Chapter 49

174 19 10
                                    


🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
            By
    🌹Teemahcutey🌹

Page 49.

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

I'ya kayan da take so ta d'auka ta bar gidan.
Bayan sati d'aya.

A yau ne Dad in Captain ya diro a sokoto wanda ya d'au alwashin fitar da wannan mutumin idan ya samu chance.
Meenah kuwa dawowar da tayi a gidan Ammie kawai dan ta samu damar bincike ne kamar yadda ya kama ta,
Washe gari taje gun wani d'an department insu wanda ya k'ware ta fannin computer, bayan d'an k'aramin bayani da tayi mishi akan abunda take so yayi mata daga bisani ta koma gida.
Haka 'i washe gari ta shirya ta k'ara koma wa gidan su Waleedah, tambaya tayi akan ina ya Haidar? Aka ce mata yana side in shi, tashi tayi taje gun, seda tayi sallama sau ukku kamun yayi mata iso akan ta shigo.
Gaida shi tayi kamun ya bata izinin zama, buk'atar son magana tayi dashi hakan ya bata izini akan yana sauraren ta, se a lokacin ta k'are mishi kallo, duka ya rame, ya rikice ya zuzuce, sannan kuma duka ya jeme a yanda taji ma tun b'atar Miemie be k'ara zuwa gun aiki ba.
Magana tayi mishi akan "mye yake hasashe akan b'atan Miemie, sannan kuma ta k'ara tambayar shi da kuma rok'onshi akan kada ya yadda akan abunda mutane suke cewa wai ita ta gudu da kanta"

Dogon tunani yayi kamun yace;
" taya za kice kada na yadda? Bayan duk abunda ake tana sane? Kina da labarin idan na gan ta online na tura mata chart tana karantawa? Did u believe hadda VN nake mata tana playing? Dan mye zatayi mun haka? Tun farko tasan bata so na dan mye zata amince mun daga baya ta juya mun baya? Dole nayi mata ne? Gabaki d'aya ina cikin rud'ani, ina buk'atar ganin ta domin ta amsamin wa'ennan tambayoyi,
k'arasowa yayi gun Meenah ya rik'e kafad'un ta yana jijjagata tare da fad'ar " whyyy?? Whyyy??? What did I do to her to procure this kind of ostracism? Did she know how much she means to me? Did she ever think the kind of situation that am going through now? Nooo!!!!! It can't bee!!!"
Dik ya wani haukace yana neman b'alla Meenah, da k'arfi ta tazge jikin ta, tana girgiza kai,tare da fad'ar,

"Ya Haidar, tana nuna shi...ya Haidar da bakin ka kake fad'ar haka? Ya Haidar ka bani mamaki, ashe soyayyar da kake mata ta banza ce koma bata kai zuci ba tunda har ka kasa tantance what she's capable of and what she's not capable of.. all this while ya Haidar? Ina soyayyar da kake mata? Ina fahimtar da ke tsakanin ku? Wani murmushi tayi wanda yafi kuka ciyo ta d'ora da, a da nayi tunanin a lokacin da kowa ya juya mata baya kai a lokacin kake tsaye tsayin daka domin ganin ka kare mutun cin ta ko ta halin yaya, ashe nayi kuskure sam!! Ba haka bane, a lokacin da kowa ya juya wa y'ar uwata baya nikuma a lokacin nake bayan ta, nayi tunanin bayan ni kai ne mutum na biyu da zaka fahimce wannan al'amarin domin taimaka min mu bishi daki daki domin gano wa'enda sike shirya wannan mak'ark'ashiyar. To Allhamdulillah! Da ka bayyana mun komai a sauk'ak'e, mun gode ya Haidar, nice nan AMEENATOU xan gano wannan gadar zaren da aka shiryawa y'ar uwata domin lalace rayuwar ta, hak'ik'a kowa ya juya mata baya a lokacin da take buk'ara kusancin ku, ni zan zamo jigo gurin tsamo yaya ta a cikin tuggun da aka d'ana mata, nice nan zan bi diddigi domin gano zare da abawa, kowaye yana tunanin yayi basaja da k'wak'walwar mutane dayawa to ni gaira tawa, Inada confidence akan yayata, yayata itace hasken rayuwa ta, itace ABUN ALFAHARI NA,! Kuma nasan baza ta tab'a aikata hakan ba har k'arshen rayuwar ta.
A daidai nan ta tashi ta fita da gudu tana share hawayen ta, ko cikin gidan bata koma ba ta nufe hanyar fita, batayi aune ba sukayi karo da Zeenatu wacce seda jakar hanun ta ta fad'i, da wani irin sauri ta duk'a ta tattare kayan jakar nata ta mayar tare da barin gurin batare da ta k'ara kallan inda Meenah take ba.
Galala!! Meenah tayi tana kallan ta,wanda tayi mamaki matuk'a da irin yanayin tsoro da firgici da ta hango a idon Zeenatun k'arara.
Kallan inda kayan na Zeenatun suka tarwatse tayi, wani d'an k'aramin complimentary card ta gani, duk'awa tayi ta d'auka, seda ta shiga motorn ta kamun ta duba card in, **Iziddeen Zayyan** tare da phone number shine abunda ta gani a rubuce, cigaba da juya card in tayi kamun ta wining glass in motor tayi jifa dashi, tada motorn ta tayi, mye ta tuna? Kawai naga ta kashe ta futo ta d'auke CC ta koma motor, a compartment ta sakashi kawai tabar gun.
Zeenatu kuwa gaban ta se faman bugawa yake saboda tsananin tsoro da firgici, ba komai ya sata hakan ba se dan wayar Miemie dake cikin jakar da kuma fad'uwar da jakar tayi.
Haka ta dinga hamdala bayan ta shiga d'akin ta. Nace hmm 🤔!

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now