi min magana" dariya yayi itama tayi dariya, sannan yace "an gama babbar yaya" ya fada yana bending gwuiwoyinsa. Suka sake dariya sannan tace "am just glad that Al'ameen have a brother like you" yace "I am glad for having him as a brother also. Kuma gwara inja miki kunne tun yanzu ki san cewa yafi so na a kanki, ehe" tace "ba matsala, ni kuma nafi son Abdallah a kan ka" haka suka cigaba da hirarsu cikin wasa da dariya, this was the first time da Humairah ta saki jiki da Bassam, kuma dukkan nin su sunji dadin hakan.

Cikin wata daya aka gama maganar auren Humairah da Al'ameen. Komai ya daidaita dan babban wan su Kamal ko thinking twice baiyi ba yace ya bayar, haka ma Alhajinsu, yana jin daga inda Al'ameen yake abinda ya tsaya bincikawa kawai shine halayyar yaron da kuma sana'arsa, dukka ya samu positive result dan haka shima yace ya bayar. Aka kai kudi aka yi komai na al'ada. Amma sai Mami tace "in anje a saka shekara biyu". Sam wannan hukuncin baiyiwa Al'ameen dadi ba amma haka Mami tayi stamping feet dinta dan ba zata bi son ran danta ba ta bata rayuwar 'yar wata. Tace ba za a yi auren ba sai Humairah ta cika shekara 18 kuma ta gama secondary school. Ta ce tana kallon yadda Al'ameen yayi kicin kicin da fuska "maybe kafin nan ma kaga ta kara yawo, maybe ta chanza decision" Bassam yayi sauri yace "Maybe ta zabe ni" duk sukayi dariya sanda Al'ameen ya ajiye spoon din hannunsa ya bar gurin kamar zai tashi sama.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now