Chapter 2

687 49 0
                                    

Waw waw waw it seems like u like the story? Vote and comment it will encourage me😉 thank you so much for the first time ILYSM😍😍😍😍

wattpad
husnasidi
Ahaanaa00

"K'was, k'was, shine sautin da takalmin ta yake bayar wa sai wani rangwad'a take, daga can ta tsinkayi muryar Mommah tana cewa;

"Wai har yanzu baki tafi bane? Kina can kina kwalliyar da na hanaki ko?

"Sorry Mommah, yanzu zan tafi"

"Allah ya tsare"

Koda ta fita a harabar gidan na su se da ta zaga ta duba mirrorn window tana wani fari da idanu, ba tare da b'ata lokaci ba tabi hanyar fita bayan ta gaida Baba kai gadi yayi mata Allah tsare.

A maimakon ta shiga napep kawai sai yarinya ta tsayar da mashin tare da hayewa abunta tana wasar baki kamar zautacciya.

Wannan yarinyar akwai abun dariya a tattare da lamurran ta, domin kuwa Allah ya hore mata k'aunar mashin, duk da gidan su ba'a bari amma ba abunda yake hana ta d'anewa idan ta samu sarari kamar irin na yau.

Suna gaf da qarasawa cinkoso ya had'u a hanya wanda aka samu go slow, dafe goshin ta tayi saboda rana da yake dukan ta,  wata mota ce qirar Velestar fara k'al a gefen ta,  kallan mirrorn motar takeyi tana gyara gelenta sai wani murmushi takeyi ganin yadda hasken rana yake bugun fuskan ta sai wani k'yalli take, can kuma sai ta sha toka tana harare harare, kuma dai daga k'arshe ta k'ara zabga murmushi duka ita da mirror take wannan abun, mamallakin wannan motan mai suna Mahmood abun mamaki ya bashi, hakan yasa ya kifa kanshi a sitarin mota yana ta dariya saboda yau yaga abunda bai tab'a gani ba, da farko dai ya d'auka shi take harara amma tuno da yayi cewa motar tana da super dark tinted hakan ya tabbatar mishi da cewa da kanta take, dariya yakeyi har ta ban mamaki, can da ya ankaro ashe har an saki hold off, mutane sai faman oda suke yi mashi saboda har na gabam shi sun wuce amma saboda tsananin dariya bai kula ba, da sauri ya gangara gefen titin domin basu guri.

Dube dube ya riqa yi amma ina, babu mashin babu labari nai, amma fah abun ya bashi haushi saboda baya son yaga mace ta hau mashin, amma yaga alamar wannan gwana ce yadda ta d'ane mashin in,  yaso ya qara ganin yarinyar amma haka ya haqura ya wuce abunsa tare da tunani kala-kala.

Meenah kuwa tuni ta qarasa inda zata, kud'in shi ta bashi tare da shirin tsallakar titi saboda d'aya side in ya ajiye ta kuma gidan da zataje opposite ne dole se ta koma d'aya b'angaren.

Ta tsallako lafiya ta wuce wata majalisar maza acan ta tsinkayi muryar d'ayan su yana fad'ar;

"Wai wai, kun ga qata mai hanci wai? Ta6arya kenan" kwashe wa duka majalisar tayi da dariya , ranta ya 6ace sosai da sosai kuma Meenah bata mantuqa bare yafiya, idan akayi mata abu their and then take mayar da martani, dawowa tayi baya baya domin bashi amsa;

"Ai ba uban wani ya kawo ni duniya ba balle ayi qorafi a kai na,  mtchewwww aikin banza masu zaman banza ana sa wa mutane ido a banza bigs for nothing" wuff tayi ta shige gidan dan dama majalisar a bakin gidan take, kuma yanda ta dawo baya-baya sai tayi kamar abu ta yada zata d'auka ne, kuma yanda tayi maganar kamar ba da su take ba.

D'aya daga cikin samarin yace;

"Kai, mu wannan y'ar ficikar yarinyar zata gayawa magana? Wlh sai mun gwadamata ida qaramar  yar rainin wayo ce"

"Common, to meye dan kayi dealing da wannan small rat? Abeg fita batun ta kawai laifin mu ne da muka kulata" cewar d'aya daga cikin su.

"Wallahi sai ta gane kuren ta zan raina mata da hankai"

Dariya suka kwashe da ita suna tafawa.

Meenah kuwa hankali ya tashi domin tana jiyo abunda sukafad'a take yan hanjin ta suka fara kururuwa, dama akwaita da afkin tafka rashin mutunci amma akwai mahaukacin tsoro.

kwashe da dariya..... daga cikin gdan da take tana jiyo abinda samarin suke cewa ...

D'an qaramin bakin ta ta turo tace;

"To meye laifina? Ai su suka fara tsokano ni ni kuma na rama, kuma wlh yau sedai na kwana a gidan nan ba inda zani su jibgeni a banza tabbb!!



Garau kakeji ta banke mutum can gurin yawan suruti da take ita kad'ai.

"keeee wace irin shaashaasha ce da bakya kallan gabanki??

Wata yar budurwa ta fada wacce daga ni ta girmi Meenah nesa ba kusa ba domin a qalla zata kai 25 years....

Abun ya 6atawa  Meenah rai kawai se tace "yoo ke da ba shashasha ba me hana ki dubi hanya? Mtsw"

taja tsaki tazagayeta ta wuce.

"Kutumar ubancan.... Ni wannan yrinyar zata zaga? Wlh se naci ubanta... naga wanda ya tsayamata"

Itakawai tanata bambami da zage zage kamar me yi da warinta, itah Meenah ta dad'e  da shigewa bata ma san  abunda take bah.

"Ke Zeenatu ke dawa?? Hankalinki daya kuwa? Naganki ke daya amma ki na ta zage zage what wents wrong?

"Yaya Haidar fah wannan mara kunyar yarinyar ce  Meenah  tazo tanamun renin sense!



Ba tare da yace komai ba ya zagayeta ya wuce, dogon tsakii  ta ja tare da figar  car nata aguje tabar gidan...

Nimadai tsaki naja nace bara naje gunsu meenah naga wace wainar ake toyawa 😂😂

Hello my pple hw u oll? I love u all .... I ope ur enjoying it?? Ur votes and comment will encourage me 😍😍

🧚🏻‍♀️ABUN ALFAHARI NA🧚🏻‍♀️

Na Teemahcutey 😍😍😍

*

*

*

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now