The Bride

8.6K 665 25
                                    


Wani irin dadi Aisha taji yana ratsa zuciyarta, sam bata ji haushin maganar Maryam ba saboda ta saba da jin maganganu na kushe halittar ta a wajen mutane, ji tayi bata damu da duk abinda Maryam ta fada ba, bata damu da duk abinda kowa ma zai fada akan ta ko halittar ta ba, Kamal loves her, and that is enough for her. That's more than enough for her. Wani irin son Kamal taji yana kara ratsa zuciyarta, yayi mata komai, ya gama mata komai. Kamar yadda yace, shi zata aura ba 'yan 'uwansa ba, dashi zata zauna ba da 'yan uwansa ba, tsakanin ta da 'yan uwansa girmamawa ce da mutunta juna.
Har Maryam zata cigaba da magana taji sallamar su, a take ta hadiye maganar ta, suka shigo duk kanin su fuskar su da murmushi suka zauna aka cigaba da hira. Anan Aisha ta fahimci cewa Maryam ba wai wulakanci ne da ita ba, ba ayi mata tarbiyyar wulakanta mutane ba, abinda suka ji ta fada ra'ayinta ne take fadawa dan'uwanta, dan haka nan take Aisha ta cire komai daga ranta ta suka cigaba da hirar su har suka tafi.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, har Aisha ta gama level one dinta, a lokacin ne shi kuma Kamal da Nura suka zana final exams dinsu. Nura har gida yazo yayi wa Aisha sallama zai koma Yola, tare suka zo da Kamal, sai Aisha taji babu dadi saboda Nura is the closest friend she have dan zata iya cewa tafi sakewa tayi magana da Nura akan kowa a lokacin, hatta shi Kamal din, duk da dai yanzu tana dan shiga mutane a makaranta.

Kamal ne yake tsokanarta "to ko zaki bishi ne ku tafi tare, naga kin wani bata rai kamar zaki yi kuka" Nura yace "kinga shikenan in kika bini sai dai kawai in an daura aure a biyo ki da angonki" ta rufe fuska, Kamal yace "chafdi, an gaya maka in ta bika ni kuma zama zanyi? Ai kafa ta kafar ta, duk inda ta tafi sai na bita, dan wadan nan kwanakin da suka rage ji nake kamar in jawo su kawai ayi a gama" suna ta abinsu Aisha kam tayi shiru tana jinsu, sai daga baya tace da Nura "amma dai zaka dawo in lokacin yayi ko?" Yayi murmushi yace "in lokacin me yayi?" Ta sunkuyar da kanta, yace "ki fada mana da bakin ki inji?" Kamal yace "kai karka takura mata mana, ai kasan lokacin me take nufi, ni bana so inga ana yi wa kowa wannan kunyar sai ni" Nura yace "Allah sarki, nima nawa lokacin zaizo ne" ya juya gurin Aisha yace "a'a, zan so ace dani za'ayi komai, zanso ace har sai na kawo miki Kamal dakinki na danka mishi amanar ki, amma hakan ba zai samu ba. Na samu scholarship zuwa Malaysia, nan da sati uku insha Allah zan tafi a can zanyi masters dina, kafin in dawo kuma inajin sai dai inzo ganin baby ko babies ma" nan take Aisha ta fara hawaye, dan ita kam a gurin Nura take samun comfort, shi kadai take iya zama dashi ta gaya masa matsalarta, shi kadai yasan sirrikanta wadanda ko shi kansa Kamal bai sani ba. Nan suka zauna daga Nura har Kamal din suna rarrashinta har saida ta daina kukan ta koma dariya, suna cikin haka Khadija ta shigo, kallo daya ta yiwa Nura taji ba zata iya zama a gurin ba, ita dai Allah bai hada jinin ta da wannan Nuran ba, shima kuma haka.

Ta tsaya daga bakin kofa tace "yaya Kamal in zaka tafi zan bika, zan karbo sako a gurin Maryam" Kamal ya nuna mata kujera yace "shigo ki zauna mana" ta kalli Nura tace "sauri nake unguwa zani kafin ka gama" Nura ya kalli kayan jikinta kawai ya dauke kai. Ta juya da sauri ta fice. Aisha sam bata jin dadin shigar da Khadija take yi musamman in Kamal yazo, kuma gashi ta mayar da zuwa gurinsu in suna tare da Kamal al'adarta, yauma tasan ganin Nura ne ya hana ta zama, ita kuma tana tsoron yimata magana kar cibi ya zama kari, dan ta samu kwana biyun nan sun shirya suna kwana tare su ci abinci tare suyi komai tare, kuma sosai yanzu Khadija ta rage yawo, ta rage samari, yawanci yawonta gidan su Kamal ne gurin Maryam. Dan haka Aisha itama lallabata take yi dan ta dore a haka.

Satin su Aisha daya da hutu Aunty Bilki ta kira Abba a waya tace ya tura ta ta tafi wurinta kafin lokacin biki, wanda sati uku ne ya rage yanzu, babu musu Abba ya bata kudin mota yace ta tafi. Lokacin da ta kira Kamal ta gaya masa har da fushi yayi, wai shi baya so ta tafi ta barshi, tace "to ai zamu ke waya ko? Kuma kano ai ba nisa ne da ita ba duk sanda kake so zaka iya zuwa ka ganni" yace "amma ba zan ke ganin ki duk sanda nake so ba, danni yanzu in son samu ne nafi son kullum in ke ganin ki, da Abba ma zai ke barina da nan gidan zan dawo inke kwana" a ranta tace 'Kamal ho' shi dai baya gajiya da nuna mata soyayya,  shi yasa kullum itama take kara jin sonsa a duk wani sa shi na jikinta.

Aisha_HumairahOù les histoires vivent. Découvrez maintenant