Chapter 43

218 22 10
                                    




🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
            By
    🌹Teemahcutey🌹

Page 43.


*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

——————————————————
Fasa fad'ar abunda tayi niya tayi, kowa ya zura mata ido yana jiran abunda zatace, kamar ba zatayi magana ba, kuma se ta tashi ta koma dap da kujerar da Captain yake,
"Ya baby, in fad'a? Shine abunda ta ce,
"Ki fad'i mye kuma?
"Sunanaaaaa"
"Ehhh" kawai Captain yace domin baya son tsawaita zance, acan cikin ranshi kuwa yace silly girl.

"Sunana baby" shine abunda ta fad'a, kallan Ammie tayi tace;
"Ammie, yau inason na d'an fita, gidan su waleedah"
"Toh" Ammie tace.
A tare suka mik'e Ammie tayi d'akin ta Meenah ma haka, a kan dining akabar mazajen, kamin daga bisani suka mik'e sukayi gaba.
K'arfe hud'u dai dai Meenah ta shirya ta fita, bata zame ko ina ba se gidan su Waleedah, to a nan ne fa taji labarin jibi za'akai lefe, wanda ta nuna jin dad'in ta matuk'a ba tare da ta nuna rashin sanin ta akai ba, bayan sun tattab'a karatu sukayi firace firacen su, bayan magriba ta gabato anan tayi musu se da safe ta koma gida, koda ta k'arasa su Captain na waje, hakan yasa suka gaisa kamun ta k'arasa ciki..
bayan ta kammala y'an Gyare gyaren ta, taje gurin Ammie, fira suke yi anan ta shaida mata kawo lefen Adda Miemie da za'ayi, sosai ta nuna jin dad'inta a d'aya 6angaren kuwa ta nuna rashin jin dad'in ta akan gayamata da wuri da Mommah batayi ba. Kiran Mommah tayi sukayi waya akan zasu zo gobe.
Suna cikin firar ne se ga alhazawan naku sun shigo, suma zama sukayi aka cigaba da firar da su. Inda Naufal ya buk'aci akan Ammie ta d'akko mishi album in pics insu da sukayi tun suna yara... albums ne guda biyu manya Ammie ta d'akko, se faman kallo suke suna dariya musamman Meenah da ta had'a hadda dariyar k'eta, wannan ne ya harzuk'a Captain ya warce album in wanda pics inshi suka fi yawa aciki, yaje ya saka shi a boot in motorn shi ya dawo, inda Ammie tace ai ko ma me zeyi dashi sedai yayi amma ta nada Copy na dik pic inda ke cikin album in.. hakan yasa Meenah ta k'ara kwashewa da dariya tana kallan sauran, kwafa Captain yayi, a nan ne Ammie ta k'arayiwa Captain magana akan auren Afrah, gayamata yayi akan cewa insha Allahu next Month za'aje ayi tambaya, Allah yakai mu yasa alkhairi kowa yayi.
Kamun suka tashi akaje akaci abinci.
Bayan kowa ya kammala ne Ammie tayi musu seda safe ta shige, Meenah kuwa zama tayi ta cigaba da kallo, inda Captain ya tashi ya tafi dandalin da suke fira shida Afrah da dare kullum.
Ganin su biyu ne kawai a parlour yasa Naufal tasowa ya k'araso gun kujerar Meenah, zama yayi daff da ita yace;
"Friends?" Tare da mik'a mata hannu.
Kallan shi tayi, ta k'ara kallan shi a karo na biyu... mik'a mishi nata hannun tayi se da ya mik'o nashi dabbbb... ta jaye nata tace;
"Friends" atak'aice.
K'ayataccen murumishi yayi yace;
"Thanks for accepting my offer"
Murmushi tayi ko ita, abunda yasa ta amince mishi tana son ta k'ara samun kusanci dashi domin sanin duk halin da Captain yake ciki akan Afrah, kuma zatayi amfani da damar domin ta d'ana mishi tarko mai zafin gaske. Nace thoohhh😂

____________________________
Duk da ya kasance d'an k'auye amma hakan besa ya kasance jahili ba, be kasance yayi zurfin karatu ba, amma Allah ya saka mishi ganuwar abu da kuma jajircewa, be kasance mara ilimi ba, amma yabi rud'in zuciya yasa shi fara aikata abubuwa irin na mara sa ilimi, be yi tawakkali ga ubangijin da ya k'arb'e mudibbo mahaifin sa ba, tun lokacin da Jauro ya waye gari babu Modibbo, tun a ranar rayuwar shi ta canja, ya tashi daga Jairo mai ilimi mai warkar da masu cutar Aljanu zuwa Jauro mai lalata y'a y'an mutane, Jauro ya koma babban terror, wanda be d'auki fyad'e a matsayin komai ba, abu d'aya ne baya yi kuma baya tunanin yinshi koda anan gaba ne shine KISA, tuni abu ya fara damuwar mutan rugar, tun basu san wanda yake aikata wannan aika ai kar ba amma har suka fara zargin shi, amma kirkin shi na da, da kuma kwarjinin shi shi ya hana a tunkare shi da maganar, ga wani masifar tsoro da shakkun shi da kowa keyi a rugar, wannan ne yasa suka yanke hukunci tunkarar shi da maganar a duk sanda suka kama shi red handed...so da yawa idan Jauro ya sami kanshi a ke6e guri d'aya yakan yi kuka marar adadi, ya kan shiga damuwa mara misali idan ya tuna rashin asalin shi, uwa uba gashi rayuwa tayi mishi zafi tana k'ok'arin juya mishi baya, tabbas yasan abunda yake baya kyautawa amma kuma ji yake kamar bashi ya ke aikata wa ba idan ya aikata, wata irin damuwa da nadama take maimaye ilahirin zuciyar shi, sosai yake kuka na fitar hankali, sau dayawa yake kwana ya tashi ba tare da yaci abinci ba, duk ta'asar da yake baya sata, sosai yake jin tsanar iyayen shi a duk inda suke, kuma tsanar ta samo asali ne akan kallan shege wanda aka haifa ta hanyar fasik'anci aka yar, wannan tunanin da yake shi ya zama jigo na hassasa wannan tsanar, tunda ya tashi shi besan wani rayuwar jin dad'i ba, amma a koda yaushe yana yawan mafarkin shi tare da wani saurayi wanda kamar su d'aya, amma shi wancan yafi kyau saboda alamar jin dadi da kwanciyar hankali da yake tattare dashi, dik da ya kasance ba yaune ya saba wannan mafarkin ba, shi i'lahirin rayuwar shi tun yana yaro yake mafarki da wannan bawan Allah tun suna yara har suka girma, basuda wani bambamci a kamanni idan aka jaye jin dad'in wancan, tun abin baya damun shi har ya fara damun shi, a yanzu ya kasance a koda yaushe ko baccin rana yake yakan ga wannan bawan Allah, yawan ganin shi da yake cikin kwanciyar hankali da nishad'i shiyasa ya fara jin haushin shi da kishin shi, wannan ne yasa yake k'ok'arin yak'i da bacci akan ya k'aurace wa idanuwan sa domin ba abunda ya tsana irin ganin wannan mutumin, baya son ganin shi cikin walwala a koda yaushe kamar yadda yake ganin shi, kishi yake da alamar da yake gani akan jin dad'i da mulkin da ke tattare da shi, akan yawan wannan tunanin da yake ya kawo nak'asu sosai gurin sharholiyar da yake da yan matan garin, duk da yarinya ukku ce kawai ya lalata, a yanzu gabaki d'aya rayuwar shi ta raja'a akan son sanin ainishin wanena wancan da yake gani? Shin wa ze amsamishi wa'ennan tambayoyi? A ina ze ganshi? Yaushe zai had'u dashi? Mutum ne ko aljan? A wane gari yake?
A koda yaushe wa'ennan tambayoyin mara sa amsa ne yake sa jikinshi yayi sanyi akan al'amarin,. Gajiya yayi da wannan kukan da yake mara kan gado, tashi yayi domin wata irin matsiyaciyar yunwa yake ji, ga wani irin azababben ciyo da kanshi keyi kamar ya watse. Daure wa yayi ya tashi ya nufi bayan gari. Bayan yaje bayan gari ne ya sami wani iccen mango ya d'ebi guda 5., 2 ne kawai ninanne amma sauran dika d'anyu ne, zama yayi kan wani dutse ko wanke wa beyi ba haka ya dinga gaptar mangoron, se kalllan babban titi yake wanda motoci ke wucewa da k'arfi.
*****

Tin da safe ya tada Ammie akan cewa yau zasuje kebbi gurin d'an wani aiki da ya taso da gaggawa, hakan yasa tace Allah ya kiyaye hanya kuma ta shaida mishi cewa ai ko ita yau ba a nan zata yini ba zataje gidan su baby coz za'a kawowa yayar ta lefe, Allah ya sanya Alkhairii yayi tare da zaro bandir na y'an dubu guda biyu yace gashi a bawa y'an kawo lefen, godiya Ammie tayi kamun ya tashi ya wuce.
Naufal ze rakashi a haka suka kama hanya around 2:45. Sun fita gari sosai
Tsayawa motar su tayi saboda tayar da ta fashe,
"Damn it!!" Captain yace tare da buga staring motor.
Dariya Naufal yayi yace "you see your life koh? Kai shikenan se kace idan Ina gari ba zaka yi yawo da guards in ka ba? Yanzu kaga da tare da su muke shikenan sedai a bamu wata motar su cimmana da waccan, amma kagani yanzu, dole ka fita ka canja spare domin wlh ni daga nan kujerar bazan d'aga ko ina ba.
Wani irin mugun kallo Captain ya watsa mishi kamun yace,
"Ni ba rago bane irin ka, ko ka manta? Am a soldier, ko duka tayoyin sukayi faci within less than 30 minutes duka zan saka" ya fad'a yana d'age mishi gira d'aya... kwashe wa da dariya Naufal yayi yace; "auu na fa manta tare nake da jarumi babban soja, I salute🕴🏻.,"
"Mtswwwwwww! Kai baka ta6a rabuwa da shirme" fita yayi a motor yaje yana canja tayar. Bayan ya kunce d'aya ya bud'e boot ya saka gurin d'akko d'ayar album in photos inshi ya fad'i ba tare da ya kula ba, Jauro dake zaune can nesa dasu duk abunda yake faruwa yana kalla, tun tsayuwar su har gyaran tayar da yaga sunayi, kula da kamar abu ya fad'o a motor yasa ya tsura idon shi agun, bayan Captain ya gama saka tayar ne ya saka komai a boot in ya maida ya rufe batare da ya kalli k'asa ba, duk da kuwa yaji kamar ya taka abu a k'afar shi amma be duba ba, saboda matsuwa da yayi subar gunn... a 360 ya tazgi motar wanda yasa Naufal tashi a firgice, coz wani d'an bacci ne yayi awon gana dashi saboda iskar da ke kad'awa agun me dad'i...
Dariyar k'eta Captain yayi mishi though da gangan yayi kawai dan ya firgitashi ya tashi.... Naufal kam be iya cewa komai ba kawai ya fita batun shi ya d'akko wayar shi yana latsa, haka suka cigaba da tafiya shiru shiru kamar kurame,.
Tasowa yayi a hankali yana tafiya yana layi saboda tsananin yunwa, dishi dishi yake gani har ya k'araso inda Motar tabari, ganin abu me kamada littafi ne kawai yasa yayi tsaki da niyar juyawa, shi ya d'auka wasu kud'ine ko wani abinci, amma maganin zuwan banza yasa ya d'auki album in ya saka a yar jakar shi ta baka, batare da yabud'a ba..




Assalam my lovers😍😍 you all miss me right?
I miss u all too😩❤️❤️

💃🏻❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️😍😍😍😍😍

Nagode sosai da adu'oinku a gareni, u really appreciated Allah ya bar qauna😊❤️ Allah ya barmin ku masoyan wannan novel..

Allhamdulillah now insha Allahu za ku riqa jina akai akai💃🏻💃🏻💃🏻❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Ur prayers means alort❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Comment in ku zasu gwadamin irin missing nawa da kukayi😉😂lol nagode sosai...



Typing.............

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now