New Customer

8.6K 768 1
                                    

Tana nan a zaune har Khadija ta shigo, ta tsaya tana kallonta sannan tace "wannan kayan fa da kika bari a akwati?" Aisha tace "gurin bai isa ba ai" Khadija ta tabe baki tace "OK bara ni in dauke kayana in mayar can dakin, tunda da akwai guri acan, dama yanzu gwoggo take cewa in koma can mu ke kwana tare" Aisha bata ce mata komai ba, kawai ta bi ta da kallo, ta debi fiye da rabin kayan ta, ta mayar dakin gwoggo.

Tun daga ranar rayuwa ta chanja wa Aisha, ita kadai take wuni a daki, ko palour bata zama, saboda data zauna sai gwoggo ta samu wata bakar maganar ta gaya mata, Khadijah kuma tayi mata dariya. Dan haka kullum da tayi sallar assuba take fitowa ta fara aikin gida, duk abinda da takeyi lokacin Umma tana da rai babu abinda ta rage, zata share dakinsu da palo da kitchen da tsakar gida, sannan ta shiga kitchen ta hada musu abin karyawa, sai ta debi nata ta koma daki. Wani lokacin tana jiyo su suna hira suna cin abinci, amma ta gwammace tayi zamanta a daki akan ta fita a gaya mata maganar da zata bata mata rai.

Duk sanda Abba zai fita yakan shigo dakin ya tambaye ta ko akwai abinda take bukata, amma kullum ce masa takeyi babu komai, saboda tasan ba zai iya bata abinda take bukatar ba.
Kullum tana cikin kewar ummanta, tayi kuka na zuci dana fili har hawayenta ya daina zuba, yanzu in tana zaune sai take jin kamar Umman tana tare da ita, wani lokacin sai tayi ta magana ita kadai kamar da Umman take hira, ko kuma ta dauko kayanta tayi ta gyara mata.

Ranar nan tana zaune ta gama kukanta tana goge hawayenta Khadijah ta shigo tana 'yar wakar ta, Aisha tana mamakin wai Khadijah ce ta warware haka kamar ba mahaifiyarta ce ta mutu ba, ta tsaya tana kallon ta tace "ni na rasa wanne kuka ne kike yi haka Aisha, in wani ya gani sai ya dauka kamar kinfi kowa sonta, muma fa duk muna sonta hakuri kawai muke kokarin saka wa zuciyar mu"

Aisha ko kallonta bata yi ba amma hakan bai hana Khadija cigaba da maganar taba "yanzu ai na tabbatar kinyi learning lessons dinki, da ace baki kirata ba da yanzu tana raye, amma bakar zuciyarki da son lallai sai kin hada ni da ita ya saka sai da kika kirata, yanzu ta tafi duk munyi two zero, kin raba ni da ita kamar yadda kika raba ni da karatuna" Aisha taji zafi sosai a ranta, ta mike tsaye tace "haba Khadija, how can you say that, akwai wanda ya isa yayi ajalin wani ne idan lokacin shi bai yi ba? Ya zaki ke magana kamar wata jahila wadda bata da ilimi?"

Khadija ta daga murya "au jahila kuma kike ce min yau? Wato dan kinga babu ran Umma shine zaki ke gayamin magana son ranki ko? To ni na barki da Allah saboda bazan hana uwa ta kwanciyar kabari ba saboda ke" sai ga gwoggo da sauri kamar zata fadi "ke lafiya naji kina magana kamar zaki yi kuka, me ya faru?" Nan take Khadija ta fara kuka tace "gwoggo Aisha ce, kawai daga shigowata daki shine ta fara gaya min maganganu wai ni jahila ce bansan abinda nake yi ba" gwoggo ta rungume Khadija "yi hakuri 'yar baba, kar ma ki kulata ki bata ranki a banza, bakin ciki ne yake damunta, bakin halinta kuwa sai dai ya kasheta, amma ace mutuwa ko sati biyu ba'ayi ba amma har ta fara halin nata? Shi yasa nace ki dawo dakina mu zauna saboda nasan ba zaku zauna lafiya ba" ta juya tana kallon Aisha da ta saki baki tana kallon Khadija, tace "ki ci kanki ki sha ba'kin ruwa, Allah ya na sane ya halicce ki a yadda kike, saboda ya nuna wa mutane kiri kiri cewa ke bakin hali ne da ke" ta ja Khadijah suka yi tafiyar su.

Aisha ta zame ta zauna a tsakiyar dakin, tace "Allah kaine gatana ya Allah" sai kuma ta kifa kanta akan cinyoyin ta tana kukan zuci, sannan ta dago ta kalli kujerar da Umma take yawan zama a kai tace "Umma ba zan iya ba, ba zan iya kula da Khadija ba, Khadija ta tsane ni kuma bansan me nayi mata ba, Khadija bata jin magana ta, Umma kiyi hakuri ki dauke min wannan nauyin da kika dora min dan ba zan iya sauke shi ba".

Tun da akayi sadakar bakwan Umma, Khadijah ta samu kafar yawo, kullum da zarar Abba ya fita ita ma zata yi kwalliya ta fice, ba zata dawo ba kuwa sai magariba, wani lokacin ma sai bayan magriba, tunda yanzu Abba kwanciya bacci ne kawai yake dawo dashi gida. Aisha bata daddara ba ta yi mata magana rannan akan yawon da take fita tace "Khadija kinsan wannan yawon naki bashi da amfani, kinsan kuma Abba ya hanaki, me yasa ba zaki ji tsoron ubangijin ki ba kuma kibi maganar iyayenki?"

Aisha_HumairahWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu