Chapter 33

269 16 6
                                    

🧚🏻‍♀Abun Alfahari Na🧚🏻‍♀
       By
   🌹Teemahcutey 🌹

Page 33.

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no
pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

Abun Alfahari na🧚🏻‍♀ https://www.wattpad.com/story/203815299?utm_source=ios&utm_content=story_info&utm_medium=link&wp_page=story_details

*~DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI~*

<><><><><><><><><><>

Tin a ranar da Meenah ta koma gida e washe gari wani aiki yataso mishi ya wuce Abuja..... wanda duk tsawon wannan time be dawo sokoto ba, se a wannan satin yadawo sokoto tare da Fahad.

Zaune suke cikin gardiner suna d'an wani aiki a laptop. Kamar wanda aka tsakula Fahad yace
" buddy wai ina wannan sister taka da kake sakawa status ne? Tinda nazo ban ganta ba fah?
"Batanan" shine abunda Captain ya fad'a ya cigaba da aikin shi.

Shima Fahad shiru yayi suka ci gaba da abunda suke.

Bayan kamar y'an mintuna suka tashi domin gabatar da sallah.

~~<><>~~<><>~~<><>~~<><>~~
A take ta banki k'ofar da zata sada ta da side in Gwammah ai kuwa k'ofarnan ta kare gabaki daya, ji kake garam, ta fa'a qasa.
Ba tayi wata wata ba ta afka cikin gidan tana wata irin masifaffiyar k'ara.
" Inalillahii-wa'innah-ilaihir-raji'un" shine abun da ke fitowa a bakin Mommah da matar uncle Omar a dai dai lokacin da sukaga Meenah tayi kukan kura ta afkawa Gwammah.... sosai ta shak'e Gwammah wanda duk iya yadda su Mommah sukayi domin ta saketa Abun yaci tura, d'aukar ta take tana jibgar ta k'asa kamar kayan wanki.

Su Mommah kuwa in ba kuka ba ba abunda suke saboda basu ta6a ganin irin wannan tashin hankali azahiri ba.
Duk iya yanda suka so su kwaci Gwammah daga muguwar shak'ar da akayi mata kasawa sukayi, domin ba k'aramin chakuma sukayi mata ba.

~<>~<>~><~<>~<>~
Ammie dake k'ok'arin shiga a bakin corridor ta had'u da Maneer.. bayan ya gaida ita ya shaida mata akan basa nan suna inda Gwammah..... so kawai dama ta jima bataje gidan ba hakan yasa ta yanke hukuncin riskar su acan kawai.

>>>>>~~~~~~<<<<<
Da kyar aka samu aka janye Meenah akan Gwammah.... wata irin k'ara ta k'ara saki wacce ta lunka ta d'azun firgici da amo... seda ta watse su duka.... aikuwa da k'ara chafkar Gwammah ta mak'ure tana kallan ta da rinannin idanun ta.

Tsakanin Poppah da Uncle Omar se rige-rigen shiga gidan suke bayan kowa ya Parker motar shi.

Shiga sukayi a gidan a 360🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️...Dama already tinda sukaga bazasu iya shawo kan lamarin ba shiyasa suka kira su Poppah.

Poppah ne yake k'okarin rabasu amma inaaa ya kasa... atake ya wanka wa Meenah mari amma ko gezau batai ba..
Ba wanda ya kawo ayi mata karatun Alk'urani saboda rud'u... da sauri uncle Omar yayi alwala ya dakko Alk'urani domin karanta mata, sassauta rik'on da tayiwa Gwammah tayi tana biyar karatun a hankali..... wani mugun sound cikin Poppah ya bada k'ululuuuuu!!!!!!!!!

Wata magana naji ta fara tashi cikin wani amo wanda be cika tayar da hankali ba

"Na jima ina jiran wannan ranar se yau tazo..... mye sa take son ta zalinci bayan Allah?"

Abun Alfahari Na✅Where stories live. Discover now