Chapter 27

230 17 9
                                    

🧚🏻‍♀Abun Alfahari na🧚🏻‍♀
                  By
   💐Teemahcutey 💐

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

Page 27.

Sossai likitocin suke iya bakin k'ok'arinsu domin ganin sun ceto rayuwar Captain,
Cikin ikon Allah numfashin shi yafara dai dai tuwa, Bayan kamar 3mnt suka mishi Allurar baccin 3hours wanda suna saka ran da zarar alurar ta sakeshi to zai farka normal.

Bayan fad'uwar Ammie da sauri aka sunkuce ta domin bata taimakon gaggawa, bayan ammata duk Abunda ya kamata saida suka bata gado suka mata alurar bacci Domin ta samu relief.

Daddyn Captain ai kuwa abu yaso ya rincha6e mishi domin shima hankalinshi yakai mak'ura gurin tashi har yana tinanin Anya kuwa be rasa d'anshi ba? Gashi kuma Ammie tashiga cikin wani halin, kwanciyar hankalin da yasamu shine da sauran likitocin suka sauko suke mishi congratulations akan samun nasarar ceto ran Captain daga baya suka bashi full assurances na cewa lallai within 3hours Captain zai farka.
Hakama suka k'ara da cemishi kada ya damu da condition na wife inshi domin kawai tasamu small attack ne kuma sun shawo kan problem in.

Sossai yay farinciki da jin wa'ennan dad'ad'an labaran.

Daga nanne suka shaida mishi cewa yakamata yaje yay ordering abinci wanda mara Lafiyar suke buk'ata Domin wanda yakamata suci babushi anan hospital in dole seyaje Vienna.

Traditional dishes na Austria suka lissafamishi kamar haka;
1)Vienna sausage.
2)Non-veal Vienna schnitzel.
3)Vienna demel pastry- cafe demel 😋😋

Atake yaje near restaurant yay ordering amma seda ya had'owa da kanshi rosted chicken with tea coz shikam baya son irin dishes in, tinda sukaxo beci dish nasu ko d'aya ba saidai Ammie.

Koda ya dawo already Ammie ta farka sossai ya kwantar mata da hankali har taci abunci tayi hani'annnn.
Jiran tsammanin farkawar d'an nasu kawai suke tsumaye.

Suna awani room suka ga an turo shi akan gado alama dai za a canja mishi daki ne, Amïñįtÿ aka mayar dashi.

Tashi sukayi suka shiga røõm in domin yanxu he's out of danger.

After like 3hours 30mnt se ga Captain yafara motsawa, Iyayen nashi basuyi k'asa aguiwa ba gurin tashi suka kira doctor kamar yadda suka umarta akan da sunga yayi motsi kada suyi wani yunk'uri face sun kirasu.

Batare da 6ata lokaci ba 3 doc, sukayi attending to him, gayawa su Ammie sukayi akan su d'anyi excusing nasu, fita sukayi xucuyarsu wasai domin sun san da yaddar Allah matsalar Allah ya kawo iyakar ta.

Bud'e idanshi yayi, yanayi yana lumshe idan saboda dogon lokacin da ya d'auka Bega hasken duniya ba.

Y'an tambayoyi suka mishi domin tabbatar da bayada wani problem,

Da kyar ya iya buda bakin shi yace

" am absolutely okay, I just wanna go home nd please kindly dislodge drip away from my hand. It's like it's been a while coz m felling so slumberous on my hand"

( Lpia qlw nake, kawai inasan aciremun
drip saboda naga kamar Yajima saboda hannun yay mun nauyi matuqa)

Da kyar ya iya had'o wa'ennan kalmomin yafada.

" Don't disquiet, we will detach it very soon because this one it doesn't take that long, if u allowed it to liquidate it will helps u to get back as strong as u are"

(kada ka damu, zamu cire nan bada jimawa ba saboda bamu jima da sakama maka wannan ba, idan ka bari ya k'are zasu taimaka maka gurin maida kuzarin jikinka kamar yadda kake).

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now