The Little Devil

8.1K 733 17
                                    

Aisha bata yi mamakin kalaman Khadija ba, saboda ta riga tasan halin Khadija a rayuwa kanta kadai ta sani bata damu da kowa ba. Sai da ta bari Faruku ya tafi sannan ta bude kofa ta fita, har daki taje ta sami Shema'u ta bata hakuri, ta kwantar mata da hankali sosai ta nuna mata cewa Khadijah ita kadai take haukanta babu yadda za'ayi Abba ya goyi bayanta, dan haka ta saka a ranta cewa wannan abin ba zai yiwu ba.

Ranar sai ga Aisha suna hira da gwoggo, har gwoggo tana bawa Shema'u labarin neman auren Aisha da za'a zo gobe, Shema'u tayi mata murna suka fara shirin abincin da za'a yiwa baki. Aisha ce ta roki gwoggo cewa kar a gayawa Abba maganar Khadijah tukunna, yanzu hankalinsa gaba daya yana kan baƙin da za'ayi gobe, a bari sai ya nutsu tukunna, tunda yanzu ba lafiya ce ta ishe shi ba.

Washegari tun safe Aisha da Shema'u suke shirin abinci, fried rice sukayi wa bakin mai kyau, duk dadai babu nama amma taji kayan lambu tayi shar da ita, sai kuma suka hada kunun aya mai kyau shima, Shema'u ce tace fried rice din nan zata fi shiga da couslow, dan haka daga cikin jakarta ta fitar da kudi ta bayar aka siyo kayan couslow, an sami komai amma kudin ba zasu isa a sai salad cream ba, dan haka Aisha tace zata iya hada wa da kanta, tace a siyo mata kwai da lemon tsami. Ana kawowa ta fasa kwan ta zuba farin a cikin blender, ta matse lemon tsami akai, sannan ta zuba sugar teaspoon daya gishiri rabin teaspoon, ta kunna blender din tayi blending dinsu har sai da suka hadu suka yi kumfa, sannan ta dauko man gyada tana zuba wa kadan kadan tana blending, nan take sai ga mayonnaise ya hadu sosai, ga dadi har yafi na company ma, ga kuma lafiya tunda ba'a saka masa chemicals ba, tana gama wa suka hada couslow dinsu suka rufe da foil paper.
Duk abinda suke yi Khadijah tana daki tana jinsu, sai da suka gama komai Aisha ta shiga dakin sannan taga Khadijan a kwance, tace "munafurcin banza munafurcin wofi, wai kenan 'yar uwata uwa daya uba daya, amma ba zaki tayani yakin neman abinda nake so ba" Aisha tace "Khadija da ace abinda kike so abu ne mai kyau da sai inda karfi na ya kare wajan nemo miki shi, amma ni ba zan taya ki kokarin raba aure ba" daga nan bata kuma kula ta ba, ta rabu da ita tana ta fadin maganganunta. Abba da zai shigo sai gashi da lemuka da ruwan roba da kuma kaji, ya basu hakurin suyi hakuri bai kawo musu kajin da wuri an yi aikin su ba, nan da nan suka tashi suka hada pepper chicken tunda kajin na gidan gona ne basu da wahalar aiki.

Alhamdulillah anyi sa rana an gama, sun kawo kudin su dubu dari uku, shi kansa Abba sai da yayi mamakin kudin saboda ganin yaron ba aikin yi ne dashi ba yanzu ma yake kokarin kammala karatunsa. An saka rana wata biyar, saboda ana so bikin yazo dai dai hutun su Aisha lokacin kuma shi Kamal ya kammala nasa karatun. Baƙi sunci abincin amarya kowa yana santi, Abba kuwa bakinsa har kunne musamman ganin su duk fulani ne kuma manyan mutane, 'yan uwan Abba ma da suka zo karbar baƙi sun nuna gamsuwarsu sosai da ganin dangin Kamal, haka suka zauna suka yi ta wasa da dariya gwanin ban sha'awa.

A cikin gida kuma bayan Aisha ta yi wanka ta shirya sai ta fito falo suka zauna suna cin abinci ita da Shema'u, duk da cewa rabin hankalinta yana soro a ranta tana son jin abinda suke cewa, Shema'u ta lura sai ta fara tsokanar ta "ko inje in jiyo miki abinda suke cewa ne?" Aisha ta sunkuyar da kai tana jin kunya, Shema'u tace "nima haka naji ranar da Murtala ya aiko tambayar aure na, daga ni har shi hankalin mu a tashe yake dan bamu san ko za'a bayar ba ko kuma a hana. Sai ni nake kiransa ina kwantar masa da hankali, gani yake wai mu fulani bama so mu bawa wani 'ya'yanmu in ba fulani ba" Aisha ta tuna da Kamal, yau musamman ya dauki azumi dan neman sa'a. Shema'u ta cigaba da bata labari "Aisha tunda akayi auren mu da Murtala bamu taba samun matsala ba, Murtala bai taba yi min ko da mugun kallo bane ba. Kuma ni kam zan iya bada shedar Murtala ko a ina ne, ba ya neman mata, ni kadai ce budurwarsa kuma tunda mukayi aure bai kuma yin wata ba" ta ajiye tsokalin hannunta hawaye yana zubuwa daga idanunta, ta cigaba "amma wai yanzu Murtala ne mai ce min in hada kaya na in bar masa gida, yadda kika san fa mahaukaci haka ya rikice min, wai akan Khadijah, wannan yarinyar dana rena da hannuna. Kuma ni babban abin mamakin fa wai a waya kadai ta juya masa hankali har haka. Saboda lokacin da taje can babu komai a tsakanin su sai mutunta juna, lokacin abokinsa ne yake nemanta, amma wai daga rabuwar Buhari da Khadijah a cikin sati biyu har ta juye ra'ayin Murtala zuwa wajenta. Rayinyar da ta iya yin haka ta waya menene ba zata iya yi a fili ba? Khadija Shaidaniya ce, She is a Devil"

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now