Chapter 54

162 17 3
                                    



🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
By
🌹Teemahcutey🌹

Page 54.


*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

A&C POV's
"Ehenn go ahead ina sauraren ka"

Kwashe komai yayi ya gayamata tun lokacin da yake tunanin an tab'a lafiyar computer shi har zuwa abunda yagani da wannan daren tare da turawa da yayi a bi su Meenah.

"Inalillahii wa'innah i'laihir raji'un! Inalillahii wa'innah i'laihir raji'un!! Inalillahii wa'innah i'laihir raji'un!!! Me yake shirin faruwa ne? Kayi babban kuskure da ka tura, a maimakon kai kaje da kanka ko kuma da kaga za'a sakata a motor ka fita? Why? Is just because ita ba k'anuwarka bace? Ko kuma dan ba Afrah bace? Zaka bari kana kallo ayiwa Afrah haka? Ka bani mamaki, ba haka na sanka ba MAHMOOD..
Ta k'arashe cikin k'araji tare da nuna bak'in cikin abun a zahiri,

"Dan Allah Ammie kiyi hak'uri, wallahi Allah bani da laifi a ciki, sannan kuma Ammie bana son nayi confronting Dad a yanzu har sai na gudanar da k'wak'waran bincike a kan shi, kuma kema kinsan cewa haka ne kawai mafita wacce zata samo maslaha akan wannan lamarin, kuma Ammie nayi bincike na gano a lokacin da aka kawo wannan mutumin a gidannan, se da na kashe kudd'i na sha wahala kamun aka yi wannan babban backup in a computer, saboda wanda yayi aikin kautar da hankalin computern k'wararre ne ta wannan fannin, bayan haka kuma a lokacin da aka shigo da wannan bawan Allah computer na ya haskomin radiant na mutum a b'angaren daban wanda nake da tabbacin Baby ce, abunda yasa nace haka shine saboda mutanen da suke shigo da wannan naga har d'ayan ya je ya duba ya gani idan ana ganin su amma bansan yanda aka yi ta bar gun ba, haka ina yawan ganin ta tanason ziyartar wannan gurin, wanda har ya kasan ce ina mamaki a duk time inda ta nuface gun.

A wannan daren da wannan lamarin ya wakana inada niyar tariyar ta idan ta dawo na tatsiye ta akan se ta gayamun Abunda take son yi a gun, amma me?

Se naga wannan Mummunan Al'amari ya faru.

Ammie kada kiga laifina saboda rud'ewa nayi na ganin mahaifina a wannan lamarin, am shocked Ammie, am lost, I don't know what I'll do right the way dan Allah Ammie ki fahimce ni kada ki kalli abun a bai-bai"

Lallai kuwa idan dai ba rashin adalci take so tayiwa d'an nata ba ta fahimce shi, sannan kuma yayi k'ok'ari matuk'a kawai dai Allah ne ya k'addari hakan.

Kallan ta ta maida kan shi tace;

"Na fahimce ka, amma wannan abun da akwai rud'ani a ciki, ban ma san ta inda zanfara ba, abu d'aya na sani shine inason ganin baby, ya kamata a nemo ta tun lokaci be k'ure mana ba, bazan yafewa kaina ba idan wani abu ya sami y'ar mutane, yadda da aminci yasa suka yarda ta zauna dani, gashi kuma nayi sake ammun sakiya, taya zan fuskanci iyayen ta? Me zance musu? An d'auke ta daga gidan mu an kaida b'arayi sunyi garkuwa da ita ko ya? What idan aka lalace mata rayuwa? Inalillahii wa'innah i'laihir raji'un, ya Rabb ka ceceni ka kawo mana mafita akan wanna abun"

Haka Ammie ta dinga maganganu gwanin tausayi ga kuma k'wallah da ta ke ta zarya akan fuskar ta, haka ma Captain he can't help but ya tayata kukan, abunda ya saka babban soja kuka ba k'aramin bane.

Abu biyu zuwa ukku ne yake saka Ammie wannan kukan.

—Na farko shine y'ar mutane da ta b'ata da kuma rashin sanin takamammen halinda take ciki.

—Na biyu kuma shin tare da wanne mutum ne take? Mai kirki ne ko akasin hakan? A wane hali take ciki? Tana lafiya? Taci abinci? Shin ta mutu ne ko kuma a raye?

—Na ukkun kuma shine wacce irin rayuwa ce Mijin ta ya fara? Dan mye ze aikata wannan abun? Anya kuwa mijinta ne?

Shima haka Captain kusan sune abubuwan da suke yi mishi yawo akai.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now