The Ghosts of the Past

8K 732 5
                                    

Kamar da fadar mala'iku kuwa sai gashi ya shigo, ya tsaya a bakin kofa yana kallon Aisha da maryam a zaune, Maryam ta mike da kyar tana washe baki tace "ya Kamal kaga Aisha yau a gidan nan, kawai muna zaune sai gata ta shigo, ko dama kasan da zuwanta?" Bai bata amsa ba idonsa yana kan Aisha wadda ita kuma kanta yake kasa, ta dago suka hada ido, har yanzu akwai rama sosai a tare dashi sai dai duhun da taga yayi kwanan baya yanzu ya washe. Har haki yake yi alamar duk daga inda yake da sauri ya taho.

Aisha ta sunkuyar da kanta kasa ta gaishe shi. Bai amsa ba ya karaso ya zauna a hannun kujerar da take facing dinta yace "Humairah? Ke ce a gidan nan da gaske ba mafarki nake yi ba?" Ta danyi dariya tace "ni ce Kamal, ba mafarki kake yi ba" ya karasa zama sosai a kujerar har yanzu idonsa a kanta, Maryam ta dawo ta zauna a gefensa, yace "Baki na ba zai iya fada miki yadda nake ji a raina ba Humairah, sanda yakumbo ta kira ni ta gata min cewa wai gaki kin zo gidan nan I couldn't believe my ears, yanzu kuma da nake ganinki a zauna I can't believe my eyes Humaira, wannan mafarki na ne kullum, addu'a tace kullum inga ranar da zamu zauna ni dake muyi magana in roke ki gafara kuma inji kince kin yafe min, bayan burina na sake ganin 'yata wannan shine second burina"

Ta gyada kai tace "nima sati daya kafin yanzu Kamal in aka ce min zanzo gidanka in zauna a palon ka tare da matarka bana jin zan yarda, amma yanzu gani a zaune, rayuwa kenan, you can't know whats going to happen next in your life har sai ya faru" yace "hakane, amma what made you come? What made you change your mind? Saboda sanda naje gurinki kano banga alamar kina bukatar gani na ba" tace "kamar yadda na gaya maka rayuwace, nima ban yi tunanin zan saurareka nan kusa ba amma yau gani, I want to put my past behind me and face my future"

Ya gyada kai yace "you want to know what made me change my mind akan aurenki?" Ta hadiye wani daci a ranta tace "yes, I want to know why" ya gyara zama yace "Farko dai Humairah ina son ki sani cewa ban taba son wata mace kamar yadda naso ki ba, I loved you fiye da tunaninki, duk abubuwan dana gaya miki tun ranar dana fara ganinki wallahi Humairah babu karya a cikin su ko yaudara, duk abinda nace miki hakan nake nufi har cikin zuciyata. Kiyi hakuri da abinda zan fada amma 'yar uwarki shaidaniya ce Humairah, nasan 'yammata iri iri a rayuwata amma ban taba haduwa da irin Khadija ba. Farkon ganina da Khadija ban taba saka ta ko da a cikin jerin matan da zan iya aura ba, saboda duk bata da qualities din matar aure a gurina. I was kind to her saboda 'yar uwarki ce, wannan shi yasa na sakar mata fuska saboda ina son in faranta miki musamman ganin yadda kike sonta a matsayinta na 'yar uwarki kwaya daya. Khadija tayi amfani da kindness dina wajan shiga jikina, she was so conning, so convincing, so conniving. At first kawai sabo ne ai tsakani da ita, kullum zata zo in muna tare dake, mostly in zan taho gida kuma zata biyo ni tace zata zo gurin Maryam. She befriend Maryam, dan haka ta samu guri a gidan nan, Maryam ta numa mata har daki na, dan haka lokuta da yawa sai dai kawai in shiga dakina in tarar da ita a zaune, ko ta kunna kallo ko tana karatu wani lokacin ma tana bacci, in nayi mata magana sai ta nuna min ita fa kanwa tace kuma dan kanwa tazo gurin yayanta ai babu wani abu, a duk lokacin da ta shiga ko kuma duk sanda muka kadaice da ita tana matukar amfani da damar ta wajen presenting her nakedness to me wanda hakan yana damuna sosai. Har sai da na chanza lock din dakina sannnan na samu ta daina shiga. A hankali abubuwa suka fara chanza min, I never love Khadija amma my body wanted her, har bana jin dadi idan ban ganta ko na yi mata magana ba, she kept leading me on and I kept following, thinking abin mai wucewa ne amma bai taba wucewa ba sai ma karuwa da yake yi kullum, kullum kara son ganin abinda take nuna min nake yi. Wallahi A'isha sai da abin ya faru da ni sannan na tabbatar da cewa shaidan is nobody's mate, ba zaka taba boosting cewa kai tsarkakke bane cewa ai kai ba zaka taba aikata kaza ba but just thank God cewa Allah bai taba yi maka irin jarabawa kaza ba. I felt so lost. I loved you with all my heart but my body wanted Khadija. It was lust, pure lust. I know it is hurting to tell you all this but I want to tell you duk da nasan ba lallai ne ki fahimceni ba saboda ke din ta daban ce, you are so innocent".

Aisha_HumairahOnde as histórias ganham vida. Descobre agora