Chapter 3

580 37 2
                                    

3
🧚🏻‍♀️Abun Alfahari na🧚🏻‍♀️
Na
💕Teemahcutey 💕

Sallam ta rangad'a taji shiru ta qara rangad'a wata nan ma shiru taji kawai se tayi wuff ta shige a main parlour.....

Tad'an  jima zaune se ga yar aiki tace mata Hajia  tana bangaren mai Gidan  Meenah tace tau.

Yaya haidar ne yay sallama ta amsa se ta gaida shi yayi mata ya hutu tace Allhmdllh.

Guri ya samu ya zauna  yana tambayar ta yaushe zasu koma? Tace mishi next week ne

"Wai yaya Haidar yaushe Walida zata dawo  ne? Yace mata "in the next 3 days...
                        ()()()()()()()()

                            TUNA BAYA.
Alhaji  Usman d'a ne  gun Alhaji Shehu
Alhaji Shehu d'an  kasuwa ne yana zaune a garin Sokoto  a wata unguwa wacce ake kira  Runjin Sambo,  dashi da Matar  shi daya Hajiya Gwammah.

Auren had'i ne aka musu, ba wata  soyayya tsakaninsu amma dai sun fahimci juna sossai kuma suna qaunar juna Sossai...

A shekarar su  ta biyu da aure Allah ya azurta gwamma da samun ciki, a ranar kuwa murna kawai suke musamman Alhaji Shehu dama yana matuqar son y'ay'a se gashi Allah ya bashi....
ranar wata asabar ranar ta zame musu ranar baqin ciki musamman a gun Alhaji Shehu saboda yammacin wannan ranar ne gwamma tafito daga ban d'aki kawai se tazame ta fad'i a qasa runtum.

Salati ne yake fita daga bakinta a yayinda jini yake gudana ta qafafunta, daidai wannan lokacin se ga Alhaji Shehu. " Assal.... sallamat da be isuwa ba kenan Saboda  mawuyacin halin da yaga matarshi a ciki...

Batare da bata lokaci ba Ya sungumeta se hospital....

A nan ake sheda musu cewa lallai dan cikinta ya zube, tashin hankali ba'a sa mishi rana domin kuwa a ranar Alhaji Shehu kiris yarage yayi hauka.

Amma dayake Allah ya bashi matar qwarai ita ta dinga kwantar mishi da hankali har ya sassauto...
Washe gari aka yi discharging nasu suka koma gida...

Bayan wata ukku hajia gwamma taqara samun wani ciki .... bayan wata tara da awa tara da Minti goma sha tara wata wahaltattar naquda ta tada ita cikin dare ba qaqqautawa.

Batare da bata lokaci bah Alaji ya kaita asibiti...

Har qarfe biyu na rana ana abu daya amma haihuwar ta gagara, cikin ikon Ubangiji,  Allah ya bata ikon haiho samballeliyar diyarta mai kama da ubanta.

Alaji yayi mata hud'uba  da suna Fad'imatuh-zahra'u. Amma ana kiranta da Zarah.

bayan shekara biyar Allah ya qara azur tasu  da haihuwar d'ansu  mai suna USTHMAN daga shi se Allah ya qara basu wani mai suna umar dagannan haihuwar ta tsaya chakk..

Babu laifi Alhaji Shehu yana kula da y'ay'a sa  yana biya musu buqatunsu

Fatima ta kammala makarantar ta anan Alaji yace ta fidda miji.

Tafitar da wani  mai suna Ahmad, aka
mata aure aka kaita garin kaduna chan xata ida karatun ta cikin kwanciyar hankali.

Usman ya kammala karatunshi a Usmanu dan fodiyo University inda ya karanta engineering... kuma yana harkan kasuwancinshi domin kuwa Alhaji shehu ya azashi..... bayan ya kammala ne aiki ya gagara so ba yadda zeyi kawai ya aje kwalinshi ya fad'a  kasuwanci ba kama hannun yaro. 

Abun Alfahari Na✅Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ