Humairah 2

9.5K 748 30
                                    

Wani abu ne ya tokare a makogwaron Al'ameen, irin abinda in ba kuka kayi ba bazai wuce ba, amma kuma shi ba ma'abocin kuka bane ba dan haka yasan abin will continue to be there har sai ranar daya goge wa Humairah hawayenta, har sai ranar da ta daina kuka. Ya dauke idonsa daga cikin nata dan ba zai iya cigaba da jure kallon cikin idon nata ba. Sai da yayi gyaran murya sannan yace "you are right. I wouldn't have survived that. You are also right, ban san rayuwaba, bansan komai a rayuwaba, abinda na sani a rayuwa kawai shine dadinta, bansan wahalarta ba" ya danyi shiru sannan ya cigaba da cewa "please ina bukatar in san more akan rayuwarki, ina son insan wacece Humairah, watakila nima in samu knowledge akan rayuwa kamar yadda kike dashi" ta rufe idanuwanta, sannan ta saka hannayenta ta rufe fuskarta, ta jima a haka sannan ta bude fuskarta tare da share hawayenta tace "zan baka labarin rayuwata Al'ameen, amma amana zan baka, in ka fadi wa wani kai da Allah, ban yarda ko Mami ka gayawa ba".

Bai ce komai ba, ita ma bata jira amsar tasa ba ta fara magana:

Sunana Aisha-Humairah, Mahmud din da nake amfani dashi ba sunan babana bane ba, bansan sunan babana ba, ban san shi ba ban san komai a kansa ba. Farkon rayuwata na fara tane a wani gari wanda ba zan iya tuna sunan saba, na san dai kauye ne sosai a kuma arewacin Nigeria yake. Babban abinda zan iya tunawa a garin shine kasuwar garin, babbar kasuwa ce sosai wadda take ci duk ran lahadi. Gidan da muka zauna a garin babban gida ne sosai, ina iya tuno girman tsakar gidan da kuma yadda dakunan suke jere a kan verandah. Wadansu dakunan da toilet a cikinsu wadansu kuma da na tsakar gida suke amfani. A daya daga cikin dakin muka zaune ni da mamana. Dakin mu bashi da girma sosai amma muna da ban dakin mu a cikin dakin. Babu gado a dakin sai katifa guda daya da kuma doguwar kujera a gefe. Labule aka saka aka raba dakin biyu, wannan yasa ya zama kamar cikin daki da palo. Gidan a cike yake da mutane maza da mata, mata suna iya kama daki maza ma haka, babu ruwan wani da wani, babu ruwan wani da me wani yake ciki duk kuwa da cewa ana zaune a gida daya. Wannan shine inda na bude idona na ganni.

Mamana bata barina in fita ko'ina, ko da kuwa tsakar gidan ne, tace min wannan shi yasa ta kama daki mai toilet saboda bata so in fita. Kullum da daddare ina jin ana ta kide kide da raye raye a tsakar gidan amma bana zuwa sai dai in tsaya a bakin kofa ina kallo, shima kuma dana hango Mama zan koma in kwanta kamar bacci nake yi. Wannan ya saka bani da abokan wasa sam, babu wanda na sani babu wanda ya sanni, sai 'yar tsanata da Mama ta sayo min da ita kullum nake wuni ina hira, ita ce abokiyar hira ta itace abokiyar shawarata, da ita zan zauna inyi ta hira ina bata labaran da nake kirkira na irin rayuwar da nake kwadayin kasancewa a ciki. Rayuwa wadda zan kasance tare da mahaifina da mahaifiyata a guri daya.

Mamana bata zama a daki, dan haka kusan kullum ni kadai nake wuni babu kallo babu abokin wasa. Amma kuma duk inda lokacin cin abinci yayi zata siyo mun abinci ta kawo min kuma ta tabbatar cewa naci sannan ta sake fita. In zata dawo kuma da daddare yawanci ba ita kadai take dawowa ba, tana dawowa tare da wani, namiji, always namiji. Wani nasan shi wani kuma bakuwar fuska ne ban taba ganinsa ba. Wani in yazo yau yakan dawo gobe, wani ma yakanyi kusan wata guda yana zuwa har in saba dashi sannan kuma sai ya daina zuwa, wani in yazo sau daya ba zai sake zuwa ba. Duk wanda yake zuwa dakin mamana yasan dani a dakin, wadansu sukan kulani suyi min wasa ko su kawo min wani abu su bani, wadansu kuma ko kallon inda nake basayi haka zasu shige ciki inda mamana take kwana. Na gaya maka dakin guda daya ne labule kadai ya raba shi biyu, ciki anan Mama take kwana da duk wanda ya biyo ta ranar, ni kuma ina daga palon akan kujera, dan haka duk abinda yake faruwa a dakin inaji, the sounds, the voices, kullum dare inajinsu, kullum dare bana bacci har sai sunyi bacci. I can still hear them in my head. Lokacin ban san takamaimai me suke yi ba amma nasan akwai abinda suke yi a ciki.

Bayan na dan kara wayo na kai shekara shida sai na fara satar kafa ina fita in Mama ta fita. Anan nake shan iska inga mutane inyi ta zagaya unguwar sannan in dawo dakin mu. Har in fita in dawo babu wanda zai kula ni, babu wanda zaiyi min magana. In fact babu yara sam a unguwar sai manya, daga masu sayar da abinci sai masu shaguna sai kuma wadanda zan gani a zaune suna zukar hayaki suna fesarwa. Ranar nan ina tafiya sai na hango kamar wata yarinya suna tafiya ita da wani, nan da nan na kara sauri inaso in ganta sosai, ko da ban yi mata magana ba in ganta kawai. Wani shago naga sun shiga dan haka na je na leka nima sai na gansu suna siyan kaya a gurin mai shagon, yarinya ce kusan sa'a ta amma ta dan girme ni sai dai ni da yake ina da girman jiki, sai namiji dan matashi daga gani yayanta ne. Suka gama siyan abinda zasu siya suka juya babban yana rike da hannun karamar suka dau hanyar barin unguwar.

Aisha_HumairahNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ