The Princes

10.1K 726 39
                                    

Tana fadin haka sai kuma ta kifa kan ta a cinyar Aisha ta fara rera kuka, Aisha ta na jin kukan nata har cikin ranta amma bata rarrashe taba sai kawai ta cigaba da shafa gashin kanta wanda yanzu ya warware ya zubo har saman bayanta. She need to cry it out, she need to open up. A ran Aisha ta fara imagining yarinya karama wadda bata san kowa ba sai mahaifiyarta, sannan kuma mahaifiyar ta fadi ta mutu ta barta.

Sai ta tuno da mutuwar tata mahaifiyar, ta tuno da yadda taji a zuciyarta duk da cewa tana da mahaifi da 'yan'uwa da gatanta. Kuma da shekarunta. Humairah kuwa fa? A hankali tasa hannu ta share guntun hawayen daya taru a fuskarta, a lokacin kukan da Humairah take yi ya dan sarara. Aisha tace "ko zaki iya bani labarin rasuwar mahaifiyarki? Ko zaki iya gayamin dalilin da yasa kika ce saboda ke ta mutu?" Humairah tayi saurin girgiza kanta, no, bazata iya bawa kowa wannan labarin ba, dan hakan yana nufin sai ta fadi ainahin wacece mahaifiyarta, zuciyarta ba zata iya dauka ba. Tunda take bata taba zama tayi hirar mahaifiyarta da wani ba sai dai tayi da zuciyarta, wani lokacin kuma ta rubuta a diary dinta, dan haka yanzun ma ba karamin kokari tayi ba da har ta fara maganar da Aisha.

Aisha ta gyada kai alamar fahimta tace "kar ki damu, babu wani abu if you are not ready to open up to me now, amma ki sani duk sanda kika shirya, duk sanda kike bukatar kiyi magana da wani, I will be here for you kinji?" Humairah ta gyada kai sannan ta mike a hankali tayi hanyar daki tana jin zuciyarta tayi mata nauyi, Aisha ta bita da kallo tana lura da yanayin tafiyarta sannan tace "Humairah?" Ta juyo, "ko zaki iya gayamin ya sunan Mahaifiyarki?" Humairah tayi shiru tana tunani, suna biyu ta san mamanta dashi, daya Aisha, sunan da take amfani dashi a duk sanda take cikin nishadi, dayan kuma Nafisa, shi kuma tana amfani dashi ne in tana cikin bacin rai, sannan kuma da can, wani lokaci da dadewa, tun kafin su je lagos, tun Humairah tana 'yar karama, tana amfani da wani suna daban, but it doesn't matter, she is dead now dan haka suna ba wani amfani zaiyi mata ba, a hankali tace da Aisha "Sunan ta Nafisa" daga nan ta bude dakin ta shiga ta rufo kofar. Aisha ta sauke numfashin data rike tun sanda tayi wa Humairah tambayar amma har yanzu ta kasa cire zargin da yake zuciyarta.

Kwanci tashi har Humairah tayi wata daya a gurin Aisha. By now ta fara sakin jikinta, tana kunna TV tayi kallo in babu kowa, kuma tana iya shiga kitchen ta zuba abinci da kanta amma duk da haka baya baya take yi saboda gudun laifi. Tana iyakacin kokarinta gurin kimtsa kanta da ajiye bad dabi'unta musamman zagi, amma duk da haka kusan sau uku Aisha tana kamata tana zagi, kuma zagin ma yawanci irin na 'yan bakin tasha, wanda twins ne suke samun rabonsu a zagin dan sune abokan wasanta kuma cikin wasan ne bakinta yake kubucewa ta zage su.

Kullum hakan in ta faru sai taga bacin rai a gurin Aisha amma kuma bata taba koda mentioning mayar da ita orphanage ba, sai dai tana kara jaddada mata tare da twins din cewa zagi ba abu ne mai kyau ba. A bangaren Nura kuma Humairah ta dan fara sakin jiki dashi, duk da ba kula ta yake ba amma yanzu bata tsorata in ta ganshi kuma tana iyakacin kokarinta gurin tunawa ta gaishe shi in yazo guri. Ita bata saba gaisuwa ba, ba'a koya mata ba.

Babban kuma abinda yasa ta fara sakin jikin nata dashi shine irin yadda yake treating dinta, babu wasa, kuma in zaiyi mata magana yana mata magana ne tamkar yadda yake yiwa twins, tamkar yadda uba ya kamata yayi wa 'yarsa. In ya shigo gida bai fiya zama a palon kasa ba, mostly a part dinsa yake zama sai dai su iyalin nasa su bishi can, Humairah kam tunda tazo gidan bata taba taka kafarta zuwa part dinsa ba, kuma daga shi har Aishan basu ta ba bukatar ta shiga din ba.

Sun saba sosai da Basma, dan indai har Basma ta fito to sai ta samu excuse din da zai biyo da ita ta gidan Aisha ta zo gurin Humairah, ita kanta Humairah ta san Basma tana sonta, irin soyayyar nan ta hadin jini. Kuma ita ma Humairan sosai take sakewa da Basma dan har tafi sakewa da ita akan Aisha, in suna hira har dariya zaka ji tana yi.

An siya wa Humairah waya, amma number din Aisha ce kawai data Nura aka saka mata, sai ta Basma data zo ta saka mata da kanta sannan kuma ta dage lallai sai ta bude mata WhatsApp account, Humairah ta nuna mata Aisha ta hana, nan take ta tafi har gurin Aishan tana rokonta. "Aunty Aisha wallahi wani group muka bude nida kawayena purposely saboda shirye shiryen bikina yadda za'ake yin passing information, dan Allah ki bari in bude mata in saka ta a ciki yadda za'ake yin komai tare da ita" yadda ta marairaice ya saka dole Aisha ta hakura ta barsu, tace "amma shi kadai, inna karbi wayar naga wani abin daban zan yi seizing dinta" suka amince.

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now