Chapter 59

301 21 10
                                    


🧚🏻‍♀️Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀️
By
🌹Teemahcutey🌹

Page 59.


*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

Sai kusan magriba Meenah ta bar gidan.

Bayan koma warta gida anan ta soma tunanin yadda zata b'ulluwa lamarin, saboda tana son ta cikawa y'ar uwar ta alk'awarin da ta d'auka.

To idan haka ne kuwa, zama gidan Ammie a yanzu ba nata bane, saboda a gaskiya gani take barata iya tab'uka komai ba idan tana gidan, amma kuma ai a nan gidan tafi samun freedom of movement, to amma ya za'ayi ta gano wani abu tana zaune a wannan katafaren gida? Haka dai ta dinga waswasi har Allah ya waye safiyar gobe.

Ta tashi ne da tarin gajiya saboda ta dad'e a daren jiya tana kaiwa Allah kukan ta akan ya taimake ta domin gudanar da wannan binciken, kuma ya haskaka mata haske a cikin duhu, to wannan dalilin ne yasa ta tashi very late wanda seda Ammie ta biyo sahu, domin a yanzu su Ammie da zarar bataji motsin Meenah ba firgicewa take tabi sahu tare da addu'ar ta taradda ita😆😆.

Bayan sunyi breakfast ne anan Meenah tace zata je gida kuma tana buk'atar addu'ar su domin akwai wani abu da take son tayi, kuma tana fatar Allah ya taimake ta.

Addu'a da fatar dacewa sukayi mata dagannan bayan sallar ZUHR tabar gidan, wanda shima haka Captain zai tafi Abuja shi da Ammie domin binciken mahaifin shi a 6oye ba tare da sanin shi ba.

Ta koma gida lafiya cikin k'oshin lafiya, a yayin da su Ammie jirgin su yayi landing safely.

A b'angaren Abrar kuwa yafi mata kwanciyar hankali akan Meenah na can a gidan Ammie, kwata-kwata bata son zaman su gu d'aya amma ya ta i'ya?
*******

Bayan shud'ewar wasu y'an makwanni.

A y'an kwanakin nan Meenah ta fara zargin Abrar, saboda wasu y'an lokuta tana yawan jinta tana waya tana d'aga murya da ta gan ta se ta datse kiran.

Haka ma a kullum bata waya se ta ga Meenah tayi bacci sannan ta fara wayar ta.

Wani abu da ya tayar wa Meenah hankali shine ganin wayar Margayiya Miemie a cikin kayan Abrar, abun yayi matuk'ar d'aure mata kai.

Haka ta dinga wasu tunane tunane but still she can't believe what she saw, taso tayi confronting inta da maganar amma se tayi tunanin ai idan baka iya kama b'arawo ba shi sai ya kama ka.

Kuma ta d'au alk'awari akan sai ta d'auki wayar nan tayi bincike a kan ta domin ta tabbatar da cewa itace.

Se a yanzu brain inta ya tuno akan irin sak'on da Miemie take turowa da ake hasashen tserewa tayi! Kuut!! To me kenan? Wallah kuwa idan da akwai hannun Abrar a cikin wannan lamari zataci uban ta.

Haka Meenah take ta maganganun ta cikin ran ta.

Akwai wani lokaci da Abrar ta shiga wanka ta bar wayan ta, to a nan Meenah ta samu dama ta d'auki wayar Abrar in.

Call log kawai ta shiga domin son ganin da su waye take yawan waya haka? Wata number ta gani wacce tayi saving da *PARTNER* saurin d'aukar number tayi tare da ajiye wayar coz taji alamun fitowa.

Bayan ta bincike kayan ta ba taga wayar Miemie ba.

Abunda Meenah bata sani ba shine gabaki d'aya duk abunda take Abrar na kule da ita, shiyasa ta canja mazaunin wayar domin tabbatar da hakan.

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now