Chapter 34

250 25 5
                                    




🧚🏻‍♀Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀
      By
   🌹Teemahcutey 🌹

Page 34.

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no
pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

...<!><!><!><!><!><!><!><!><!>...
Bayan sun wuce ne a ka kawo mata garwashin, karatun Alk'urani ta saka a TV ta zuba wannan maganin a cikin garwashi... AC ta kashe na parlourn tare da kunna fan kad'an yadda zata dinga hura garwashin, ajiyeshi tayi dai dai inda Meenah ke jiyo k'amshin shi, bayan ta k'ara zuba maganin ne ta haye sama abunta.
Wata irin atishawa ce Meenah ta dinga yi ba k'auk'autawa, ak'allah tayi fiyeda 8 kuma dika a jere da juna, daga k'arshe ce tayi wata irin atishawa mai k'arfi wacca tazamo cikon ta goma.
Ai kuwa atake naga Meenah ta zama ta zaune tana wani mutsitsika ido.
Tashi tayi zaune da kyau dan ganin Inda take, mamaki tayi na yadda akayi ta zo gun Ammie? But share zancen kawai tayi tare da haurawa sama.

/*\/*\/*\/*\/*\/*\/*\/*\/*\/*\/*\/*\/*\
Zaune take ba abunda take kawai tabar Meemee da aiki, ita kuwa bata damu ba dama ba raguwa bace gun aiki.
Tashi tayi ta shiga d'aki ta kunna d'ayan SIM card inta da ba kowa yasan tanada layin ba se tsirarrun mutane.
Bata daddara ba duk wulak'ancin da ya Haidar ya zabga mata akan baya son ta yanada wacce yakeso dum da besan ko dawa yake magana ba, a hakan ta jure ta typer mishi text message na soyayya mai dad'i...
D'ayar number da ake turowa Meemee text in gargad'i akan Haidar ta kira but still kashe. Yanke hukuncin turawa number text tayi kamar haka:
ZAN TAIMAKA MIKI GURIN RABA TSAKANIN MEEMEE DA HAIDAR.
Turawa tayi tare da kashe sim in.

After 5days.......
Har yanzu Gwammah na asibiti, ta farfad'o sai dai ba umm ba umum, saboda ciwon da taji abaki.

A b'angaren Meenah kuwa tinda taje sama d'akin ta bata k'ara waiwayar k'asan ba har na tsawon 5days, anan maids ke kawo mata abincin ta, daga ci se wanka se sallah.
A kowace safiya da bak'in rai take tashi kamar wacce ake yiwa bushara da wani mugun abu, wata rana ma rufe d'akin take ko Ammien bata zuwa ta gaidar, a hakan ma a wani lokaci Ammie da kanta take zuwa tayi knocking har tagaji kuma tasan tana jinta sarai se ta k'yaleta tak'i budewa. Ko Ammien dai ta d'aga mata k'afane tasan zata dawo normal.

Yau kam da alama hajiya Meenah an tashi cikin farin ciki domi kuwa bayan tayi wanka ta saka doguwar riga ta yadi mai santsi.
Bayan ta saka hula a kanta ta fito ta nuface d'akin Ammie tora k'ofar tayi batare da tayi sallama ba, aikuwa abunda tayi tinani hakane domin bacci take bata tashi ba.
Kitchen taje ta tadda maids suna batun fara aiki a nan ta tsayar dasu akan cewa kada su d'ora komai.
Order ta basu akan su d'akko wake su wanke bayan sunyi abunda ta umarta se tasa suka d'an sussukasu bayan sunyi ne tasa suka cire 6awan baqin waken, d'an jik'a wanken tasa sukayi.
They have no idea what she's going to do cause basu iya irin traditionals food sosai ba.
A haka dai suka cigaba da bin umarnin ta.
Tattasai da attarugu da albasa da tafarnuwa tasa suka wanke suka saka aciki.... daga nan tayiwa d'aya daga cikin su umarni akan taje gurin mai gadi tace ya kaita gurin markad'e.
Ganin tayi ta tsaya tana kallan ta batayi abunda tace ba daga nan ta d'ago jirgin ta domin mai gadin da ke duty a yanzu ba haushe ne bayajin turanci., sukuma maids in ba kasafai suke gane ko wace irin hausa ba...
Bayan Sunje gurin me gadin ne Meenah tayi mishi bayani akan inda ze kaita.
Dawowa tayi ta d'ora ruwan a butar ruwan zafi.
Albasa da gabun albasar ta yanka da d'an dama... dagannan after like 5mnt sega shi an kawo mata k'ullun na waken. Zama tayi akan kujerar tsuguno bayan ta d'akko maggie, farin maggie curry da kwai.
Zama tayi ta na buga k'ullun bayan ta gama bugashi ne ta saka maggie fari da d'an gishiri seta juye albasar da ta yanka da gabu..... bayan ya buggu ne ta saka maggie star d'aya.. juyashi ta k'arayi daga nan ta raba k'ullun biyu.
D'ayan ta fara dauka ta k'aramishi maggie star yanda zeji tare da zuba curry, already ta dafa kwai da anta daga nan ta kwalde kwan nata dayawa ta saka aciki, bayan ta juya da kyau ta d'akko hantar ta data yanka ta tafasa ta juye akai, wata albasar ta k'ara tare da zuba mai aciki yanda ya kama ta ...... juyawa tayi k'ullun gwanin sha'awa haka ta shiga kukullashi a leda tana kad'awa a ruwanda ta aza wanda sun dad'e suna tafasa.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now