Chapter 50

193 28 16
                                    


🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
By
🌹Teemahcutey🌹

Page 50.
*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

Saura kad'an ta isa kan balcony na side in kawai taji motsi, tsayawa tayi chakkk... alamar fitowa da kuma sawun k'afa da taji yasa ta lab'e wani gu.

Captain kuwa maida hankalin shi ya k'arayi kachokam domin son ganin abunda take b'oye wa.

Relaxing yayi very calmly Yana winning chair ah slowly kamar me kallan a very Romantic series film😄.

Meenah kam tasan cewa tabbas in mutane ne a gun babu abunda ze hana su gan ta saboda kusancin da ke tsakanin su.

Rik'e da wannan bawan Allah suka fito k'arti biyu ne ke rik'e da shi tare da biyu baya, Dad ne ya fito daga k'arshe.

Zuwa sukayi suka saka shi a motor, juyowan da Dad zeyi karaff yaga macce da hijab a can lab'e, umarni yayi akan a je azo da ita.
Meenah kam kasa motsawa tayi dik da taga k'arti na nufato ta, addu'a Dad yake Allah ya sa ba wata ta jikin shi bace, aikuwa koda suka k'araso da Meenah a gun, kallan ta Dad yake haka ma Meenah kallan shi take da tsoron abun da za'ayi mata cikin wannan daren.
"Lallai wannan yarinyar ina ganinta a nan gidan, gun Fateemah, but nasan cewa ba y'ar uwarta bace.

Tuno maganar da bokanya tayi yayi,
D'auke idon shi yayi a kan ta, kamin yayiwa k'artin nan umarni akan ;

"Ku had'a da ita, ku kai su can guri mai nisan gaske, inda zasuyi nisa sosai da garin Sokoto, kada kuyi musu komai, sannan kuma kada ku cutar da su, ku kaisu can cikin daji mai girma wanda yayi nisa da garin nan."

"Inalillahii wa'innah ilaihir raji'un"

shine abun da Meenah ke nana tawa a ran ta, tace;

"Shi kuma Dad in Captain wane irin mutum ne?
"Me wannan bawan Allah yayi mishi da ni karan kai na?

Meenah kam k'ok'arin guduwa take domin har ta tattare hijab inta, amma kash!!

Tako biyu wani bujimi yayi kawai ya sharb'ota ya sakata a motor tana ta kiciniya, duka ta yage mai fuska, kuma abun mamaki Allah ya rufe mata baki ta kasa yin ihu ko kad'an, kunsan sometimes idan mutum yana in a great danger, tashin hankali da tantama akan wai kuwa wannan abun dani yake faruwa ayau? Yana hana mutum b'arkata komai😂, tau yau kam shi ya faru da Meenah.

Haka aka shiga dasu motar a take suka bata wuta suka bar gidan cikin matsiyacin speed.

Captain kam mutuwar zaune yayi ganin mahaifin shi da kuma wannan abun da ya aikata, what makes him delirious is that yanda Dad inshi ya saka wani k'ato ya d'auki wacce ba muharramar sa ba.

"For what reason Dad?

"To a ina zai kaisu?

"Me sukayi?

"Especially Meenah da suka gani a gun kawai"

"what about the poor man?

"Ba dai a na nufin a gidan su yake surviving ba all this while?

Saurin katse wa'ennan zantutukka nashi yayi before is too late, wayar shi ya wafto ya kira Oscar, soji ne shima amma yana d'aya daga cikin guards in shi... umarni ya bashi akan da sauri ya bi wata motor da tafuto gidan su yanzu yanzu kuma kada ya bari yayi loosing in su, nd don't he dare let them know that ana following nasu, kawai ya bisu slowly till they reach their fucking destination. Katse kiran yayi yana hucii kamar wanda ya sha maganin kusa.
A zafafe Oscar ya figi motor shima domin k'ok'arin bin bayan su, gudu ne suke falfalawa kamar ba gobe, shima haka Oscar yana k'ok'ari domin kada su k'aurace wa ganin idanun sa, saboda ba a kusa kusa yake biyar su ba domin kada su gane.
Sunyi kusan rabin hour suna kashin gudu, sun bar garin sokoto sosai , se faman gudu suke, Meenah kam ji tayi kamar an kashe ta a motor dan tasan cewa babu halin guduwa, haka ma babu halin ihu balle neman taimako, haka ta dage ta dinga karanta duk abunda ta sani na dangance da addinin ta.
Ko tsoro basa ji kuma gashi hanyar ba tada kyau ko kad'an.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now