Humairah

7.1K 781 46
                                    

Yayi studying titin da suke kai, babu mutane kuma straight ya tafi babu kwanoni, akwai kuma nisa daga inda suke zuwa karshen titin, ya kalli Humairah yaga gudunta kawai take yi ko waigensa bata yi. He was not about to run after her, not again. Komawa yayi cikin motar ya saka ta a giya ya fara tafiya deadly slow, bai jima ba ya kamo Humairah ya daidaita tafiyar motar da gudun nata ya cigaba da tafiya ta gefenta. Tun tana gudun sosai har ta rage karfin gudun, ta sunkuya ta dafe gwuiyoyinta tana haki sannan ta waiga bayanta daga alama nemansa take amma taga babu kowa, yayi mata dan karamin horn, ta kallo side din da yake da sauri suka hada ido sai kuma ta mike da sauri ta cigaba da tafiya kamar zata tashi sama.

Both sides din titin dogayen katangun gidaje ne babu inda zata shiga ta buya babu kuma wanda zai taimaketa idan Al'ameen yayi niyyar lakada mata duka akan Allah ya isan da tayi masa, amma kuma bashi da niyyar fitowa daga motarsa ma ballantana har ya tabata, sannan kuma bashi da niyyar tafiya ya barta ita kadai akan titin. A haka suka cigaba da tafiya har suka zo karshen titin. Sai da Al'ameen ya jira yaga wanne turn Humairah ta shiga sannan ya bi bayanta a ransa yana murmushin mugunta dan yasan hanyar bata bullewa, Humairah bata ankara ba sai ganinta tayi a kofar wani gida, karnukan gidan kuwa suna ganinta suka fara yi mata haushi babu shiri ta juya da gudu ta bar gurin, duk zafin da zuciyar Al'ameen take masa sai da yayi dariyar irin burkin da taci da yadda ta juya da gudu, shima reverse yayi ya cigaba da bin bayanta har suka koma wancan junction din da suka baro.

By then Humairah ta gaji sosai dan sama sama numfashinta yake fita, kafafuwanta ba zasu iya cigaba da wannan tafiyar wadda babu gurin zuwa ba, ga zuciyarta wani irin daci take mata saboda har yanzu maganganun Al'ameen ne suke amsa kuwwa a kanta. She had been insulted da yawa a rayuwarta amma bata san me yasa nasa yafi yi mata zafi ba. Kuma abin haushin wai dole dai gidansu zata koma tunda bata da gurin zuwa sai can din. Kai rashin gata ma dai baiyi ba a rayuwa. Wadansu steps ta hango a gefen titin wanda daga gani anyi sune saboda zama, ba tare da dogon tunani ba ta karasa gurin ta hau ta zauna tana jin duk jikinta yana yi mata ciwo, tana ganin sa yazo yayi packing a gefen ta.

A bangaren Al'ameen kuma tun kafin su dawo junction din ya fahimci ta gaji da tafiya, amma ya kasa fitowa yayi mata magana kamar yadda ya kasa dauke idonsa daga kanta. She have been running and walking for about an hour amma ko dai dai da second daya hawaye bai daina bin fuskarta ba. Ko wanne digon hawayenta ji yake kamar a zuciyarsa yake diga. Da ace hawaye yana karewa daya tabbata yau da hawayen Humairah ya kare. Sai ya samu kansa da tambayar kansa cewa sau nawa tana irin wannan kukan a rayuwarta? He really want to know more akan rayuwarta duk da baisan dalilin da yasa yake so ya sani din ba, maybe curiosity.

Yana ganin ta zauna ya taka burki a gefenta, still idanuwansa akan fuskarta wadda ya lura har kumbura tayi tayi ja saboda yawan kukan da tayi. Sai yaji a ransa cewa bai kyauta mata ba. Yasan matsalarta, amma duk da haka ta daure ta shigo motarsa bai kamata ya gaggaya mata maganganun daya gaya mata ba, bai kamata ba sam, it was not gentleman like. A lokacin ya lura da yadda jikinta ya fara karkarwa alamar sanyi takeji, sanyin dare ya fara sauka gashi kuma babu wani mayafin kirki a jikinta. Ya kashe motar ya fita ya bude baya ya dauko wata coat dinsa ya zagaya gurinta. Sai da ya hau kan steps din sannan ya zauna shima a kusa da ita duk suna kallon titi, yana zama ta mike ta matsa daga kusa dashi ta sake zama, shima ya tashi ya bita inda take amma bai zauna ba sai da ya lulluba mata coat din a jikinta sannan ya zauna. Wannan karon bata tashi ba sai ta kara jan coat din tana lullube hannayenta da ita.

Sun jima a haka kafin ya bude baki a hankali yace "am sorry". Bata ce komai ba ya sake cewa "am sorry. I shouldn't have said what I said. You don't deserve that" ta yi magana cikin muryar kuka tace "ba sai ka bani hakuri ba, ka fadi abinda yake ranka ne. Abinda ka fada shine exactly what you think of me" ya jinjina maganarta sannan ya tambayi kansa "hakane? Abinda ya fada shine abinda yake ransa?" A fili kuma cewa yayi "still, I shouldn't have said it. Kiyi hakuri" ta jima tana kallon bangles din hannunta sannan tace cikin sanyin murya "abinda ka fada din ai gaskiya ne, that's who I am, haka rayuwata take, but I did not choose to be like this, I did not choose to be born like this. Idan da ace ana neman shawarar mutum ne kafin a halicce shi maybe da zan zabi rayuwa irin taka ne, maybe da zan zabi iyaye irin naka. Amma Allah yafi mu sanin dai dai kuma shi ya zaba min wannan rayuwar saboda yana ganin tafi dacewa dani. But you know what?" Bata jira amsar sa ba tace "Banajin kunya ko danasanin kasancewa ta yadda nake, in fact, am even proud of what I am. Dan nayi rayuwa iri iri, naga abubuwa iri iri, nasan rayuwa fiye da yadda a Prince like you ya sani. Nayi surviving abubuwa da yawa wanda am sure kai da kake namiji, strong and perfect, bana jin zaka iya surviving abubuwan da nayi surviving".

Al'ameen yaji challenge a voice dinta, nan take wani tunani yazo masa, if he plays his cards well maybe zata iya ta bashi labarin rayuwarta, amma kuma wata zuciyar sai ta fara tambayarsa "anya kuwa yana so ya sani? Sometimes knowing hurts more than not knowing" Ya juya yana kallonta suka hada ido, ya danyi smiling cynically yace "kina tunanin da akwai wani abinda har ke kika iya surviving wanda ni ba zan iya ba? Kina tunanin akwai wani abu da kika sani akan rayuwa wanda ni ban sani ba?" Ta dauke idonta daga cikin nasa tana kallon fitulun kan titi, har ya fara tunanin tarkon sa baiyi kamu ba sai kuma ta juyo tana kallonsa, idanunta har kyalli suke tace "I have seen my mother raped, times without number, I have been sexually assaulted so many times by different men, so many times that I lost count of, I have been marginalized a makaranta da kuma a unguwa because of who I am, because of who my mother was, I have lived on the street for one full year on my own; babu abinda ban gani ba a wannan shekarar, I have lived in ten poster homes and have attended more than ten schools. Amma duk wadannan ba komai bane ba Ya Ameen, abinda yafi komai a gurina shine the fact that I lost my mother, my only relative, the only soul that really loved me, and the worst thing is that she died because of me, she died protecting me" ta hadiye wani daci a bakinta tace "can you survive all that? Huh Prince?

Nasan ba yawa amma ance da babu gwara ba dadi ko?

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now