Stranded

8.4K 760 33
                                    

Let's look at this story from Khadija's point of view.

Yau itama tunda ta tashi daga bacci bata koma ba, tayi sallah ta fito ta taya Aisha hada breakfast, Humairah ma ta shiga amma ganinta yasa ta koma bata zauna ba. Bayan sun gama Aisha ta koma sama dan ta shirya ta kuma taimakawa mijinta shima ya shirya. Khadija bata koma dakin da take ba, sai ta shiga dakin twins ta karbi hudimar shiryasu daga hannun 'yan aiki. Suna yi suna zuba mata surutu tare da jerin tambayoyi, yanzu sun fara sakin jiki da ita. Bayan ta shirya su tsaf ta ja su kitchen ta basu abinci suka ci sannan suka fito palour dan jiran saukowar iyayen. A lokacin ne taji hayaniyar su daga kan bene.

Da dumbin mamaki Nura yake kallon Aisha. Daga alama bai taba tsammanin Aisha zata iya tubure masa irin haka ba. Baki bude yace "what? Kina nufin ki ce min kin zabi Khadijah a kaina?" Aisha tayi saurin girgiza kanta tace "ko daya. Khadija 'yar uwata ce, my only sister. Kai kuma mijina ne, uban 'ya'yana. Duk cikin ku babu wanda zan iya zaba in bar wani. Ina so ne ka fahimci cewa.. " ya katseta yace "in fahimci me? Me zan fahimta? In fahimci cewa ba zaki iya bin umarni na ba? Ko in fahimci cewa kin manta wacece Khadijah? Me kika manta daga halayenta? karyar? Yaudarar ko cin amanar? Kar ki manta bariki fa taje tayi ta dawo. Ko kina tunanin shiryuwa taje tayi a barikin? Now she is here, the next thing you will know zata ce duk abinda kike da shi shi take so, she will try to take away everything from you and I won't stand by and let that happen. And zaI won't have someone like her mixed up with my family". Aisha tace "she is already mixed up in your family, she is already part of your family" bai kula ta ba yacigaba da sauka daga stairs din cikin gaggawa.

A karshen stairs din yaga Khadijah tsaye hannayenta rike da twins wadanda suke shirye tsaf cikin uniform dinsu. Dukkanninsu sun daga kai suna kallonsu shi da Aisha, obviously sunji duk maganganunsu. Ya zo ya janye twins sannan ya nuna ta yace "kar in dawo in ganki a gidana. Ki tattara ki koma inda kika fito" sannan ya daga kai yana kallon Aisha yace "ke kuma ban yarda ki fita ko bakin gate ba, office din ma yau ba zaki je ba" ya ja 'ya'yansa yayi gaba, har ya kai bakin kofa ya juyo ya kalli Humairah da take tsaye a gefe yace "ke kuma kizo ki wuce mu tafi tun kafin in ta tashi tafiya ta kuma sace ki ta tafi da ke".

Khadijah ta daskare a inda take tsaye, ta riga tasan Nura baya son zamanta a gidan amma bata yi tsammanin abin zai kaisu ga rigima shi da Aisha ba. Ta juya tana kallon Humairah wadda tabi bayansa da sauri, har takai bakin kofa kuma sai ta juyo tana kallon Khadijah, da sauri Khadijah ta karaso inda Humairah take tsaye ta riko hannayenta tace "Dan Allah Baby kice kin yafemin" Humairah ta kwace hannayenta ta fice daga gidan, sai data shiga mota ta rufe kofa sannan ta juyo tana kallon Khadija wadda take tsaye a bakin kofar palour, sai taji wani abu mai daci ya taso mata a makogwaro.

A cikin gidan kuma, Aisha ce take saukowa a hankali tamkar wadda aka zarewa lakar jikinta. Tun da suka yi aure da Nura bai taba daga mata murya irin na yau ba, amma kuma a cikin maganganun sa babu komai sai tsantsar nuna kulawa gare ta, wannan damuwar da yayi da ita shi yasa ya zama selfish akan Khadijah. Khadijah ta juyo cikin palourn itama duk jikinta a sanyaye. Suka hadu a tsakiya.

Khadija tace "Yaya Aisha tafiya zan yi" da sauri Aisha tace "No! No! Babu inda zaki je" Khadija ta lankwasa kai gefe tace "mijinki baya son zamana, bana son ku samu sabani a dalili na. Kuna gudanar da rayuwar ku cikin kwanciyar hankali kar inzo in lalata muku." Aisha ta jata suka zauna akan kujera tana fuskantarta tace "Khadijah, Nura mutunin kirki ne, he is just been too cautious, kuma yaki tsayawa inyi masa bayani yadda zai gane, amma na tabbatar miki indai ya bani dama nayi masa bayani zai gane kuma zai barki ki zauna" Khadija tace "na fahimci Nura ai, Abba na ma yace bazan zauna masa a gida ba ballantana Nura? Duk wata soyayya da fahimta ai bayan ta tsakanin iyaye da 'ya'ya take" Aisha tace "Abba fa fushi ne kawai yayi dake, amma kema kinsan irin soyayyar da Abba yake miki babu yadda za'ayi ya juya miki baya, fushi yake yi saboda kin tafi babu waiwaye, baki yi tunanin wanne hali ya shiga ba a cikin shekarun nan. Yasan kina gurina yanzu shi yasa yace kar kije dutse. Amma in ya huce da kansa zai nemi ki tafi can gurinsa ki zauna" Khadija tace "kafin sannan fa? Shikenan sai in zama sanadiyyar samun sabani a tsakanin ki ke da mijinki? Sai in zama sanadiyyar da zaki ki yiwa mijinki biyayya? Am a bad influence Yaya Aisha, duk inda nake alkhairi baya zuwa gurin" Aisha tace "to yanzu me kike so ayi? Hmmm? tell me, so kike in barki ki fita ba tare da kina da gurin zuwa ba? You will be stranded and... "

Aisha_HumairahWhere stories live. Discover now