Fashin Bak'i

92 8 4
                                    

At the top⬆️ Meenahs parlour.

Fashin Bak'i

1)Cuta; haqiqa cuta wata aba ce wacce take abin qi a cikin al'ummah, idan mutum ya kasance macuci, to tabbas idan baiyi saurin tuba zuwa ga Allah ba rayuwar shi baza tayi kyau ba, cuta wata abace haramtacciya acikin addinin musulun ci.
Haqiqa Zeenatu da Abrar zunyi cuta  a cikin wannan novel, kuma duk mutumin da ya kasance macuci baze taba ganin da kyau ba arayuwar shi, kamar yanda kuka gani rayuwa ta juya musu baya, haka kuma daga baya suka tuba suka koma ga Allah, kuma haqiqa ubangijin mu mai karban tuban mu ne a koda Yaushe, Allah ya qara nesantar da mu daga macuta ya kuma qara sakamu cikin bayin shi tsalkakkaku.

2)Munafurci; munafurci wani abu ne wanda daga yanda ake fadar kalmar kasan cewa batada kyau, munafurci babban zunubi ne, kuma munafiki baya shiga aljannah, idan mutum ya kasance munafiki bazai taba ganin ci gaba a rayuwar shi ba, amma idan ya tuba zuwa ga Allah ana d'anmahwar mishi, amma babu shakka Allah baya yafe laifin wani dan wani, shiyasa a koda Yaushe neman gafara da kuma yafiya yake da amfani, lallai Hahha taci amana, kuma ta munafurci mijin ta da kuma abokina zaman ta, wanda daga qarshe kunga yanda ta kasance, dama duk wanda yabi wani tafarki wanda bana addinin musulunci ba to tabbas yana cikin bala'e, Allah ya qara tsalkake mu ya wanke mana zuqatan mu daga munafurci kuma ya qara nesan tamu da munafukai.

3)Tausayi; tausayi da jinqai yana daga cikin kyawawan d'abi'u, Allah ya qara mana tausayin a cikin zuqatan mu, kamar yanda kuka gani Grandpa ya tausaya wa su Abrar akan abunda suka aikata, kuma babu shakka ya rangwanta musu gurin hukuncin da ya yanke, domin babu shakka ba hukunci bane abunda yayi musu gata ne, domin aure gata ne, ya nuna tausayi akan su, kuma sanadiyyar wannan sassauci da yayi musu Allah ya kawo musu shiriya, a na son idan mutum yayi kuskure kada a hantare shi, a dad'a janyo shi a jiki domin gayamishi gaskiya, duk Abunda kwanciyar hankali bai kawo ba tashin hankali baya kawo su, Allah ya qara saka mana tausayi a cikin rayukkan mu kuma ya had'amu zamantakewa da masu tausayi.

4)Son Zuciya; duk wanda ya biye wa son zuciya qarshen shi nadama, son zuciya wata muguwar halayya ce wacce batada kyau, duk abinda mutun zaiyi kada ya biyawa zuciya, gwara ka tsaya kayi abunda yake daidai, Lallai Dad ya biye wa son zuciya da Alaji Atiku sun fara aikata barna, amma da Allah yake karimun rahimun sai yayi saurin ceton Dad daga wannan halaka shikuma alaji Atiku da ya saba aikata hakan sai ya ga sakayya tun a nan duniya, hakama son zuciy ya saka Bokanya bukwaltu kauce hanya kuma kunga yanda sakayya ta kasance domin kuwa anyi mutuwar qasqanci, rabbi ya qara nesanta mu da su kuma ya karemu da son zuciya.

5)Sakaci; sakaci wato rashin dabara da kuma rashin kula, haqiqa Mommah tayi sakaci a lokacin da ta aike Meenah a waje da dare, wanda sakacin da Mommah tayi na sakin yarinya mace budurwa shi yayi sanadiyar saceta da akayi, ya kamata iyaye su kula sosai gurin kula da tarbiyar yara da kuma yanayin zamantakewa, hakama Jauro yayi sakaci a lokacin da rud'in duniya yaso kwasarshi da ya afka wata rayuwa Allah yasa mu dace Ameen

6)Rashin Dabara; rashin dabara wata halayyace wacce take samo asali daga rashin tunani, lallai Hajja tayi kuskure da yayi tunanin cewa boka zata iya yi mata Abunda Allah baiyi ba ta hanyar had'a auratayya domin wata buqata ta duniya, Allah ya sa mu dace Ameen.

7)Qaddar; qaddara tana daga cikin jarabawar duniya, yana daga cikin manya manyan abubuwa na gari wanda ubangiji yake so wato yadda da qaddara mai kyau ko mara kyau, qaddara ta afkawa Miemie wanda tayi sanadiyar rayuwar ta, haka ma Ahmad, kuma iyayen su sunyi haquri sun d'auki qaddara, hakama qaddara ta afkawa Musaddiq da Miemie wanda suka tasa rayuwar su, amma iyayen su sukayi haquri kuma Allah ya basu madadin su, qaddara ta afkawa Abrar da Zeenatu na auren mutumin da na tsarar su ba amma haka sukayi haquri suka  dauki qaddara wanda har Zeenatun ta rasa rayuwar ta, kuma su Grandpa sun d'auki qaddarar had'uwar zuri'arsu da ta aljanu, domin sun san ba yin kansu bane, kuma da sukayi haquri suka d'auki qaddara Allah ya kawo kusu qarshen komai cikin sauqi da salama, haka ma Haidar ya dauki qaddara auren yar uwar maryam wanda yaji dadin hakan  kuma yaga ribar hakan, dama jarabawar ubangiji yawane da ita, kuma dukkan su sunyi haquri gurin cin wannan jarabawar, kuma Allah ya taimake su sunga haske a cikin rayukkan su, Allah ya bamu ikon amsar qaddara a duk yanda ta zo mana Ameen.

8)Nadama; nadama tana da kyau, haqika duk wanda ya sami kanshi cikin nadamar Abunda ya aikata to babu shakka Allah ya so shi da rahama, domin kuwa duk wanda ya gano kuskuren shi ya tuba to lallai yayi babbar nasara, kamar yanda , Zeenatu da kuma Abrar sukayi nadamar Abunda suka aikata, kuma sunyi nadama da istigfari domin Allah ya yafe musu, Allah ya qara bamu ikon gano kurakuran mu muyi nadama da istigfari domin mu gyara Ameen.

9)Fad'akarwa; iyaye da matan aure da kuma emmata ya kamat mu tashi tsaye domin gyara zamantakewar mu na yau da kullum, kun daiga wannan family crisis da suka samu acikin wannan novel, ina fatar kun fad'akartu da wasu abubuwa.

10) Nishad'antar wa; nasan cewa kun nishadan tu da wannna novel, musamman Meenah🌹

🌹ABUN ALFAHARI NA🌹

                    ✍🏻Teemahcutey ✍🏻

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now